• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, July 10, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

ABIN DA YA SA AKE RAINA MAGANAR WASU “MALAMAI”

TSOKACI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
July 16, 2024
in Gizago
1
ABIN DA YA SA AKE RAINA MAGANAR WASU “MALAMAI”

Sheikh Mahmud Gumi, Sheikh Albani Zaria da Sheikh Ja'afar Mahmud Adam (Allah Ya ji ƙan su da rahama)

97
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

ABIN DA YA SA AKE RAINA MAGANAR WASU “MALAMAI”

Sheikh Mahmud Gumi, Sheikh Albani Zaria da Sheikh Ja’afar Mahmud Adam (Allah Ya ji ƙan su da rahama)

√ GABATARWA:
Babu shakka Allah Ya karrama malamai kuma ya yabe su sosai a wurare da yawa a cikin littafinSa mai girma (Alkur’ani). Sai dai kuma ba kowane malami ne ya cancanci yabo da karramawa ba, sai MALAMIN ALLAH, wato “auliya’ullahi” wanda Allah Ya yi wa alƙawarin: “laa khaufun alaihim walahum yahzanun.” Wannan yake nuna cewa ke nan akwai gurɓatattun malamai, masu ci-da-ceto, waɗanda ko kaɗan ba za su samu irin waccan karramawar daga Allah ba. A wannan taƙaitaccen tsokacin, zan bayyana wasu ‘yan dalilai ƙalilan da suka sanya al’umma ke wa wasu “malamai” gani-gani a wannan zamani. A gani na, ga kaɗan daga cikin dalilan:

Related posts

Tattaunawar Ɗan Jarida Da Bazawara ‘Yar Tuwo-Tuwo

Tattaunawar Ɗan Jarida Da Bazawara ‘Yar Tuwo-Tuwo

June 23, 2026
Ilimin Zamani: Babban Ƙalubale Ga Al’ummar Musulmin Arewa

Ilimin Zamani: Babban Ƙalubale Ga Al’ummar Musulmin Arewa

June 22, 2026

~~~
1 √ Malaman baya da suka yi shuhura, kamar Sheikh Gumi, Ja’afar Mahmud Adam, Albany Zaria suna da tawali’u da gudun duniya. Ba su yin tarayya da masu mulkin da suke zaluntar al’umma, balle su riƙa ba su kariya.

2 √ Su kuwa wasu daga fitattun malaman wannan zamanin, har rige-rige suke wajen ba azzaluman masu mulki kariya.

3 √ Marigayi Sheikh Gumi ya yi rayuwar Zuhudu, bai tara dukiyar haram ba. Har ya mutu suturunsa ƙidayayyu ne. Bai da gida a Abuja ko Legas, bai da babbar motar kece raini.

4 √ Malaman yanzu sun tsunduma ga son duniya da ƙyaleƙyalenta. Su ne da manyan suturun kece raini. Su ne da shiga manyan mitoci cikin ayari kamar gwamnoni. Su ne da manyan gidaje a manyan birane. Alhali mabiyansu suna cikin talauci da buƙata.

5 √ Marigayi Sheikh Mahmud Gumi, a duk lokacin da aka kawo masa zakka, komai yawan ta, a nan take yake rarraba wa almajiransa da suke da buƙata.

6 √ Wasu manyan malaman yanzu kuwa, daga mabiyansu suke tara dukiya. Ko dai su sallamar da mabiyansu ga ‘yan siyasa ko kuma su riƙa tattara sadakar da ake bayarwa domin amfanin kansu. Ko makaranta suka gina, ɗan talaka ba zai iya karatu a cikinta ba saboda tsadar kuɗin makaranta da suke sakawa.

7 √ Marigayi Sheikh Ja’afar ya kasance mai fayyace gaskiya ga masu mulki, kamar yadda yake faɗakarwa ba tare da kare wata ƙungiyar addini ba. A matsayinsa na ɗan Ƙungiyar Izalatul Bid’a wa Iƙamatussunna, ko ita ta kauce hanya, yana bayyanawa tare da neman a gyara. A lokacin da gwamnati ta ba shi shugabancin Hukumar Hizba ta Jihar Kano, da ya gano cewa ba da gaske ake ba wajen tabbatar da gaskiya, sai ya aje muƙamin, domin abin ya yi karo da aƙidarsa ta jaddada gaskiya da son kawo gyara.

8 √ Marigayi Sheikh Albany Zaria ya kasance tsayayyen malami mai cin gashin kansa. Bai zama ci-ma-zaune ba, wanda ke jiran ɓarayin gwamnati su ba shi zakka ko sadaka ba. Sana’a yake yi sosai kuma yake sadaukar da abin da ya samu wajen gina makarantu da wallafe-wallafe domin karantar da mabiyansa da ‘ya’yansu.

9 √ Ke nan babban abin da zai sa a riƙa daraja malami kuma a riƙa sauraren maganganunsa shi ne, ya nuna da gaske yake kan da’awarsa. Ya kasance mai tausayi da jin ƙan mabiyansa.

10 √ Ya kamata malamai su tsaya a matsayinsu na gaskiya da gaskiya – magada annabawan Allah. Su tsaya kan gaskiyar koyarwa bisa Igiyar Allah. Su daina haifar da rarraba kan al’umma da sunan ƙungiyanci. Su zamanto masu son al’umma da kishin su na gaskiya.
~~~

Previous Post

ƊANLADI HARUNA

Next Post

KO ME YA SA MABIYA PETER OBI SUKA RIƘA MURNAR MUTUWAR HON. EKENE ABUBAKAR ADAMS?

Related Posts

Tattaunawar Ɗan Jarida Da Bazawara ‘Yar Tuwo-Tuwo
Gizago

Tattaunawar Ɗan Jarida Da Bazawara ‘Yar Tuwo-Tuwo

June 23, 2026
Ilimin Zamani: Babban Ƙalubale Ga Al’ummar Musulmin Arewa
Gizago

Ilimin Zamani: Babban Ƙalubale Ga Al’ummar Musulmin Arewa

June 22, 2026
Taɓarɓarewar Tsaro A Najeriya: Janar Buratai Ya Buƙaci A Ɗauki Matakan Gaugawa
Gizago

Taɓarɓarewar Tsaro A Najeriya: Janar Buratai Ya Buƙaci A Ɗauki Matakan Gaugawa

June 16, 2026
Next Post
KO ME YA SA MABIYA PETER OBI SUKA RIƘA MURNAR MUTUWAR HON. EKENE ABUBAKAR ADAMS?

KO ME YA SA MABIYA PETER OBI SUKA RIƘA MURNAR MUTUWAR HON. EKENE ABUBAKAR ADAMS?

Comments 1

  1. ydjyedih says:
    1 year ago

    ABIN DA YA SA AKE RAINA MAGANAR WASU “MALAMAI” – Taskar Gizago
    aydjyedih
    ydjyedih http://www.g28c87jwqd0e6tn7577l28030vmgp5ohs.org/
    [url=http://www.g28c87jwqd0e6tn7577l28030vmgp5ohs.org/]uydjyedih[/url]

    Reply

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Malam Nasir El-Rufa’i: Guga Sha Kwaramniya

Wa Ke Tsoron Malam Elrufa’i Ya Zama Minista?

August 9, 2023
ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (5)

ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (5)

May 24, 2025
Janar Buratai: Sarki Mai Littafi

Janar Buratai: Sarki Mai Littafi

July 6, 2023
EFCC Ta Kai Farmaki Jihar Katsina

EFCC Ta Kai Farmaki Jihar Katsina

June 9, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Afirka Ta Fice Daga Gasar Kofin Duniya Na Bana
  • Book Launch Seeks to Rewrite Lassa’s Story, Preserve Cultural Heritage
  • Zaɓen 2027: Akwai Yiwuwar Farfesa Pantami Ya Yi Nasara – Farfesa Lawanti

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Afirka Ta Fice Daga Gasar Kofin Duniya Na Bana

Afirka Ta Fice Daga Gasar Kofin Duniya Na Bana

July 10, 2026
Book Launch Seeks to Rewrite Lassa’s Story, Preserve Cultural Heritage

Book Launch Seeks to Rewrite Lassa’s Story, Preserve Cultural Heritage

July 9, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.