Sojan Gona: An Kama Sojan Bogi Mai Muƙamin Manjo-Janar
Daga Bashir Yahuza Malumfashi
__________
Dakarun Rundunar Sojojin Atilare ta 312 (312 Artillery Regiment) ƙarƙashin Runduna ta Ɗaya ta Sojojin Najeriya da kuma Sashe na Ɗaya na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa Maso Yamma, ƙarƙashin Operation FANSAN YAMMA, sun kama wani mutum da ake zargi da yin sojan gona, a yayin wani samame da suka gudanar domin kare martaba da mutuncin Rundunar Sojojin Najeriya, tare da kare jama’a daga ayyukan damfara.

An kama wanda ake zargin, wanda farar hula ne, da misalin ƙarfe 9:50 na safe a jiya Alhamis (11 ga Yuni, 2026), ta hannun dakarun da ke aiki a Strike Force Base Sabo.
Sojan na bogi da aka kama, ana zargin yana yi sojan gona ne da sunan Manjo Janar AT Ibrahim (mai ritaya).
Kamar yadda Hukumar Sojojin Najeriya ta bayyana, a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da binciken farko kan lamarin, inda suka ce da zarar an kammala binciken kuma za su miƙa wanda ake zargin ga hukumomin da suka dace; domin ci gaba da bincike da gurfanar da shi a gaban ƙuliya.
Sojojin na Najeriya sun sake jaddada aniyarsu ta yaƙi da dukkan nau’ukan laifuffuka, ciki har da masu yin sojan gona da sauran ayyukan da za su iya raunana amincewar jama’a ga rundunar soja.
An shawarci jama’a da su kasance cikin shiri tare da kai rahoton duk wani mutum da ke iƙirarin kasancewa soja ba tare da sahihin katin shaida ko wata takardar tantancewa ba. Sojojin Najeriya sun tabbatar wa al’umma cewa za su ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace kan duk wanda aka samu yana amfani da suna da martabar Rundunar Sojojin Najeriya, domin aikata haramtattun ayyuka













