
LITTAFIN YAMTARAWALA: Babban Jigon Farfaɗo Da Tarihi Ne – Henry Akubuiro
Daga Bashir Yahuza Malumfashi
~~~~~~~
Marubucin littafin ‘Yamtarawala – The Warrior King’ (Yamtarawala: Jarumin Mayaƙin Sarki), Henry Akubuiro ɗan jarida ne kuma marubucin ƙirƙira. A kwanan nan littafinsa na wasan kwaikwayo, ‘Yamtarawala – The Warrior King’ ya ciri tutar zama ɗaya daga cikin uku da suka tsallaka siraɗin ƙarshe na Gasar Adabi ta Najeriya ta bana, wadda Kanfanin Sarrafa Iskar Gas na Najeriya (NLNG) ke shiryawa duk shekara. Marubuci ne da ya ƙware wajen rubuta wasannin kwaikwayo, zube, waƙoƙi, littattafan yara, tarihin mutane da sauransu. Shi ne ya rubuta littafin ‘Prodigals in Paradise’ da ‘Vershima and the Missing Cow’ da ‘Adventures of Bingo and Bomboi’ da kuma ‘Little Wizard of Okokomaiko.’ Ya sha samun nasara a gasar rubuce-rubuce da dama, waɗanda suka haɗa da Gasar Adabi ta Matasan ‘Yan Rahoto da BBC ke shiryawa da Gasar Rubutun Insha’i da Ma’aikatar Matasa da Wasanni ta Gwamnatin Tarayyar Najeriya ke shiryawa da Gasar Gwarzon Ɗan Jaridar Shekara da Ƙungiyar Marubuta ta Najeriya (ANA) ke shiryawa da Gasar Rubutun Zube da ANA/Lantern Books ke shiryawa da sauransu da dama. Haka kuma shi ne Shugaban Alƙalan Gasar Adabin Afirka ta James Currey da aka gudanar a 2023. A yanzu haka kuma shi ne Mataimakin Editan Jaridar Saturday Sun.
~~~~~~~

Muna taya ka murnar nasarar zuwa siraɗi na ƙarshe a Gasar Rubutun Adabi ta Najeriya. Shin yaya kake ji a ranka dangane da wannan nasara?
Kamar yadda aka sani, wannan gasa ta rubutun adabi a Najeriya, wacce Kamfanin Sarrafa Iskar Gas na Najeriya (LNGN) ke ɗaukar nauyin shiryawa duk shekara, ita ce gasa mafi girma a Afirka kuma ɗaya daga cikin mafi kwarjini a duniya. Babu shakka Najeriya ce uwa mabada mama a fagen adabi a Afirka, tun daga zamanin su Soyinka da Achebe, har zuwa wannan zamani da marubuta irin su Chimamanda ke riƙe da kambi. Saboda haka a ce marubuci ya cin ma zuwa wannan siraɗi a babbar gasa irin wannan a Najeriya, inda ‘yan takara sama da 140 suka fafata, lallai wani babban al’amari ne da zai inganta harkata ta rubutu. Wannan kuma ya nuna cewa lallai mutum yana kan hanya mai ɓullewa.
Ko za ka yi mana ƙarin haske dangane da littafinka na wasan kwaikwayo da ya samu nasarar zuwa siraɗin ƙarshe a wannan gasa, wato ‘Yamtarawala – The Warrior King?’ Sunansa ma kawai na musamman ne.
Wato “Yamtarawala” suna ne da ya samo asali daga Arewa Maso Gabashin Najeriya, inda a kansa aka shirya wasan kwaikwayon. Wannan littafi mai suna ‘Yamtarawala – The Warrior King’ wasan kwaikwayo ne da ke da nasaba da tarihin wani shahararren sarki mai suna Yamtarawala, wanda mahaifinsa ya kasance tsohon Sarkin Ngazargamu, babban birnin Daular Kanem-Borno. A kitsa wasan ne dangane da labarin tirka-tirkar da ta faru yayin gadon sarautar Ngazargamu, bayan mutuwar sarkinsu.
Sai dai kuma abin takaici shi ne, Yamtarawala bai samu nasarar hawa gadon sarautar ba, ƙaninsa Umar ya kasa shi. Bai ji daɗin wannan kaye ba ko kaɗan, don haka sai ya haɗa dakaru magoya bayansa, su 72, suka nausa kudancin daular, suna yaƙar ƙananan yankuna, da nufin kafa tasa ƙasar. A haka ya yi nasarar kafa Daular Biu, a Kudancin Jihar Borno. A yanzu haka, Masarautar Biu ita ce ta biyu a girma a dukkan masarautun da ke Jihar Borno. Abin da ya biyo bayan mulkinsa a wannan sabuwar masarauta, yana ƙunshe da rikice-rikice da tirka-tirkar siyasa, waɗanda duk an zayyana su a cikin wannan wasan kwaikwayo.
Bayan ƙayataccen labari na musamman da ke littafin nan, shin wane tasiri zai yi a rayuwar al’ummar wannan zamani?
Wato tun da farko dai, ni na ci karo da labarin nan ne cikin wani littafi mai suna ‘Tarihin Biu.’ Littafin, ya ƙayatar da ni matuƙa. Dokta Bukar Usman, Shugaban Ƙungiyar Manazarta Al’adun Najeriya ne ya rubuta shi. Nan take tunanina ya nuna mani cewa lallai zan iya rubuta wasan kwaikwayo daga labarin. Kuma abin da ya ba ni mamaki shi ne, babu wanda ya hango wannan fasaha da na hango. Haka kuma na lura da cewa ya zuwa yanzu, marubutan adabi a Najeriya ba su yi rubutu a kan wannan zamanin na Yamtarawala ba. Daular Kanem-Borno na ɗaya daga shahararrun dauloli a Afirka. Ta yi tashe da sa’anninta, irin su daulolin Songhai, Mali, Ethiopia, Oyo, Benin, Ghana da sauransu. Ta ƙunshi dukkan yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya na yau, har ma da kusan dukkan sassan Chadi, Arewacin Kamaru, Kudancin Libya da Kudu Maso Gabashin Jamhuriyyar Nijar.
Mun daɗe muna da’awar cewa a dawo da koyar da darasin tarihi a manhajar makarantunmu. Wannan littafin ya samar da hanyar koya tarihi ta hanyar wasan kwaikwayo. A kwanaki da nake kallon shirin Big Brother Naija, na faɗi ba nauyi cikin kunya, domin ‘yan wasan, waɗanda shekarunsu suka kama daga 20 zuwa 30 sun kasa amsa tambayar lokacin da aka fara Yakin Basasar Najeriya. Akwai ma daga cikinsu da a kan jahilci, ya ce ai ƙasar Kamaru tana cikin Ƙasashen Ƙawancen Bunƙasa Tattalin Arziƙi na Afirka ta Yamma (ECOWAS). Wani daga cikinsu kuma ya gaza faɗin sunan Babban Birnin Jihar Bayelsa, wacce aka ƙirƙiro a 1996, shekara 27 kacal da ta gabata. Wannan ke nuna cewa, Najeriya da ake wa kirari da Giwar Afirka amma tana ƙyankyashe jahilai? Ba za mu taba amincewa da wannan tsarin ba.
Kuma wani abin lura shi ne, dama akwai rashin fahimta sosai da ake yi wa Arewacin Najeriya, musamman ma daga wasu daga cikinmu ‘yan Kudu. Da yawa daga cikinmu ba mu da masaniya game da tarihi ko halayen al’ummar Arewa. Dalili ke nan ma ake ta samun saɓani da rashin fahimtar juna a tsakani. Haka ma a Arewa, akwai mutane da yawa da ba su fahimci halaye da al’ummar Kudu ba.
Duk da cewa tarihin al’adun Hausawa na dauri ya samu wakilci a adabin Najeriya, mai yiwuwa saboda yawan su, amma ba haka abin yake a Arewa Maso Gabas ba. Idan ka duba, mafi yawan littattafan wasan kwaikwayo da ake da su a Najeriya, mafi yawansu sun fito ne daga Kudancin ƙasa. Wannan giɓin yana nan yana kallon mu a kullum. Kuma wai ba haka yana nuna cewa babu marubutan wasan kwaikwayo a Arewa ba ne. Kawai ina ganin marubutanmu ne har yanzu ba su ankara da ɗimbin abubuwan tarihi da ke jiran a yi rubutu a kansu ba daga wannan yanki.
A lokacin da Abubakar Adam Ibrahim ya rubuta littafinsa mai suna ‘A Season of Crimson Blossom’ daga mahangar Arewa, ai an ga yadda ya samu gagarumar tarba ko’ina, nan da nan. Wannan ya faru ne saboda zaren labarin da zubi da tsarinsa a ɓoye yake a can baya, ba a cika kula shi ba a tsarin adabin Najeriya. Don haka irin waɗannan labaru, suna nan suna jiran a haƙo su, a amayar da su.
Dalili ke nan ya sa na ƙuduri aniyar ɗaukar ƙalubalen, domin samar da wani abu mai daraja daga al’adun al’ummar Daular Kanem-Borno da kuma na ‘yar uwarta, Daular Biu. Yana ɗaya daga cikin abin da ya rataya ga wuyanmu, a matsayinmu na marubuta, mu yi rubutu kan abubuwan da suke ɓoye, mu bayyana labarinsu, koda kuwa daga ina suka fito.
Idan za mu iya tunawa, ai Farfesa Ola Rotimi Bayarabe ne amma ya rubuta ƙayataccen wasan kwaikwayo na ‘Ovonramwen Nogbaisi’ wanda labari ne da ya fito daga Daular Benin. A yau wannan littafi fitacce ne da ya karɓu a Afirka. Haka kuma idan ka lura da yadda Farfesa Wole Soyinka ya sarrafa tarihi a littafinsa na ‘Death and the King’s Horseman’ ba sai an tsaya yi maka bayanin cewa, babu shakka wasannin kwaikwayo masu jigon tarihi suna haskaka adabi da kuma rayuwar al’umma ta gargajiya ba. Kana magana ne kan wata rayuwa da ta shuɗe, wacce ba mu ɗanɗane ta a zahiri ba, rayuwar da ke cike da abubuwan ban sha’awa da mamaki, wacce kuma za ta ƙara mana ilimi a tamu rayuwar.
Kuma ka dubi abin da J.P. Clark ya yi a littafinsa na ‘Ozidi Saga’ wanda ya samar daga almarar Izon – ya ƙayatar sosai!
Shi jarumi Yamtarawala a tarihin al’ummar Bura/Babur da ke Jihar Borno, sun ɗauke shi kamar yadda Yarabawa suka ɗauki jarumi Oduduwa da sarauniya Moremi ne a fagen jarumta, a matsayinsu na waɗanda suka kafa masu daula. Haka kuma za a iya kwatanta shi da Amina Sarauniyar Zazzau, ta fuskar jarumta a fagen yaƙi. Wani abin burgewa kuma shi ne, an haifi Sarauniya Amina a shekarar 1533 kuma ta yi mulki a tsakiyar ƙarni na 16. Tana ‘yar shekara biyu da haihuwa, a lokacin da Yamtarawala daga Ngazargamu ya sauka a yankin Biyu, ya mamaye shi kuma ya kafa Daular Biu, wacce har yanzu take da karsashi a matsayinta na masarauta da ke da harshe har zuwa Gombe da Adamawa. Haka kuma al’ummar Bura/Babur suna ɗaukar Yamtarawala, kamar yadda al’ummar ƙasar Zulu ke ɗaukar Sarki Shaka ko kuma kamar yadda al’ummar Daura ta Jihar Katsina ke ɗaukar Bayajidda, ta fuskar jarumtaka. Haka ma kamar yadda al’ummar Daular Mali ke ɗaukar Sarki Mansa Musa.
Dukkan waɗannan jarumai da na ambata, an yi rubuce-rubuce a kansu a adabin Afirka, musamman ma dai wasan kwaikwayo. Sai dai babu wanda ya yi maganar Yamtarawala. A ce muhimmin mutum kamar Yamtarawala, wanda ya samar da muhimmiyar daula a Arewa Maso Gabas, su ne masu gina ƙasa na farko a Najeriya. Su da mutanensu da waɗanda suka biyo bayansu, su ne masu kishin gina ƙasa da za mu yi bugun ƙirji da alfahari da su. Dangane da haka, batun kishin ƙasa da al’umma da gina su, su ne ƙunshiyar wannan littafi wasan kwaikwayo a tarihance.
Wannan wasan kwaikwayo zai yi amfani wajen koyon hikimar sasanta rikici. A misali, a lokacin da Yamtarawala ya yi rashin nasarar samun sarautar Ngazargamu, Sarki Umar ya hau karaga; maimakon ya tsaya gida ya yaƙe shi, sai ya fita waje neman tasa daular sabuwa, domin ya mulka kuma daga bisani ya samu.
Yamtarawala ɗan kishin ƙasa ne kuma jarumi, babu shakka a wannan batu. Jarumi kamar Igodo, Ogiso na farko na Daular Igodomigodo, wacce bisani ta rikiɗe zuwa Daular Benin. Ina ƙalubalantar wanda ya taba jin batun Jarumi Yamta a Najeriya, domin an kusa ɓatar da tarihi ga mutanen zamanin nan. Saboda haka, irin wannan littafi na ‘Yamtarawala – The Warrior King’ tamkar wani mabuɗi ne da zai buɗe ƙofar tarihi. Haka kuma an tsara shi a sigar ingantaccen wasan kwaikwayo, wanda za a iya nuna shi a daɓe ko kuma a allunan fim, wanda ya kawo wata fasaha ta daban ga al’ummar Najeriya.
Wannan wayewar kai da jarumtar kafa dauloli da ka ambata a wannan littafi na wasan kwaikwayo, al’amarin ya faru ne kafin zuwan Turawan Mulkin Mallaka Najeriya ta Arewa?
Babu shakka wannan muhimmin abin tarihi ne. Arewacin Najeriya ya sha wahalar mulkin mallaka har kashi biyu, ɗaya a hannun Larabawa, ɗaya kuma a hannun Turawa. Mu kuwa mutanen Kudu, iri ɗaya kaɗai muka ɗanɗana – na Turawan Birtaniya. Idan ka karanta littattafan Chinua Achebe, ‘Things Fall Apart’ da littafin ‘Arrow of God’ ko kuma littafin Wole Soyinka, ‘Death and the King’s Horseman’ za ka samu waɗannan bayanan. Za ka fahimci yadda aka samu karon barta tsakanin al’adu, tsakanin addinin Kirista da na gargajiya.
A littafin ‘Yamtarawala – The Warrior King’ na waiwayi tarihin baya a ƙarni na 16, domin bayyana wannan muhimmin al’amari. Kamar yadda tarihin yake a zahiri, haka ma a cikin wannan wasan, an bayyana rikice-rikice tsakanin al’adu da ƙabilu. Haka kuma an bayyana dangantakar da ke akwai tsakanin al’ummun dauri na Afirka ta Arewa da kuma na Kudancin Nahiyar Asiya, waɗanda suka yi zamani ɗaya da Yamtarawala. A gani na, marubuta adabi a Najeriya, ba su yi wa wannan ƙarni na Yamtarawala adalci ba.
Dalili ke nan ya sanya na ce wannan wasan kwaikwayo tamkar ƙaddamar da sabon aiki ne. An nuna al’ada, kaɗe-kaɗe da raye-raye da waƙe-waƙe da yare da suturun da aka yi amfani da su, ba waɗanda muka saba gani ko ji ba ne a gidajen wasannin kwaikwayo ko na silima a Najeriya. Wannan wani sabon al’amari ne na daban, mai kama zuciya. Ya zama wajibi a matsayinmu na marubuta, mu bayyana tarihinmu da bambance-bambancenmu. Kai in gajarce maka labari, yanzu haka akwai wanda ke tattaunawa da kamfanin da ya wallafa littafin, dangane da samar da fim ɗinsa. Abin akwai ƙayatarwa kam.
To yaya ka sha haƙilon bincike, ganin cewa kai ba mutumin Arewa Maso Gabas ba ne?
Wannan tambayar ta sa na tuno da shararren marubucin wasan kwaikwayon nan na kowane zamani, William Shakespeare, yadda ya tsara wasannin kwaikwayon mutanen Rum, duk da cewa shi Baturen Scotland ne. Dubi wasan kwaikwayon Julius Caesar na ‘The Tragedy of Anthony and Cleopatra’ da ‘Coriolanus and Titus Andronicus.’ Dukkan waɗannan wasannin kwaikwayo, a ƙarni na 16 aka samar da su ko makamancin haka. A yau, ga shi har yanzu muna nazarin su a matsayin litattafan adabi a makarantun da ke faɗin duniyar nan.
Wannan shi ke ishara da yadda babban tarihi ke kasancewa idan aka danganta shi da adabi. Har kullum akwai dangantaka tsakanin adabi da tarihi. Kada kuma mu mance da babban wasan kwaikwayo na Shakespeare mai suna ‘Macbeth’ wanda a cikinsa aka yi hasashen mulkin Sarki Duncan IV na ƙasar Scotland ko kuma wasan kwaikwayon ‘King Lear’ wanda aka kitsa kan al’amuran sarauta. Waɗannan wasannin kwaikwayo, har zuwa yau suna da tasiri. Yanzu ɗauki misalin wasan kwaikwayon ‘Murder in the Cathedral’ na marubuci T.S. Eliot, wasan da aka rubuta bisa wani abin tarihi da ya faru a ƙarni na 12.
A ta ɓangarena, da na tashi rubuta littafin nan, sai da na tashi takanas na je Masarautar Biu, a shekarar 2016, duk kuwa da barazanar al’amuran tsaro da ke akwai a lokacin. Tun da farko dai ni ban ma san akwai wannan masarauta ba, har sai da na karanta littafin Bukar Usman mai suna ‘Tarihin Biyu.’ Kafin lokacin, ban san komai ba dangane da al’ummar Bura ko Babur ba. Amma lokacin da na ziyarci yankin, na gamu da abubuwan mamaki. Na ga yadda mutanen ke da karimci da yanayin ƙasarsu mai kyau da ban sha’awa, yanayin da ban tsaba gani ba a rayuwata. Na ga kwarurruka da tsaunuka da shimfiɗaɗɗar ƙasa da duwatsu da kuma al’adu masu burgewa. Kuma wannan fa duk wani yanki ne daga cikin Najeriya, mai ƙunshe da al’adun jarumai. Mutun zai ga wadannan abubuwa a duk lokacin da ya ziyarci fadar Sarki. Zai ga kayan tarihi da aka adana na tsawon shekaru 500.
Ashe ka sadaukar da kai sosai yayin wannan ziyarar bincike. Haka ne?
Babu shakka kai tsaye mutum ba zai iya fahimtar irin sadaukarwar da na yi ba, a yayin binciken wannan aikin. Na tarbi aradu da faɗin kaina – na cire tsoron ‘yan Boko Haram da masu kama mutane don kuɗin fansa. Sau biyu na ziyarci yankin nan na Arewa Maso Gabas, domin kuwa sai da na koma a bara, domin kammala aikin wannan littafi na Yamtarawala. A wannan tafiya ta biyu, na ziyarci wurare daban-daban, ciki har da fadar Sarki, inda na gana da masu kula da kayan tarihi na masarautar. Na kuma ziyarci ƙananan hukumomi daban-daban da ke ƙarƙashin masarautar, domin ganin komai da idona.
Haka kuma baya ga waɗannan ziyarce-ziyarce, na amfana sosai da littafin Bukar Usman mai suna ‘A History of Biu (Tarihin Biu), wanda ke ƙunshe da muhimman bayanai masu yawa da ƙayatarwa dangane da tarihi da al’adun al’ummar Biu. Ina matuƙar farin ciki a yau, ganin cewa na kitsa tarihinsu cikin taswirar adabi da gargajiyar Najeriya. Kada fa mu mance, Jihar Borno da ma dukkan yankin Arewa Maso Gabas suna fama da matsalar tsaro na fiye da shekara 12 amma sai ga ni daga wani yanki na Najeriya, na tunkari dukkan ƙalubale, na karrama tarihi da al’adunsu. Na yi murna ƙwarai, ganin cewa na samu nasarar saka farin ciki a fuskokin al’ummar yankin, a lokacin da suke cikin jimami. Idan har na samu goyon baya da mai ɗaukar nauyi ta fuskar kudi, zan ɗauki wasan kwaikwayon nan, ina nuna shi sako da lungu na Arewa Maso Gabas, musamman ma sansanonin ‘yan gudun hijira. Haka kuma zan nuna shi a sassa daban-daban na ƙasar nan, domin samar da canji dangane da al’amuran wasannin kwaikwayo a ƙasar nan.
~~~~~~~
An wallafa wannan tattaunawa ce a Jaridar Guardian ta ranar 27 ga Agusta, 2023. Bashir Yahuza Malumfashi ya fassara a Jaridar Taskar Gizago (a intanet)
~~~~~~~













