• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, May 25, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda A Ƙafur Jihar Katsina

• Sun Ƙwato Dabbobi 529

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
February 8, 2026
in Babban Labari
0
Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda A Ƙafur Jihar Katsina

Wasu daga dabbobin da aka ƙwato

31
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda A Ƙafur Jihar Katsina

• Sun Ƙwato Dabbobi 529

Related posts

Ta Banka Wa Mijinta, Kishiyarta Da Yara Wuta A Kano

Ta Banka Wa Mijinta, Kishiyarta Da Yara Wuta A Kano

May 13, 2026
Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi

Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi

May 9, 2026

__________

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

A yayin da jami’an tsaro ke ta ƙoƙarin samar da tsaro da zaman lafiya a sassa daban-daban na ƙasar nan, a Jihar Katsina Sojojin Ayarin Forward Operation Base (FOB) Malumfashi, ƙarƙashin Hedikwatar Birged ta 17 ta Rundunar Sojin Najeriya, sun samu gagarumar nasara, bayan sun ƙwato dabbobi 529 daga hannun ‘yan ta’adda, biyo bayan fafata artabu da su a Ƙaramar Hukumar Kafur ta Jihar Katsina.

Sojoji a bakin aiki

Aikin, wanda Laftanar Kanal MM Isa, Kwamandan FOB Malumfashi ya jagoranta, ya biyo bayan samun sahihan bayanan sirri dangane da ’yan ta’adda a yankin Kasuwar Sabo ta Ƙaramar Hukumar Kafur a ranar 7 ga Fabrairu da ta gabata.

Binciken farko ya nuna cewa ana zargin ’yan ta’addar sun shigo ne daga maƙwabciyar Jihar Zamfara kuma an samu tabbacin cewa Idi-A-Ba-Su-Aiki ne yake jagorantar su, wanda ake zargin ƙanin shahararren jagoran ’yan bindiga Ado Aliero ne.

A wata takardar manema labarai daga Ofishin Kyaftin Abayomi Adisa, Muƙaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa Da Jama’a na Rundunar Sojin Birged ta 17, Rundunar Sojin Najeriya, ya bayyana cewa, bayan da suka samu wannan bayanin sirri, sojojin FOB Malumfashi ba su ɓata lokaci ba, suka yi gaggawar tattaruwa suka nufi yankin. Da ganin sojojin suna matsowa, ’yan ta’addar suka fara harbi, sai dai sojojin suka mayar da martani da ƙarfin wuta mafi rinjaye, lamarin da ya tilasta wa ’yan ta’addar tserewa zuwa dazuzzukan da ke kewaye da yankin, tare da ɗaukar wasu daga cikin dabbobin da aka sace.

“Nan take sojojin suka shiga bin sawu cikin himma da ƙaimi, suka cin ma ’yan ta’addar da ke tserewa a tsakanin ƙauyukan Burdugau da Unguwar Mantau a Ƙaramar Hukumar Malumfashi. Lamarin da ya tilasta musu barin dabbobin da suka sace,” in ji Kyaftin Abayomi.

Bayan gudanar da cikakken bincike a yankin, sojojin sun yi galaba kan ’yan ta’addar gaba ɗaya, suka kuma samu nasarar ƙwato jimillar dabbobi 529, waɗanda suka haɗa da shanu 290, tumaki 238, jaki guda ɗaya da kuma babur guda ɗaya. “Abin takaici, shanu 14 da ake zargin ’yan ta’addan sun yi amfani da su a matsayin garkuwa sun mutu, sakamakon musayar wuta a yayin artabun. Aikin bai yi sanadin asarar rai ko rauni a ɓangaren sojoji ba, abin da ke nuna ƙwarewa da ingancin aikin sojojin,” a cewar Kyaftin ɗin.

Ya zuwa yanzu dai an miƙa dabbobin da aka ƙwato ga hukumomin da suka dace, domin tantancewa tare da mayar da su ga ainihin masu su. Shugaban Ƙaramar Hukumar Ƙafur, Surajo Nature da DPO na Ƙafur, Aminu Salihu, su ne masu sa ido kan tantancewa da kuma miƙa dabbobin yadda ya kamata.

Babban Kwamandan Rundunar Soji na Shiyya ta 8 kuma Kwamandan Sashen Aiki na 2 na Rundunar Haɗin Gwiwa (Arewa maso Yamma) Operation FANSAN YAMMA, Manjo Janar Paul Koughna, ya yaba da jarumtaka da ƙwarewar da sojojin suka nuna, tare da tabbatar wa al’umma da ci gaba da jajircewar Rundunar Sojin Najeriya wajen ci gaba da kai farmaki kan dukkan nau’ukan ’yan ta’adda a yankin.

A halin da ake ciki dai, Sojojin FOB Malumfashi suna ci gaba da  sintiri a dukkan yankin, domin hana ’yan ta’adda sake yin wata ɓarna.

Previous Post

Mun Yi Rashi: A Taya Mu Da Addu’a

Next Post

KWANAN WATAN HIJIRIYYA A YAU LITININ

Related Posts

Ta Banka Wa Mijinta, Kishiyarta Da Yara Wuta A Kano
Babban Labari

Ta Banka Wa Mijinta, Kishiyarta Da Yara Wuta A Kano

May 13, 2026
Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi
Babban Labari

Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi

May 9, 2026
Yan ta’addan Daji Kafirai Ne  – Sarkin Musulmi
Babban Labari

Yan ta’addan Daji Kafirai Ne – Sarkin Musulmi

May 8, 2026
Next Post
KWANAN WATAN HIJIRIYYA A YAU LITININ

KWANAN WATAN HIJIRIYYA A YAU LITININ

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Muhammad Salissou Hamissou: Ta’aziyyar Ƙwararren Ɗan Jarida Mai Raya Al’adun Gargajiya

Muhammad Salissou Hamissou: Ta’aziyyar Ƙwararren Ɗan Jarida Mai Raya Al’adun Gargajiya

February 26, 2024
BUNKASA TATTALIN ARZIKIN NAJERIYA: Tsakanin Dangote Da Gwamnatin Tarayya

BUNKASA TATTALIN ARZIKIN NAJERIYA: Tsakanin Dangote Da Gwamnatin Tarayya

July 31, 2024
Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

May 18, 2026
SHARI’AR MUSULUNCI: Bayan Yaƙi Da Baɗala, A Yaƙi Ɓarayin Gwamnati, Hanci Da Rashawa

SHARI’AR MUSULUNCI: Bayan Yaƙi Da Baɗala, A Yaƙi Ɓarayin Gwamnati, Hanci Da Rashawa

November 3, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • POSITIVE COMRADE
  • BUKAR USMAN: The Human Library
  • Sule Lamido’s Theme of Authenticity

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

POSITIVE COMRADE

POSITIVE COMRADE

May 20, 2026
BUKAR USMAN: The Human Library

BUKAR USMAN: The Human Library

May 19, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.