SHEIKH YAKUBU YAHAYA KATSINA: ZUWAN KA TA’AZIYYAR BUHARI KOYI NE DA HALAYEN MANZON ALLAH (SAW)
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Kwanaki kaɗan da suka gabata, na wallafa wani labari, inda na ambato wata sahihiyar majiya da ta tabbatar mani da labarin cewa Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Uwa Musulmi Mabiya Shi’a na Jihar Katsina, Sheikh Yakubu Yahaya zai kai gaisuwar ta’aziyyar Janar Muhammadu Buhari a Daura.
Wannan labari bai yi wa wasu da dama daga cikin ‘yan Shi’a daɗi ba. Wasu ma har da zage-zage da cin zarafi suka biyo ni baya. Allahu akbar, ni kuwa sai na ga muddin dai mutum “MUSULUNCI” yake yi, irin wanda Manzon Allah Muhammadu (saw) ya koyar, to bai kamata ya ji zafin kira ga aikata alheri ba.
Ya kamata a nan in ƙara tunasar da ‘yan uwa ‘yan Shi’a cewa, gaisuwar ta’aziyya sunna ce ta Manzon Allah (saw). Don haka, idan Sheikh Yakubu ya kai gaisuwar nan, ba laifi ya yi ba, a’a, ya yi koyi ne da Manzon Allah kuma hakan zai ƙara masa martaba da kwarjini, sannan ya ƙara tabbatar da cewa lallai Musulunci yake yi na ƙwarai.
Gaisuwar ta’aziyya wata muhimmiyar ibada ce a cikin Musulunci da take nuna jin ƙai, zumunci da imani da ƙaddara. A lokacin da Musulmi ya rasa ɗan uwa ko aboki, yana daga cikin sunnonin Manzon Allah (SAW) a je a gaishe shi da ta’aziyya, domin rage masa baƙin ciki da ƙarfafa masa gwiwa a kan rashin da ya yi. Wannan aiki yana nuna soyayya da haɗin kai da kuma cika hujjar al’umma ɗaya da Musulunci ya yi kira da ita.

Gaisuwar ta’aziyya tana daga cikin manyan hanyoyin da Musulmi ke nuna tausayi da kulawa ga ɗan uwansa. A hadisin Tirmizi mai lamba 1077, Anas bin Malik (RA) ya ruwaito, Manzon Allah (SAW) ya ce: “Duk wanda ya nuna tausayi ga wanda ke cikin wata musiba, yana da lada kamar tasa.”
Wannan hadisi yana nuna yadda ta’aziyya ke da lada mai yawa, musamman idan aka yi ta cikin kyakkyawar kalma da nasiha mai kwantar da hankali.
Allah a Alƙur’aninsa, Suratul Baƙara, aya ta 155, ya yi kira ga Musulmi da su zama masu juriya da ƙarfafa juna da kalmomi masu daɗi, musamman a lokacin fitina ko rashin wani abu ko mutuwa. Allah (SWT) ya ce: “Za mu jarrabe ku da wani abu na tsoro, yunwa, rashin dukiya, rai da amfanin gona. Kuma ka yi bushara ga masu haƙuri.”
Wannan ayar na nuna cewa baƙin ciki da rashin ɗan uwa jarrabawa ce daga Allah, kuma Musulmi ya kamata ya nuna juriyar imani da taimaka wa ɗan uwansa da kalmomi masu taushi da tausayawa.

Haka kuma Musulunci, addini ne da ya koyar da mu kuma ya nuna mana muhimmancin yafiya ga mamaci. Akwai lokuta inda mamaci ya rasu alhali yana cikin rashin jituwar dangantaka da wani Musulmi. A irin wannan hali, Musulmi yana da haƙƙi da lada mai yawa idan ya yafe wa mamacin. Yafiya a irin wannan lokaci yana jawo rahamar Allah da yardarSa. Allah (SWT) a cikin Suratun Nur, aya ta 22 ya ce: “Ku yafe, ku gafarta. Ashe ba ku so Allah Ya gafarta muku ba?”
Haka kuma, Manzon Allah (SAW), a cikin hadisin Bukhari mai lamba 2,076 ya ce: “Allah Ya ji ƙan wanda ya kasance mai sauƙi idan yana saye, sayarwa da neman haƙƙinsa.”
Don haka yafe wa mamaci yana nuna girman zuciya da kuma tsoron Allah, domin ba wanda ya san irin yanayin da Allah zai karɓi rayuwar bawa.
A rayuwarsa, Manzon Allah bai riƙi mutane da gaba da ƙiyayya ba. Koda kafirai sun cuta masa, yakan yi masu addu’ar shiriya. Akwai misali da yawa kan haka:
Akwai lokacin da mutanen Ɗa’ifa suka yi wa Manzon Allah rotse da duwatsu, amma ya yafe masu, ya nema masu shiriya wajen Allah. Akwai wani Bayahude da ya riƙa zubar da shara da ƙazanta a ƙofar gidan Manzon Allah. Ranar da Manzo (saw) ya ga an daina zuba sharar, sai ya tambaya, me ya faru? Aka ce masa ai wannan Bayahude ba ya lafiya ne. Nan take ya je ya gaishe shi, ya nuna masa jin ƙai da tausayi. Sanadiyyar wannan sai ya musulunta.
Idan har Sheikh Yakubu Yahaya Katsina ko ma shi kansa Sheikh Ibrahim Yakubu Elzakzaky suka je Daura ta’ziyyar Buhari, wallahi su za su amfana fiye da kowa. Domin hakan yana nuna cewa sun yi koyi da Manzon Allah (saw) wajen nuna yafiya da jin ƙai. Sun maida alheri kan cutar da aka yi masu. Hakan kuma zai ƙara masu kwarjini da soyayya daga al’ummar Musulmi gaba ɗaya. Haka kuma za su yi amfani da wannan dama wajen toshe gaba da ƙiyayya tsakanin iyalan mamatan da mabiyansa da kuma nasu iyalan da nasu mabiyan.
Ga wasu mutane da suka ƙaryata labarin da na kawo game da Sheikh Yakubu Yahaya, na yiwuwar zuwa Daura ta’aziyya, to idan ma ƙarya na faɗa, ku sani cewa a Musulunci, akwai wurare uku da ya halatta Musulmi ya yi ƙarya. A hadisin Sahih Muslim mai lamba 2605, an nuna cewa ya halatta Musulmi ya yi ƙarya, a: 1-Wajen sasanta zumuncin musulmin da suka yi saɓani da juna. 2-Wajen farfagandar yaƙi tsakanin Musulmi da Kafirai. 3-Tsakanin miji da mata domin yauƙaƙa soyayya da ƙauna.

Haka kuma, kusan mafi yawa daga manyan Malaman Musulunci na Najeriya, sun je Daura domin gaisuwa. Malamai kamar Sheikh, Farfesa Ibrahim Maƙari, Sheikh, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, Sheikh Abdullahi Bala Lau, Sheikh Yahya Jingir da sauransu, to me zai sa su Malam Yakubu Yahaya su ƙi zuwa? Saboda haka, gaisuwar ta’aziyya wata sunnah ce mai ƙima a Musulunci. Ita ce ke nuna soyayya, tausayi da juriya ga ‘yan uwa a lokacin rashin da suka yi. Hakazalika, yafe wa mamaci musamman idan akwai saɓani tsakaninku yana da matuƙar muhimmanci domin ya shafi rahama da gafara daga Allah. A zamanin da ake fama da ƙiyayya da rabuwa, ya zama wajibi ga Musulmi su riƙa tafiya gaisuwa da yafe wa juna domin tabbatar da haɗin kai da nasarar al’umma.
Allah sa mu dace da daidai kuma ya yafe mana zunubbanmu gaba ɗaya, ya yi mana rahama. Amin-summa-Amin.
__________
Bashir Malumfashi, shi ne Editan Mujallar Taskar Gizago (online)














Allaah yaji Kansa da rahama ya kyautata na mu karshen. Shi ke nan fa, rayuwar!!!. Innalillahi wa Inna Ilaihirraji’un.