• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Wednesday, September 16, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Ta Banka Wa Mijinta, Kishiyarta Da Yara Wuta A Kano

BABBAN LABARI

Daga Wakilinmu by Daga Wakilinmu
May 13, 2026
in Babban Labari
0
Ta Banka Wa Mijinta, Kishiyarta Da Yara Wuta A Kano

Hoton AI: Samfurin yadda aka kama wacce ake zargi

31
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Ta Banka Wa Mijinta, Kishiyarta Da Yara Wuta A Kano

Daga Wakilnmu

Related posts

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

September 9, 2026
Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta

Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta

September 3, 2026
Hoton AI: Samfurin yadda aka kama wacce ake zargi

 

___________

Ana zargin wata mata mai suna Maryam Muhammad da laifin zuba wa mijinta da kishiyarta da yara biyu fetur, sannan ta banka musu wuta a unguwar Hotoro da ke cikin birnin Kano.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, kishiyar tata mai suna Firdausi Musa, mai shekaru 28 tare da ’ya’yanta ƙanana biyu sun samu munanan ƙonewa a sassan jikinsu.

Lamarin, wanda ya faru a daren jiya Litinin a yankin Mai Allo da ke Unguwar Hotoro, ya jefa mazauna yankin cikin firgici, yayin da ake tsare da wadda ake zargin a ofishin ’yan sanda na Mariri.

An bayyana sunayen yaran da suka jikkata da Khadija Ya’u mai shekaru 7 da kuma Isma’il Ya’u mai shekaru 3. Ana kula da lafiyarsu tare da mahaifiyarsu a Asibitin Ƙashi na Ƙasa da ke Dala da kuma Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano.

Mijinsu, Malam Saminu, wanda rahotanni suka ce shi ma ya samu ƙonewa yayin ƙoƙarin ceto su daga wutar, shi ma yana karɓar magani.

Da yake zantawa da jaridar Daily Trust, ƙanin Firdausi mai suna Buhari Musa Sa’ad, ya ce sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 3 na dare, cewa an banka wa ’yar uwarsa da mijinta da yaran biyu wuta daga kishiyarta.

A cewarsa, Firdausi ba ta yi ko makonni biyu ba da komawa gidan aurenta kafin wannan lamari ya faru.

“Firdausi tana da kusan shekaru 28. Yaran da suka ƙone kuwa su ne waɗanda ta zo da su daga aurenta na baya,” in ji shi.

Wata ’yar uwa ga Firdausi mai suna Rukayya ta kuma shaida wa Daily Trust cewa tun kafin harin, Firdausi ta yi ta ƙorafin cewa kishiyarta tana yi mata barazana da tsangwama.

“Mun kasance a kwance a nan, lokacin da aka kawo ta kuma ita da kanta ta gaya mana cewa kishiyarta ce ta zuba mata fetur sannan ta kunna ashana,” in ji ta.

Rukayya ta bayyana cewa tun da farko a ranar, Firdausi ta bar gidan saboda yawaitar barazanar da ake yi mata amma daga baya ta koma, bayan mijinta ya shiga tsakani.

Ƙoƙarin jin ta bakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano bai yi nasara ba kafin kammala haɗa wannan rahoto.

________

Previous Post

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (12)

Next Post

ALHAMDU LILLAH

Related Posts

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?
Babban Labari

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

September 9, 2026
Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta
Babban Labari

Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta

September 3, 2026
KATSINA_2026: Bikin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya
Babban Labari

KATSINA_2026: Bikin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya

August 29, 2026
Next Post
ALHAMDU LILLAH

ALHAMDU LILLAH

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Tsarin Mulki: Jan Hankali Ga Shugabannin Arewa

Tsarin Mulki: Jan Hankali Ga Shugabannin Arewa

July 13, 2023

October 1, 2023

June 27, 2025
Sarkin Gobir: ACF Demands Thorough Investigation and Security Overhaul

Sarkin Gobir: ACF Demands Thorough Investigation and Security Overhaul

August 23, 2024

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • MALAM SULE LAMIDO: Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78
  • ADO GWANJA – Ya Samu Lafiya
  • SUNANTA UMMU-KHULSUM

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

MALAM SULE LAMIDO:  Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78

MALAM SULE LAMIDO: Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78

September 15, 2026
ADO GWANJA – Ya Samu Lafiya

ADO GWANJA – Ya Samu Lafiya

September 13, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.