• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, January 16, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Addini

Malaman Zamani: Wa’azi Ko Gyaran Gangar Auzinawa?

Darasi Daga Abubakar Imam

Fatuhu Mustapha by Fatuhu Mustapha
September 15, 2023
in Addini
0
Malaman Zamani: Wa’azi Ko Gyaran Gangar Auzinawa?

Babban Masallacin Abuja

47
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Malaman Zamani: Wa’azi Ko Gyaran Gangar Auzinawa?
Darasi Daga Abubakar Imam

Daga Fatuhu Mustapha

Related posts

Baffa Hotoro Ka Ci Amanar Ilimi

Baffa Hotoro Ka Ci Amanar Ilimi

November 29, 2025
Jama’a Mu Fahimta: Musulunci Daban Ƙungiyanci Daban

Jama’a Mu Fahimta: Musulunci Daban Ƙungiyanci Daban

November 28, 2025

~~~~~~~
Wata shekara wani wakilin jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo a Kano, ya aike da wani rahoto da ke cewa “An Kama Wani Ɗan Yankan Aljihu A Kasuwar Kurmi.” Ya sa ran Editan jaridar, Malam Abubakar Imam zai maraba da rahoton, ya gaggauta sanyawa a buga shi, amma abin mamaki sai ya ga jaridar ta fito ba a buga ba.

Wannan abu ya ba shi mamaki, har ya fara zaton ko rahoton bai kai ga edita ba ne, musamman ma da yake yankan aljihu wani baƙon abu ne da ba a san da shi ba a ƙasar Hausa.

Ran nan dai sai ya wanke ƙafarsa ya tafi Zariya ya iske Malam Abubakar Imam a ofis, yake tambayar sa ko bai ga rahotonsa da ya aiko ba ne. Edita ya kalle shi, ya ce “dama kai ne ka aiko da rahoton yankan aljihu?” Nan da nan ya jawo wata dirowar da ke teburinsa, ya ɗauko rahoton ya miƙa masa, ya ce “in dai wannan ne ba za mu buga ba. Domin kuwa, in har muka buga to satar da za a yi nan gaba sai ta fi waccan da ka aiko mana.”

Ya ci gaba da cewa, “a yanzu haka ba za ka rasa wasu ɓatagari da suke neman sabuwat hanyar da za su yi sata ba. In suka samu wannan labarin to sun samu dama ke nan, duk Kano za su tafi domin su koyo yadda ake yankan aljihu. Daga nan sai abin ya yaɗu, maimakon mu yi gyara, sai mu yi gyaran gangar Auzinawa.”

Azarɓaɓi da son bayar da labari, su ne manyan abubuwan da a yau ke zubar wa malamai ƙima da mutunci a idon duniya. Salon wa’azin malaman yau ya sha bamban da na malamanmu na dauri da muka sani a Ƙasar Hausa. Mun shafe shekaru muna jin wa’azin su Malam Nasiru Kabara, Sheikh Abubakar Gumi, Sheikh Isa Waziri, Sheikh Tijjani Bala, Ustaz Yusuf Ali, Malam Na’ibi Suleiman Wali da sauransu, amma ba za ka taɓa jin suna yaɗa jita-jita ko suna munana zato ga al’umma ko wani yanki na al’umma ba. In za su yi wa’azi a kan zina, ba sa keɓe wani gungu na mutane su zarge su da abin da ba su da wani tabbas a kai. Wanann ya sanya har suka mutu ba za ka taɓa samun wani yana musu hawan ƙawara da cin fuska ba. Ko a yau, ka saurari malamai irin Sheikh Sambo Rigachukum, Sheikh Sherrif Ibrahim Saleh da irin su Farfesa Ibrahim Maƙari, ba za ka ji wata kalma yasasshiya ko ta batsa a wa’azinsu ba.

A yau wasu gungun matasa da suke zaton karatu shi ne ilmi, sun duƙufa wurin yin wa’azi da ya saɓa da yadda muka san wa’azi a Kasar Hausa. An mayar da mumbari ya zama wani fage ne na yin batsa, yaɗa fasadi, sharri da cin fuskar juna. Malamai sun koma ba su da maraba da ‘yan siyasa. An daina koyar da addini, an koma koyar da aƙida kawai. Mabiya, maimakon su ƙara fahimtar addini, sai ƙara dulmiya suke cikin ruɗu da jahilci.

Ɗauki misali da batun da yake ta yawo a yanzu, na cewa mata masu sana’a ta intanet, da yawansu mazinata ne. A ɗauka haka ne, shin fadar da Malam ya yi, za ta magance abin ko kuma za ta amfanar da al’umma? Shin Malam yana da tabbacin hakan? Shin shi wannan malami ba ya ganin kamar ya ankarar da wasu da ba su sani ba, yanzu sun sani, kuma za su yi amfani da damar su ma su shiga a dama da su? Malam ba ya ganin da wannan ba gara ya yi wa’azi a kan su ji tsoron Allah ba, ya yi wa’azi a kan illat zinace-zinace? Na yi imanin a yau, wasu da ba su san da wannan hanyar ba, to an tallata masu, da yawa za su gwada ko za su yi sa’a.

Haka yake a kan batun da wasu ke cewa ana zina a gidajen silima. Da yawa da suke neman inda za su je su yi zinar, sun samu bayani a ɓagas. Idan ma da ba a yi, to yanzu an samu wuri mai duhu sai a je a raƙashe.

Ƙila da Manzon Allah ya ce “ku kyautata wa mumini zato” da irin waɗannan malaman yake. Domin mummunan zaton da suke wa al’umma shi yake kai su ga yin hakan.

Lokaci dai ya yi da ya kamata malamai su tashi tsaye su yi wa kansu karatun ta natsu. In kuma sun ƙi, to kar su kuka da kowa, su yi kuka da kansu.

Allah Ya sa mu gane!

~~~~~~~

Malam Fatuhu Mustapha, mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, yana zaune ne a Kano

~~~~~~~

 

Previous Post

Sabon Gari, Kano – Prof. Adamu Baikie’s Insider Perspective

Next Post

Batun Tsaro A Malam Madori: Jan Hankali Ga Hukumomi Da Al’umma

Related Posts

Baffa Hotoro Ka Ci Amanar Ilimi
Addini

Baffa Hotoro Ka Ci Amanar Ilimi

November 29, 2025
Jama’a Mu Fahimta: Musulunci Daban Ƙungiyanci Daban
Adabi

Jama’a Mu Fahimta: Musulunci Daban Ƙungiyanci Daban

November 28, 2025
Muhammadu (Saw): Haske Mai Haskakawa
Addini

Muhammadu (Saw): Haske Mai Haskakawa

November 21, 2025
Next Post
₦16,000 Za Mu Sayar Da Taki A Jigawa – Gwamna Namadi

Batun Tsaro A Malam Madori: Jan Hankali Ga Hukumomi Da Al'umma

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

KAMUN LUDAYIN JEMAGE

KAMUN LUDAYIN JEMAGE

July 23, 2023
Barkwancin Ƙarshen Mako

Barkwancin Ƙarshen Mako

July 30, 2023
BAYAN KAMMALA TARON HAƊIN KAN ƘASA A NIJAR, KO ƘUDURORIN TARON ZA SU YI TASIRI?

BAYAN KAMMALA TARON HAƊIN KAN ƘASA A NIJAR, KO ƘUDURORIN TARON ZA SU YI TASIRI?

February 20, 2025
EXTINCTION

EXTINCTION

January 1, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation
  • Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco
  • Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

January 15, 2026
Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

January 14, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.