• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, January 16, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

Nazari Da Sharhin Littafin “Sai An Yi Da Gaske”

SHARHIN LITTAFI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
May 21, 2025
in Adabi
0
Nazari Da Sharhin Littafin “Sai An Yi Da Gaske”

Litttafin "Sai An Yi Da Gaske" da marubucinsa, Malam Suleiman Ɗanyaro a

41
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Nazari Da Sharhin Littafin “Sai An Yi Da Gaske”

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

December 23, 2025
Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine

Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine

December 6, 2025
Wuraren da za a samu littafin

 

                         __________
Sunan Littafi: Sai An Yi Da Gaske.
Sunan Marubuci: Suleiman Ɗanyaro.
Kamfanin Wallafa: Haiba Publishers Nigeria Limited Kaduna.
Tsarin Littafi: Wasan Kwaikwayo.
Yawan Shafuka: 69.
Shekarar Wallafa: 2023.
Farashin Littafi: Naira 700.
Mai Sharhi: Bashir Yahuza Malumfashi.
                        __________

Gabatarwa:
Ga waɗanda suka ga jiya kuma suke rayuwa a yau, za su iya zama alƙalai kuma su zama shaidu na haƙiƙa, yadda zamani ya kawo sauye-sauye a rayuwar al’umma. Musamman ma ta ɓangaren canjin yanayi, ɗabi’u da halayyar mutane.

A lokacin da amana, gaskiya, kunya da zumunci da taimakon juna suka zama ruwan dare a zamanin da, a wannan zamanin babu abin da ke wakana, illa rashin gaskiya, cin amana, fitsaranci, fasiƙanci, ta’addanci, rashin daraja manya, rashin kunya, shaye-shayen kayan maye, fashi da makami da sauransu. A taƙaice dai al’ummar yanzu tana cikin hargitsi da tashin hankali. Ya zama dole a tashi tsaye domin kawo gyara da saita wannan al’umma.

Ɗaya daga cikin hanyoyin da ake bi domin saita kowace irin gurɓatacciyar al’umma, ita ce ta hanyar neman ilimi da ilimantarwa, karatu da karantarwa, nasiha da wa’azantarwa da faɗakarwa. Babban tubalin dukkan waɗannan hanyoyi na gyara, shi ne rubutun littafi.

Yana daga cikin babban dalilin da ya sanya Malam Suleiman Ɗanyaro ya ɓata hankalin dare, ya samar da wannan littafi na wasan kwaikwayo na “Sai An Yi Da Gaske.”

A cewar Dokta Ibrahim Shehu Liman, babban malami a Jami’ar Jihar Kaduna, a yayin da yake ta’aliƙi ga littafin: “Suleiman Ɗanyaro bai yi ƙasa a gwiwa ba. Ya yi amfani da basira da hangen nesa wajen bayyana matsalolin da ke addabar al’ummar da yake ciki, musamman shaye-shaye da sata da karɓar rashawa da cin hanci da kuma fasiƙanci. Bayan haka sai ya yi dabarar kawo mafita, ta hanyar haɗa ƙarfi tsakanin al’umma da shugabanni da kuma jami’an tsaro.” (Shafi na iv).

Ƙunshiyar Littafin:
Marubucin littafin nan ya ɗauki matakai sahihai na samar da littafin wasan kwaikwayo na haƙiƙa, domin faɗakarwa cikin sauƙi. Ya fara da godiya a shafi na iii. Akwai shafin ta’aliƙi, inda ƙwararren malamin Hausa ya yi tsokaci game da littafin, a shafi na iv. Akwai shafin gabatarwa, wato shafi na v. Sannan kuma ya gabatar da sunayen ‘yan wasan da suka taka rawa a littafin, a shafi na vi.

Domin warware babba da ƙananan jigogi da ma katafanin ƙunshiyar littafin, marubucin ya karkasa shi zuwa kashi uku. Kashi na ɗaya yana ƙunshe da fitowa huɗu – daga shafi na 1 zuwa na 27. Kashi na biyu yana ƙunshe da fitowa uku – daga shafi na 23 zuwa na 49. A yayin da kuma kashi na uku na littafin ke ƙunshe da fitowa uku – daga shafi na 50 zuwa na 69.

‘Yan Wasa Da Dacewarsu:
Ɗaya daga cikin ginshiƙan kowane wasan kwaikwayon da ke son samun nasarar isar da gamsasshen saƙo, shi ne samar da ‘yan wasan da suka dace da jigon maudu’in da aka nufa. A wannan littafi, za a iya cewa marubucin ya samu nasara, musamman yadda ya samar da ‘yan wasan da suka warware manya da ƙananan jigogin wasan.

Duba da cewa mas’alar da aka assasa littafin nan ta shafi al’umma ne gaba ɗaya, don haka sai marubucin ya samar da ‘yan wasan da suka wakilci kowane rukunin al’umma. Misali, Alhaji Nura (babban attajiri), Hajiya Zara (matar babban attajiri), Hakimi, Dagaci (sarakunan gargajiya). Akwai alƙali, akwai Difi’o, akwai limamin gari, akwai ma’aikacin gwamnati, akwai matasa, akwai ‘yan shaye-shaye, akwai ɓarayi, akwai magidanta da sauran rukunnan al’umma.

Muhimman Darussa:
Babban jigon wannan wasan kwaikwayo shi ne yaƙi da munanan ɗabi’u da suka zame wa al’umma alaƙaƙai. Haka kuma an samar da wasu darussan da suka haɗa da muhimmancin gaskiya da riƙon amana, kamar yadda suke samar da zumunci da lumana tsakanin al’umma, waɗanda kuma ke haifar da farin ciki da tsari a cikin al’umma. A hannu ɗaya kuma akwai illar rashin kunya da rashin tarbiyya da illar son zuciya, waɗanda ke haifar da munanan ɗabi’u da ke karya al’umma, su samar da rashin zaman lafiya da rashin tsaro.

Daga rayuwar gurɓatattun mutane kamar Alƙali Mantsala, wanda ke cin hanci da rashawa da yin zina da matan aure da ɗaure wa ƙarya gindi, an ga sakamakon da yake haifarwa na karya doka da oda. Daga halayen Dagaci Mantau na haɗa baki da mugun Alƙali da mugun Difi’o da ashararin attajiri, an ga yadda suka haifar da rushewar duk wata kyakkyawar tarbiyya a cikin al’umma.

Haka kuma daga halayen magidanta marasa tarbiyya irin Maƙi-Kira, an ga illar sangarta yara, wanda ke haifar da matasa marasa tarbiyya, waɗanda ke zaman banza, daga ƙarshe su shiga shaye-shaye da sace-sacen kayan mutane.

Akwai darussan da ke nuna illolin zaman banza ga matasa da illolin shaye-shaye da illolin sace-sace da ma sakamakon da ke biyo bayan duk mai yin haka. An doka misali da matasa kamar Gagare da Goje da Ƙaura da lalatattar budurwa ‘Yartsamage da kuma ƙasurgumin ɗan fashi, mai suna Babban Ƙwaro.

A wannan wasa, an kuma nuna muhimmancin gaskiya da mai gaskiya da abin da ke biyo bayan duk wanda ya tsare gaskiya da amana a rayuwarsa. An samar da kyakkyawan misali da rayuwar Alhaji Nura da matarsa Hajiya Zara da Liman da Hakimi da Injiniya da Malam Abdu da Difi’o Arangama (mai gaskiya), waɗanda saboda gaskiyarsu da kishin al’umma, suka yi nasarar fatattakar miyagun mutane daga cikin al’ummarsu.

Wani babban darasi kuma shi ne na muhimmancin haɗin kai bisa manufa ɗaya, domin samar da gyara. An nuna yadda al’umma suka haɗu suka bi doka wajen yaƙi da gurɓatattu. A nan ne ma sunan littafin nan ya fito na “Sai An Yi Da Gaske.” Watau dai kisan baƙi sai gayya. Hakan na nuna cewa sai al’umma sun haɗa kai bisa manufa ɗaya ta kirki, sannan za su iya yaƙi da ɓarna, sannan za su samar wa kansu lafiya da zaman lafiya.

Azanci Da Kwalliyar Harshe:
Marubucin littafin nan ya yi matuƙar ƙoƙari wajen samar da kalmomi da karin magana iri-iri da suka ƙayatar da ƙunshiyar littafin. Hakan ya taimaka sosai wajen bunƙasa harshen Hausa, musamman saboda an taskace su domin nazarin al’ummar yau da ta nan gaba mai zuwa.

Wasu daga cikin karin maganar da suka bayyana a littafin nan sun haɗa da: 1-Albarkacin karen gidanka kakan ga karen gidan wani (shafi na 13). 2-Kashinmu ya bushe (shafi na 26). 3-Difi’on gizago ne, ko kaɗan ba ya da sabo (shafi na 27). 4-Don mu ƙara ɗaure akuyarmu a gindin magarya (shafi na 37). 5-Rayuwa irin ta tsohon biri (shafi na 40). 6-Hankaka da mai aya sun kusa haɗewa. 7-In yar da ƙwallon mangwaro, in huta da ƙuda (shafi na 53). 8-Hannu ɗaya ga alewa, ɗaya hannun kuma ga bulala (shafi na 63).

Kammalawa:
Tabbas, an yi matukar ƙoƙarin tsabtace rubutun littafin nan, ta yadda aka kauce wa kurakurai.

Wannan littafi na wasan kwaikwayo ya ƙayatar matuƙa kuma ya samar da babbar kafar kawo gyara cikin al’umma, musamman ta fuskar nusar da matasa illolin shaye-shaye da zaman banza da aikata miyagun laifuka. Haka kuma ya samar da hikimomi da hanyoyin da al’umma suka kamata su bi domin magance miyagun halaye da ke addabar al’umma.

Wannan littafi babban kundi ne da ya kamata kowane matashi da matashiya su mallake shi. Ya kamata a saka shi a manhajar makarantun sakandare da na gaba da sakandare, domin nazari ga ɗalibai. Haka kuma ya dace hukumomin da ke yaƙi da miyagun ƙwayoyi da hukumomin yaƙi da rashin ɗa’a su tanadi littafin nan domin inganta ayyukansu ga al’umma. Haka kuma zai yi matuƙar tasiri, idan aka wassafa shi zuwa fim da za a iya kallo domin isar da saƙonninsa kai tsaye ga al’umma.
•••••••
Ga duk masu buƙatar sayen littafin, kwafi ɗaiɗai da ‘yan sari, za a iya samun shi a wurare kamar haka:

√ Alhaji Yusuf Mustapha Book Shop, Block 182, No 2, Tudun Wada gate, Sheikh Abubakar Gumi Market Kaduna. Phone No: 08062615865

√ Muhammad Sani Book Shop, Belcom Plaza opposite Dan Musa Plaza, Kasuwar Bacci Motor Park Kaduna. Phone No: 08033268404

√Alhaji Abdullahi Book Shop, Kawo Road opposite Yahaya Hamza House, Kawo Market Kaduna. Phone No 08037494613
_______________
Bashir Malumfashi, shi ne Editan Mujallar Taskar Gizago (online)

Previous Post

SAƘON ADDU’A DA TAYA MURNA GA SHUGABAN JAMI’AR FUDMA: FARFESA AMINU ADO KAFUR

Next Post

ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (5)

Related Posts

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)
Adabi

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

December 23, 2025
Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine
Adabi

Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine

December 6, 2025
Yau Take Juma’a: Allah Ka Albarkace Mu
Adabi

Yau Take Juma’a: Allah Ka Albarkace Mu

December 5, 2025
Next Post
ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (5)

ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (5)

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Rage Raɗaɗin Talauci: Attajirai Ku Yi Koyi Da Sabi’u Mahuta

Rage Raɗaɗin Talauci: Attajirai Ku Yi Koyi Da Sabi’u Mahuta

August 7, 2023
BIU: A Visit to a City on a Plateau (3)

BIU: A Visit to a City on a Plateau (3)

December 23, 2023
Aure Sunnar Ma’aiki: Taya Murna Ga Uba Nagari Shehu Musa Sarkin Ƙofa

Aure Sunnar Ma’aiki: Taya Murna Ga Uba Nagari Shehu Musa Sarkin Ƙofa

October 26, 2025
Daura Birnin Bayajidda: Janar Buratai Da Ayarinsa Sun Ziyarci Buhari Da Sarki

Daura Birnin Bayajidda: Janar Buratai Da Ayarinsa Sun Ziyarci Buhari Da Sarki

June 4, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation
  • Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco
  • Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

January 15, 2026
Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

January 14, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.