• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, September 20, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Nishadi

Tsakanin A’isha Humaira da Umar Baana: Sulhu Alheri Ne

NISHAƊI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
October 31, 2025
in Nishadi
0
Tsakanin A’isha Humaira da Umar Baana: Sulhu Alheri Ne

Sulhu alheri ne

15
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Tsakanin A’isha Humaira da Umar Baana: Sulhu Alheri Ne

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

ADO GWANJA – Ya Samu Lafiya

ADO GWANJA – Ya Samu Lafiya

September 13, 2026
TSAKANIN ALI JITA DA SOJABOY: WANE NE YA FI GASKIYA?

TSAKANIN ALI JITA DA SOJABOY: WANE NE YA FI GASKIYA?

February 15, 2026
Sulhu alheri ne


                  _______________
A ‘yan kwanakin nan, kafafen sada zumunta sun cika da maganganu da rigima tsakanin A’isha Humaira, matar fitaccen mawaƙi Adamu Dauda Kahutu Rarara da ɗan wasan Hausa, Umar Baana. Wannan saɓani da ya samo asali daga maganganun da suka yi ta musaya, ya janyo hankalin jama’a, musamman masoyansu na masana’antar Kannywood.

A batu na gaskiya, ban ji daɗin wannan hatsaniya ba kuma lallai ya kamata Sarki Ali Nuhu da shi kansa Rarara su shigo cikin lamarin nan, domin a yi sulhu da kuma taka wa wannan fitina birki.

A matsayinmu na Musulmi kuma ‘yan Arewa, lallai ne mu zama masu taka-tsan-tsan da rayuwa. Allah (swt) a cikin littafinsa mai girma Alkur’ani, Suratul Hujurat, aya ta 9 yana cewa: “Idan ƙungiyoyi biyu daga cikin muminai suka yi faɗa, to ku sasanta tsakaninsu.” Wannan aya ta Alƙur’ani tana jaddada muhimmancin sulhu da zaman lafiya tsakanin ‘yan uwa Musulmi.

Ya ke babbar mata mai daraja, A’isha Humaira (sunan mahaifiyata ke na), ina son ki sani cewa a yanzu ke matar aure ce, kuma ana kallon ki da ƙima da daraja. Ana kallon ki a matsayin abin koyi ga mata da matasa. Ya kamata ki kiyaye duk wani furuci da halayen da za su iya zubar da mutuncinki da na mijinki. A matsayinki na mace mai aure, ya fi dacewa ki yi haƙuri da komai, ki bar maganar nan don Allah. Kada ki ce za ki zurfafa neman haƙƙinki zuwa kotu. Babu shakka ba a kyauta maki ba kuma Baana bai yi mutunci ba ko kaɗan, musamman da ya kama sunanki da na mijinki a soshalmidiya, yana ƙasƙantarwa. Amma duk da haka, don Allah ki share batun, domin kin riga kin yi sama, ke ba sa’arsa ba ce.

Kai kuma Umar Baana, kana iƙirarin cewa kai mai gyara ne, to ka sani, bai dace ba ko kaɗan ka ɗauko cin zarafi ka jefa ga matar aure, wai da sunan gyara ko nasiha kuma ka ɗora a soshalmidiya. Kai ma fa kana da iyali, ka haifa. Shin yaya za ka ji a ce wani ya ci zarafin matarka ko ɗiyarka, idan sun aikata wani kuskure a rayuwa? Don Allah ka kiyaye, ka san abin da ya kamata da wanda bai kamata ba. Neman suna ba hauka ba ne.

A wannan gaɓa, ina kira ga A’isha Humaira da Umar Baana, don Allah ku zauna ku yi tunani, ku sulhunta da juna. Ku yi haƙuri kuma ku gafarta wa juna. Domin kuwa babu abin da ke da daraja fiye da zaman lafiya, mutunci da sulhu; ba rigima da saɓani ba. Ku sani cewa shi sulhu alheri ne, kamar yadda Manzon Allah (saw) ya ce: “Shin ba zan gaya muku abin da ya fi daraja fiye da azumi da salla da sadaka ba? To shi ne sulhu tsakanin mutane, domin rigima tsakanin mutane tana ruguza addini.”

Wannan hadisi daga Abu Dawud, yana nuni da cewa zaman lafiya da fahimta sun fi rigima da tsokana daraja a gaban Allah. Allah sa mu dace, Amin.
______________

Previous Post

Aure Sunnar Manzo (saw): Isma’il Angon A’isha

Next Post

Taya Ni Mu Gyara: Kisan Baƙi Sai Gayya

Related Posts

ADO GWANJA – Ya Samu Lafiya
Nishadi

ADO GWANJA – Ya Samu Lafiya

September 13, 2026
TSAKANIN ALI JITA DA SOJABOY: WANE NE YA FI GASKIYA?
Nishadi

TSAKANIN ALI JITA DA SOJABOY: WANE NE YA FI GASKIYA?

February 15, 2026
Rasuwar ‘Yar Kannywood Jidda Fulani: Ko Furodusa Aminu Saira Ya Kyauta?
Nishadi

Rasuwar ‘Yar Kannywood Jidda Fulani: Ko Furodusa Aminu Saira Ya Kyauta?

December 27, 2025
Next Post
Taya Ni Mu Gyara: Kisan Baƙi Sai Gayya

Taya Ni Mu Gyara: Kisan Baƙi Sai Gayya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Yan Bindiga Sun Halaka Babban Jami’in Soja A Abuja

Yan Bindiga Sun Halaka Babban Jami’in Soja A Abuja

July 28, 2026
TAURARON GIZAGAWA: ABDULHADI DABO

TAURARON GIZAGAWA: ABDULHADI DABO

July 20, 2023
ALLAH JI ƘAN INJINIYA TUKUR

ALLAH JI ƘAN INJINIYA TUKUR

February 27, 2026
SADAUKARWA: Tinubu Tsaye Yake Ga Manufofin Najeriya Da Afirka – Minista Idris

SADAUKARWA: Tinubu Tsaye Yake Ga Manufofin Najeriya Da Afirka – Minista Idris

October 22, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso
  • JAGORA: Leader of the Masses
  • MALAM SULE LAMIDO: Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

September 20, 2026
JAGORA: Leader of the Masses

JAGORA: Leader of the Masses

September 17, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.