Daga Adam Ahmad Muhammed
A yau zan yi tsokaci a kan filin Polytechnic da aka wayi gari ‘yan rusau sun dirar masa.
Da farko dai Ganduje bai kyauta ba da ya yanka filayen ya rabar, ko ni a lokacin ban goyi baya ba.
Zan iya tunawa har Daraktan Makarantar aka cire daga kujerarsa don kawai ya ce bai ga dacewar karɓe wa makarantar wannan fili ba.
Duk da cewa shi Daraktan ya san Gwamna Ganduje ya bayar da wani katafaren filin a Badume, wanda ya fi wannan girma nesa ba kusa ba.
A ra’ayin Daraktan shi ne, kamata ya yi a ce wancan na Badume ƙari ne ga makarantar ba wai canji ba.
A kan wannan ra’ayi nasa ne ake ganin ya yi fito na fito da ra’ayin gwamnati, duk da cewa ba wai a bainar jama’a ya yi maganar ba, ya yi maganar ce a WhatsApp Group na abokan aikinsa.
A haka dai aka cire shi kuma aka yanka filayen aka raba wa ‘yan gata. Tabbas babu mai kishin da zai goyi bayan wannan aiki.
An raba filaye bisa tsarin gwamnati. Mafi yawa da aka bai wa sayarwa suka yi, waɗanda suka saya kuma suka bi ƙa’idoji suka gina kayansu. Ni dai a nan ban ga laifinsu ba, tun da dai a doka Gwamna yana da ikon yin haka.
A yanzu kuma an sami sabon Gwamna da yake ganin hakan ba daidai ba ne, kuma yake ganin rushe wajen shi ne kawai hanyar bi.
A ra’ayina wannan mataki ba daidai ba ne, kamata ya yi idan har ta kama dole sai an ƙwace filayen, to a bi hanyar doka, a biya masu gidajen diyya, saboda dai ba ‘yan share wuri zauna ba ne.
Ko bayan an biya su diyya bai kamata a rushe gidajen ba, sai a duba idan akwai abin da za a iya amfani da su sai a yi.
Idan kuma Gwamna yana tsoron kada a tsaya bin doka a ƙarshe a tabbatar musu da gigajen ne ya sa yake rushewa, to an kuma.
Idan har akwai yiwuwar wata doka ko hukuma za ta iya mallaka musu filayen, to gara a bari ta mallaka musu din. Saboda wannan rushewar da ake yi, rushe tattalin arzikin Kanawa da Kano ne. Idan ana ganin wai an ƙwato wa Kanawa filinsu ne, to Kanawa dai aka kashe wai don a ƙwato wa Kanawa da Kano fili.
Duk wanda ya san ciwon dukiya da muhimmancin kuɗi a rayuwar nan zai ji ciwon yadda ake rusa dukiya ba gaira ba dalili. Idan da za ka ji biliyoyin da ake yi wa mutane asara da kanka ba zai iya ɗauka ba.
To kuwa meye hikimar a yi asarar irin wannan dukiya don kawai ana tunanin idan an ƙwace wata kotu ko wata gwamnati za ta iya dawo musu da gidajensu?
Duk wanda ka ga yana murnar wannan abin da ake yi to irin matsiyatan da suka tashi cikin taluci ne, ba su san wani abu arziki ba. Su so suke yi a karya duk wani mai arziki ya dawo kamar su.
Wannan dai kawai ra’ayinane ba shawara ba, saboda su sun ce ba sa buƙatar shawarar kowa da ba a cikinsu yake ba.
Allah Ya raba mu da aikin mai hassada a yayin da ya yi hassadarsa.
Malam Adam Ahmad Muhammed, Daga Jihar Kano.













