Ilimin Zamani: Babban Ƙalubale Ga Al’ummar Musulmin Arewa
Daga Fatuhu Mustapha
__________

Saint Luis da Saint Thomas: Kalubale ga Ƙadiriyya, Shia, Izala da Tijjaniya. Ina ta mamaki da wasu malamai suka fara hawa mumbari suna ɓaɓatu a kan wai, suna mamaki ya aka yi gari kamar Kano amma Musulmi ke kai ‘ya’yansu makarantar Kiristoci!
Amma ai ba wannan ya kamata su tuhuma ba. Shekara sama da 700 ana Ƙadiriyya a Kano. A nuna min ƙwaƙƙwarar makarantar boko koda guda ɗaya da ‘yan Ƙadiriyya suka kafa a Kano, ko ma a wani wuri domin ‘ya’yan ‘yan ɗariƙar su samu ilmin boko mai kwari. A lura, ban ce babu ba fa, ban san da ita ba ne! Je ka Bagadaza ka ga irin makarantun bokon da ‘ya’yan Ƙadirawa suke zuwa.
Tun kafin zuwan Shehi Ibrahim Nyass, a shekarar 1920 ake Tijjaniya a Kano amma a yau sama da shekara 100 da zuwan Shehu Ibrahim, ba mu da ƙwaƙƙwarar sakandare da za mu nuna wa duniya, wadda take yaye ‘yan Tijjaniya, su samu karatun boko mai inganci! Je ka Morocco ka ga irin makarantun da ‘ya’yan Tijjanawa ke zuwa. Ƙasar Morocco tna ware kashi 1/5 na kasafin kuɗinta, domin bayar da ilmi kyauta kuma dole ga ‘yan ƙasar.
Izala ta haura shekara 40 da kafuwa, ta doshi 50 yanzu. Kuma a iya kiranta da ‘ya’yan nan da Turawa suke ce wa, “born with golden spoon.”. A nuna min makaranta kamar Saint Luis guda ɗaya da suka kafa, wacce take samar wa ‘ya’yan mabiyansu, ƙwaƙƙwaran ilmin boko. Kusan da yawansu sun je Saudi karatu. Haka suka ga ana yi wa ilmin boko a can?
Ina ‘yan Shi’a? Ba fa muzahara ce kawai aikin Shi’a ba. Babban abin da ya sa Shi’a ta yi zarra, duk da rashin yawansu, in an kwatanta da Sunni, amma kuma saboda jahircewarsu a fannin ilmi, ya sa yau ƙasar da ita ce karfin Shi’a a duniya, ta zama gagara-gasa a duniya, wato kasar Iran.
An kafa Sakandaren Saint Luis da Saint Thomas a Kano tun a shekarar 1951, sama da shekaru 70 ke nan a yanzu. Kuma tun lokacin makarantar ba ta taɓa yadda ta yi ƙasa a gwiwa wurin bai wa yara ilmi mai inganci ba. Saɓanin yadda muka bari, namu makarantun suka lalace, suka koma bai wa yara ilmi mara inganci.
Bari mu ɗau darasi daga Musulmin Yarabawa, waɗanda muke yi wa kallon cewa mun fi su zama Musulmi. A lokacin da kusan makarantun boko a ƙasashen Yarabawa kusan kashi 70 na ‘yan Mishan ne, sai aka lura da yadda suke ɗora wa ‘ya’yan Musulmi ƙa’idoji masu tsauri, kafin su yadda su ɗauke su a makarantun. Don haka, a 1943, srishararren Lauyan nan kuma Ministan Yaɗa Labarai a Jamhuriyya ta farko, Alhaji Thanni O.S. Benson, da haɗin gwiwar wasu mutum biyu, suka kafa Kungiyar Ansaruddeen, domin su tabbatar sun bai wa ‘ya’yan Musulmi ilmin zamani mai nagarta, ba tare da an tsangwame su ba.
Sun fara kafa ta farko a Isolo daga nan suka ci gaba da kafa makarantu saboda ‘ya’yan Musulmi su samu ingantaccen ilmi. Waɗannan makarantu sun taimaka wa ‘ya’yan Musulmi a ƙasar Yarabawa. Sun yi kafaɗa da kafaɗa da ‘ya’yan kiristoci da a da suke musu wani gani-gani.
A zagaya, a Arewa da muke kallon mu ne Musulmi na gaske fiye da Yarabawa, a nuna min fitacciyar makarantar boko da wata ƙungiyar addini a Arewa ta kafa kuma ta ɗore har zuwa yau. Makaranta ɗaya da walau Ƙadiriyya, Tijjaniya, Izala ko Shi’a ta kafa, domin ta samar da injiniyoyi, lauyoyi, kafintoci, likitoci da sauransu.
Zan so mutane su nemi ƙasidar Dr. Bala Usman da Alkasim Abba, mai taken “Political Economy of Political Instability: Facing Reality in 7 Northwestern States.” A nan za mu fahimci irin mummunar fahimtar da muka yi wa ilmi a addinin Musulunci.
Allah ya ganar da mu!
___________












