Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

__________
Ana sa ran Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Manyan Hafsoshin Sojojin Najeriya za su halarci bikin ƙaddamar da wani sabon littafi da ya yi nazari kan shugabanci, sauye-sauye da kuma sauya fasalin Rundunar Sojin Najeriya a ƙarƙashin tsohon Shugaban Rundunar Sojoji, Laftanar Janar Tukur Yusufu Buratai (mai ritaya).
Littafin mai taken “Military Transformational Leadership in Action: The Buratai Era,” wanda Dakta M. S. Abubakar ya rubuta, za a gabatar da shi ga jama’a a ranar Laraba, 16 ga Satumba, 2026, a Zauren Taro na Rundunar Sojojin Najeriya da ke Asokoro, Abuja.
A cewar wata sanarwa da Shugaban Kwamitin Shirye-shiryen taron, Dakta Ahmad Manzo, da Babban Daraktan Kamfanin Clarivox Creative Limited, Mista Segun Adeyemi, suka fitar a jiya Laraba, za a fara taron da ƙarfe 9:45 na safe.
An sanya Shugaban Ƙasa Tinubu a matsayin Babban Bako na Musamman, yayin da ake sa ran tsohon Ministan Tsaro, Alhaji Umaru Abdul Mutallab, zai jagoranci taron.
Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ne zai gabatar da littafin, yayin da Shugaban Kamfanin Max Air, Alhaji Dahiru Barau Mangal, zai kasance ɗaya daga cikin manyan masu ƙaddamar da littafin. Ana kuma sa ran Manjo Janar I. D. Penap (mai ritaya) zai yi bitar littafin.
Masu shirya taron sun ce ana sa ran dukkan Hafsoshin Rundunonin Sojoji, ciki har da Shugaban Rundunar Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, za su halarci taron a matsayin manyan baƙi na musamman.
Littafin ya yi nazari kan shekarun da Buratai ya yi a matsayin Shugaban Rundunar Sojoji, inda aka fi mayar da hankali kan matakan shugabanci, sauye-sauyen hukumomi da kuma ƙalubalen tsaro da Rundunar Sojojin Najeriya ta fuskanta a wannan lokaci, musamman yaƙin da aka yi da masu tayar da ƙayar baya da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.
A cewar Abubakar, littafin bai tsaya kawai wajen rubuta tarihin wa’adin wani kwamandan soja guda ɗaya ba, sai dai ya yi nazari kan alaƙar da ke tsakanin shugabanci, sauya fasalin hukumomi da kuma tsaron ƙasa.
Ya ce, “Babban manufar wannan littafi ita ce yin nazari kan shugabanci a aikace, wato yadda aka tsara matakai, aka aiwatar da sauye-sauye da kuma yadda hukumomi suka mayar da martani bisa haƙiƙanin ƙalubalen da Rundunar Sojojin Najeriya ta fuskanta a wani lokaci mai matuƙar wahala a tarihin tsaron ƙasar.”
Ya ce wasu daga cikin manyan tsokacin da littafin ya kawo, sun haɗa da yadda rundunonin sojoji suke tinkarar barazanar tsaro da ke sauyawa da kuma rawar da shugabanci ke takawa wajen daidaita hukumomi da sababbin yanayi.
Ana sa ran bikin gabatar da littafin zai samu halartar manyan jami’an gwamnati, hafsoshin soja masu aiki da waɗanda suka yi ritaya, sarakunan gargajiya, jami’an diflomasiyya, malamai da masu bincike da sauran masu ruwa da tsaki.
Daga cikin sarakunan gargajiya da ake sa ran za su halarta, akwai Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, da Olowu na Kuta, Oba Hameed Oyelude Makama Tegbosun III.
Shirin taron zai kuma ƙunshi tattaunawar ƙwararru wadda Amina-Akano Bello da Manjo Janar Victor Ezegwu (mai ritaya) da Rear Admiral Adamu Biu (mai ritaya) da Farfesa Phillip Dahida za su gabatar. Haka kuma marubucin littafin, Abubakar, zai kasance a cikin masu tattaunawar.
Abubakar ya ce an rubuta littafin ne domin adana ƙwarewa da abubuwan da hukumomi suka gabatar a baya, tare da ƙarfafa yin tunani mai zurfi kan tsarin tsaron Najeriya.
Ya ce, “Hukumomin tsaro suna ci gaba da samun sauye-sauye ne ta hanyar yin nazari kan abubuwan da suka fuskanta, tsarin da ya yi aiki da wanda bai yi ba da tsarin ya sauya da kuma darussan da ya kamata a ci gaba da riƙewa.”
Adeyemi, wanda ya haɗa gwiwa tare da Dakta Manzo wajen bayar da sanarwar, ya ce rubuta muhimman lokuta a tarihin hukumomin Najeriya, na iya samar da tushe mai kyau wajen koyo da kuma gudanar da muhawara mai ma’ana.
Ya ce littafin zai ba ƙwararrun sojoji, masu bincike, masu tsara manufofi da sauran jama’a damar yin nazari kan wani muhimmin lokaci a tarihin tsaron ƙasar, tare da duba darussan da za a iya amfani da su wajen tsara makomar ƙasar.
__________













