Rai Baƙon Duniya: Allah Ya Ji Ƙan Abokinmu Yahaya Skito
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

•••••••
Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!
Allahu Akbar! Babu shakka daga Allah muke kuma zuwa gare shi za mu koma. Tabbas, kowane rai sai ya ɗanɗani mutuwa. Kamar kuma yadda a haƙiƙa, kowane mutum da akwai iya adadin lokacin da zai rayu a duniya.
Da safiyar nan na ci karo da labarin rasuwar ɗan uwa kuma abokinmu, Malam Yahaya Skito, a Kaduna.
Na fara sanin Yahaya Skito ne tun farkon shigowar finafinan Hausa, inda na riƙa ganin sunansa yana gilmanya a cikin finafinai, a matsayin ɗaya daga cikin masu ma’aikatan da ke karakaina wajen shirya finafinan Hausa. Daga bisani kuma, a shekarar 2006, Allah ya sa muka haɗu da shi a Kaduna.
A wannan shekara ta 2006, mun yi aiki da shi a Kamfanin Wallafa Jarida na Public Agenda. Tun daga lokacin kuwa zumuncinmu ya ɗore. Mukan daɗe ba mu gana ido-da-ido ba amma godiya ga Soshalmidiya, inda mukan ga juna kuma mu yi musharaƙa, musamman ma ta kafar Facebook.
Babu shakka Malam Yahaya mutum ne marar damuwa. Ba shi da wani hali na kushewa. Mutum ne mai son raha da barkwanci. Muna roƙon Allah ya ji ƙan shi da rahama, ya sa ya huta. Mu kuma da muka rage, Allah ya ba mu ikon cikawa da imani, idan tamu mutuwar ta zo. Amin-Summa-Amin!
_______________













