• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, August 23, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Matasa Masu Fusata Sun Ƙone Ofishin ’Yan Sanda

Babban Labari

Daga Wakilinmu by Daga Wakilinmu
June 20, 2026
in Babban Labari
0
Matasa Masu Fusata Sun Ƙone Ofishin ’Yan Sanda

Wasu daga cikin motocin da aka ƙona

13
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Matasa Masu Fusata Sun Ƙone Ofishin ’Yan Sanda

Daga Wakilinmu
__________
Wasu fusatattun matasa sun ƙone Ofishin ’Yan Sanda na Isan da ke Ƙaramar Hukumar Oye a Jihar Ekiti.
Matasan, waɗanda suke zanga-zangar nuna rashin amincewa da zargin cewa ’yan sanda sun harbe wani matashi, sun sha alwashin ci gaba da gudanar da zanga-zangar har sai an yi adalci.

Related posts

Ɗalibin Jami’ar Sojoji Ya Ƙera Robot Mai Kashe Gobara

Ɗalibin Jami’ar Sojoji Ya Ƙera Robot Mai Kashe Gobara

August 12, 2026
Rarara Ya Ƙara Haska Farin Jinin Sheikh Pantami

Rarara Ya Ƙara Haska Farin Jinin Sheikh Pantami

July 31, 2026

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, wani bidiyo ne da aka samu, wanda ke nuna wani matashi kwance cikin jini ya bazu sosai a kafafen sada zumunta, musamman a shafin X, shi ne ya harzuƙa matasan.

Wani sashi na ɓarnar da masu zanga-zanga suka yi

Wani mai amfani da shafin X mai suna Stephen Ayeni ya ce wanda lamarin ya rutsa da shi, ya je filin ƙwallon ƙafa ne domin kallon wasa lokacin da abin ya faru.

Cikin fushi da wannan lamari, an ce matasa masu zanga-zangar sun mamaye ofishin ’yan sandan tare da banka masa wuta.

Wani jami’in ɗan sanda, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:00 na yamma lokacin da wasu mahara suka kai farmaki kan ofishin ’yan sandan.

A cewarsa, ɗaya daga cikin jami’an da suka jikkata, yana cikin mawuyacin hali kuma yana karɓar magani a wani asibiti.

Jami’in ya kuma bayyana cewa an lalata motoci da dama a harin, ciki har da wata bas da jami’an ’yan sanda suka yo hayarta daga Abuja.

Ya ƙara da cewa jami’an Rundunar ’Yan Sandan MOPOL, waɗanda aka sanar da harin yayin da suke kan hanyarsu daga Oye zuwa Isan, sun fafata da masu zanga-zangar, tare da hana su karɓe ikon garin.

Jami’in ya bayyana cewa wasu jami’an da ke bakin aiki sun tsere lokacin harin amma ya ce jami’an tsaro sun sake dawo da iko a yankin tare da maido da zaman lafiya.

An ga mummunar ɓarna a ofishin ’yan sandan, inda motoci biyu suka ƙone a cikin harabar ofishin. Haka kuma, wutar da suka kunna, ta lalata janareta, tagogi, ƙofofi da kuma rufin ginin. A wajen harabar ofishin kuma, an ga wasu motoci uku da suka ƙone ƙurmus.

Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ekiti ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance game da lamarin ba.

Previous Post

Maryam ‘Yar Aljanna

Next Post

Dakta Bukar Usman Zai Gabatar Da Sharhin Littafin Tarihin Al’ummar Lassa

Related Posts

Ɗalibin Jami’ar Sojoji Ya Ƙera Robot Mai Kashe Gobara
Babban Labari

Ɗalibin Jami’ar Sojoji Ya Ƙera Robot Mai Kashe Gobara

August 12, 2026
Rarara Ya Ƙara Haska Farin Jinin Sheikh Pantami
Babban Labari

Rarara Ya Ƙara Haska Farin Jinin Sheikh Pantami

July 31, 2026
Janar Buratai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne – Oba Adekunle Makama
Babban Labari

Janar Buratai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne – Oba Adekunle Makama

July 30, 2026
Next Post
Dakta Bukar Usman Zai Gabatar Da Sharhin Littafin Tarihin Al’ummar Lassa

Dakta Bukar Usman Zai Gabatar Da Sharhin Littafin Tarihin Al’ummar Lassa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Mawaƙi Kizz Daniel Ya Amshi Musulunci

Mawaƙi Kizz Daniel Ya Amshi Musulunci

January 3, 2026
BIU: A Visit to a City on a Plateau (3)

BIU: Ziyarar Babban Birni A Kan Tsauni (3)

December 23, 2023
DAY 3 FESTIVAL OF AUTHORS KADUNA 2024

DAY 3 FESTIVAL OF AUTHORS KADUNA 2024

October 25, 2024
Na Samu Rufin Asirin Rayuwa Dalilin Rubutu Fiye Da Kwalin Digirina – NAS

Na Samu Rufin Asirin Rayuwa Dalilin Rubutu Fiye Da Kwalin Digirina – NAS

September 25, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Professor Bello Sa’idu: The Demise of Literary Icon
  • Bankwana Da Jigon Adabi: Ta’aziyyar Farfesa Bello Sa’idu
  • Musulunci Ba Addinin Tsauri Ko Sakaci Ba Ne…

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Bankwana Da Jigon Adabi: Ta’aziyyar Farfesa Bello Sa’idu

Professor Bello Sa’idu: The Demise of Literary Icon

August 23, 2026
Bankwana Da Jigon Adabi: Ta’aziyyar Farfesa Bello Sa’idu

Bankwana Da Jigon Adabi: Ta’aziyyar Farfesa Bello Sa’idu

August 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.