ALLAH TSIN€
WA MAƘIYA MANZO
(SAW)

__________
Ya Allahu ta roƙo nake,
Gwiwa biyu durƙushe nake,
Fuskata a turɓune take,
Zuciyata tafarfasa take,
Allah tozarta maƙiyan Manzo
Ya Ƙawiyyu muradi muke,
Cikin sauri gaƙuwa muke,
Rayukanmu duk ɓaci suke,
Hankalinmu sai tashi yake,
Allah darkake masu tozarta Manzo.
Yau wulaƙantattu ihu suke,
Sunan Manzonka kamawa suke,
Iyayensa tozartawa suke,
Har masoyansa cutarwa suke,
Allah ka daɗo tsira ga Manzo!
•••
(Sallallahu Alaihi Wasallam)
__________
© Bashir Yahuza Malumfashi
(Fasihin Galadiman Katsina-I,
Asabar, 30-03-1448 (Hijriyya)
12-09-2026 (Miladiyya)
__________













