• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, August 14, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Yan Bindiga Sun Halaka Babban Jami’in Soja A Abuja

BABBAN LABARI

Daga Wakilinmu by Daga Wakilinmu
July 28, 2026
in Babban Labari
0
Yan Bindiga Sun Halaka Babban Jami’in Soja A Abuja

Allah ya ji ƙan Kanar Abdulsalam Udeh

44
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Yan Bindiga Sun Halaka Babban Jami’in Soja A Abuja

Daga Wakilinmu
__________
Rahotanni daga Abuja sun bayyana cewa wani babban jami’in sojan Najeriya, mai aiki a ɓangaren leƙen asiri, Kanar Abdussalam A. Ude, ya rasa ransa, bayan da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka harbe shi.

Related posts

Ɗalibin Jami’ar Sojoji Ya Ƙera Robot Mai Kashe Gobara

Ɗalibin Jami’ar Sojoji Ya Ƙera Robot Mai Kashe Gobara

August 12, 2026
Rarara Ya Ƙara Haska Farin Jinin Sheikh Pantami

Rarara Ya Ƙara Haska Farin Jinin Sheikh Pantami

July 31, 2026

Kafar watsa labarai ta PRNigeria ta ruwaito cewa, jami’in na soja ya nuna jarunta da tirjiya wajen tunkarar ‘yan bindigar da suka kai masa hari, domin yin garkuwa da shi a gidansa da ke Unguwar Kurudu, Abuja.

Marigayin, wanda ɗan asalin Jihar Enugu ne, ya kasance ƙwararren jami’i mai jajircewa wajen gudanar da aikinsa kuma ana sa ran za a ɗaga matsayinsa zuwa muƙamin Birgediya Janar a baɗi, sai kuma ga ta Allah ta kasance.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun yi masa kwanton ɓauna ne, jim kaɗan bayan ya isa gidansa, inda suka buɗe masa wuta a lokacin da yake saukowa daga motarsa a yammacin jiya Litinin.

‘Yan bindigar sun yi yunƙurin yin garkuwa da shi amma ya yi musu turjiya, duk da cewa sun fi shi yawa sosai, inda ya ƙi miƙa wuya gare su.

Wasu majiyoyi da ke da alaƙa da harkokin tsaro sun ce juriyar da Kanar Ude ya nuna, ta hana maharan yin nasarar tafiya da shi da ransa. Sai dai daga bisani suka harbe shi sau da dama , lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

A yayin harin, maharan sun kuma buɗe wuta kan wasu daga cikin iyalansa, inda matarsa, direbansa da jami’in tsaronsa suka samu raunukan harbin bindiga masu tsanani a wurare daban-daban. An garzaya da su asibiti, inda suke ci gaba da karɓar magani.

Allah ya ji ƙan Kanar Abdulsalam Udeh

Majiyoyin tsaro sun bayyana Kanar Ude a matsayin jajirtaccen jami’in leƙen asiri, mai matuƙar mutunci, wanda ya ci gaba da nuna ƙarfin hali da nutsuwa ko da yana fuskantar hatsarin mutuwa.

“Wannan jami’in ya yi musu turjiya. Bisa bayanan da masu bincike suka tattara, maharan sun so su yi garkuwa da shi ne amma ya ƙi miƙa wuya, ya kuma yi faɗa da su. Abin takaici, hakan ya jawo ya sadaukar da rayuwarsa,” in ji wata majiya da ke da masaniya kan lamarin.

Har yanzu hukumomin tsaro suna ci gaba da gudanar da bincike, domin gano cikakkun bayanan harin, tare da ƙoƙarin gano waɗanda suka aikata wannan ta’asa domin gurfanar da su a gaban shari’a.

Kafin rasuwarsa, Kanar Ude ya riƙe muƙamai masu muhimmanci da dama a fannin leƙen asirin soja da yaƙi da ta’addanci a cikin Rundunar Sojin Najeriya.

Ya halarci hare-haren soji da dama kan ‘yan ta’adda a Arewa maso Gabashin Najeriya, sannan an tura shi wasu muhimman ayyuka na ƙasa da ƙasa, ciki har da a Jamhuriyar Chadi da Faransa, inda ya taka rawa wajen haɗin gwiwar leƙen asiri da tsaro.

An gudanar da jana’izarsa a Masallacin Mambilla da ke Abuja a yau Talata, bisa koyarwar addinin Musulunci.

Wannan kisan ya sake tayar da hankula kan hare-haren da ake kai wa jami’an soji masu aiki da waɗanda suka yi ritaya, musamman a Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Lamarin ya tunatar da kisan Birgediya Janar Uwem Harold Udokwere (mai ritaya), wanda aka kashe a ranar 22 ga Yunin 2024, bayan wasu ‘yan bindiga sun kutsa cikin gidansa da ke Sunshine Homes Estate, a yankin Lokogoma na Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa an caka masa wuƙa har lahira ne yayin da yake ƙoƙarin kare iyalansa, kafin maharan su tsere da bindigarsa da wasu kayayyaki masu daraja.

Masana harkokin tsaro sun bayyana cewa sabon harin na iya ƙara matsa lamba kan gwamnati da hukumomin tsaro, domin ƙarfafa matakan kariya ga jami’an soji masu aiki da masu ritaya, musamman waɗanda suka taɓa riƙe muƙamai masu matuƙar muhimmanci a fannin ayyukan tsaro da leƙen asiri.

A halin yanzu, bincike kan kisan Kanar Abdussalam A. Ude na ci gaba, yayin da hukumomin tsaro ke ƙoƙarin gano ainihin dalilin harin, tare da tabbatar da an kama waɗanda suka aikata wannan mummunan laifi kuma an hukunta su bisa doka.
__________

Previous Post

A Voice for Eternity

Next Post

General Buratai Is a Great Patriot — Oba Adekunle Makama

Related Posts

Ɗalibin Jami’ar Sojoji Ya Ƙera Robot Mai Kashe Gobara
Babban Labari

Ɗalibin Jami’ar Sojoji Ya Ƙera Robot Mai Kashe Gobara

August 12, 2026
Rarara Ya Ƙara Haska Farin Jinin Sheikh Pantami
Babban Labari

Rarara Ya Ƙara Haska Farin Jinin Sheikh Pantami

July 31, 2026
Janar Buratai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne – Oba Adekunle Makama
Babban Labari

Janar Buratai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne – Oba Adekunle Makama

July 30, 2026
Next Post
General Buratai Is a Great Patriot — Oba Adekunle Makama

General Buratai Is a Great Patriot — Oba Adekunle Makama

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Still Around

Still Around

August 2, 2026
ABDULLAHI ALKWATONAWI: ALLAH JI ƘAN ƊAN UWA DA RAHAMA

ABDULLAHI ALKWATONAWI: ALLAH JI ƘAN ƊAN UWA DA RAHAMA

February 13, 2025
…BUT WHERE IS IFEANYI?

…BUT WHERE IS IFEANYI?

February 26, 2026
GURƁATACCEN HATSI: An Ja Hankalin Hukumomin Jihar Katsina

GURƁATACCEN HATSI: An Ja Hankalin Hukumomin Jihar Katsina

August 20, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Our Daily Message
  • Regulation, Standardisation of Qur’anic Schools Under Way in Katsina
  • Gwamnati Za Ta Samar Da Ingantaccen Tsarin Gudanar Da Makarantun Alƙu’rani A Jihar Katsina

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Our Daily Message

Our Daily Message

August 14, 2026
Regulation, Standardisation of Qur’anic Schools Under Way in Katsina

Regulation, Standardisation of Qur’anic Schools Under Way in Katsina

August 13, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.