Alhaji Sule Lamido : Jagoran Talakawa Na Haƙiƙa
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

__________
A wannan zamani, idan ana neman ɗan siyasa na haƙiƙa kuma mai aƙidar ‘yan mazan jiya, mai hangen nesa; ɗan siyasa kaifi ɗaya, wanda za a kira da Jagoran Talakawa, to da an zo wajen Alhaji Sule Lamido, sai a shafa Fatiha kawai a tashi.
A tarihinsa, tun da ya fara harkokin jama’a yana matashi, har ya kai ga shiga siyasa, layi ɗaya ya tsaya – ra’ayin hidimar talakawa da tallabar marasa galihu. Shi ya sa ma tun a Jamhuriya ta Ɗaya ya kasance a Jam’iyyar NEPU, ta marigayi Malam Aminu Kano.
A Jamhuriya ta Biyu ma, bai gushe daga aƙidarsa ba, domin ya kasance tare da Jam’iyyar PRP, ta Malam Aminu Kano. Haka kuma tun da Sojoji suka ba da ragamar Dimokuraɗiyya a 1999 zuwa yau, Malam Sule, tsaye yake ƙiƙam, a jam’iyya ɗaya – PDP. A cikinta ya yi Gwamnan Jihar Jigawa har karo biyu, na tsawon shekara takwas. Bai taɓa canja sheƙa ba ko sau ɗaya.
A kwanakin baya, na samu ganawa da Jagoran Talakawa, Alhaji Sule Lamido, a gidansa na Abuja. Na ga karimci da mutunci daga wannan bawan Allah. Wani babban abin jin daɗi, shi ne da ya ba ni kyautar littafin tarihinsa (mai babban bango) mai taken, “Being True to Myself” bayan ya rattaba sa-hannunsa (Autograph). Ni ma na ba shi kwafin nawa littafina mai taken “GALADIMA: Kundin Waƙoƙi.”
Ina matuƙar godiya, Jagoran Talakawa na Haƙiƙa – Malam Sule Lamido. Allah ƙara maka lafiya da imani. Ina godiya ga Malam Mansur Ahmed bisa waɗannan hotuna da ka ɗauke mu.
__________













