Taya Ni Mu Gyara: Kisan Baƙi Sai Gayya
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

•••••••
Rubutu da marubutan Hausa sun daɗe suna taimakon al’umma ta hanyoyi da dama. Wannan kuwa ya haɗa da yaɗa ilimi, faɗakarwa, har ma da nishaɗantarwa.
Wani fage mai matuƙar muhimmanci da marubutan Hausa ke tallafa wa al’umma, shi ne fagen inganta zamantakewa tsakanin ma’aurata. An samu rubuce-rubuce masu tarin yawa da suka taka rawa wajen yauƙaƙa so da ƙauna tsakanin maza da mata, waɗanda har suka kai ga wasu da dama suka zama ma’aurata.
Ɗaya daga cikin irin waɗannan littattafai, shi ne littafin TAYA NI MU GYARA, wanda Zuwaira Dauda Kolo ta rubuta kuma ake shirin ƙaddamar da shi a ranar Lahadin makon gobe (08-11-2025), idan Allah ya kai mu.
Littafi ne da za a kira da laƙanin “Jagorar Ma’aurata.” Ba ma’aurata kaɗai ba, wannan littafi babban jagora ne ga masoya maza da mata, wanda zai saita masu hanyar zuwa kafa iyali. Yana ƙunshe da shawarwari, nasihohi da amsoshin manya da ƙananan ƙalubalen da ke fuskantar iyalai.
Idan Allah ya yarda, zan yi ƙoƙarin halartar wannan biki, domin ƙaddamar da wannan mashahurin littafi. Haka kuma, ina shawartar ‘yan uwa da abokan arziƙi da su yi ƙoƙarin mallakar wannan littafi, domin kuwa babbar taska ce mai ƙunshe da hajar ilimi.
_______________













