NASIHARMU TA YAU 30

__________
JINJINA GA MAI MARTABA SARKIN KATSINA
Shugabannin al’umma, musamman sarakunan gargajiya da malaman addini, su ne majiɓantan talakawa, su ne garkuwa kuma su ne jagorori da fitilun da suke jagora da saita wa talakawa hanya. Su ne ya kamata su tsaya tsayin daka wajen yi wa masu mulki nasiha da jan hankali, domin su kyautata wa talakawa.
A kan haka, ya zama wajibi mu yi jinjina da addu’ar alheri ga Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Dakta Abdulmumini Kabir Usman, CFR, wanda a kullum yake kare talaka, wanda ba ya tsoro ko shayin fayyace gaskiya ga masu mulki.
Muna kira ga sauran iyayen ƙasa, sarakunanmu da malaman addini, da su yi koyi da Mai Martaba Sarkin Katsina, su kare mutuncinsu, su cire kwaɗayin abin duniya, su yi abin da ya dace, kamar dai yadda shi yake yi.
Muna roƙon Allah ya ƙara wa Mai Martaba Sarkin Katsina lafiya da imani. Allah ya kare shi da sauran shugabanninmu da malamanmu masu son gaskiya daga dukkan sharri. Amin-Summa-Amin.
__________











