Fatima Gana: Marubuciya Mai Alƙalami Biyu
__________
Sunanta Fatima Abba Gana. Marubuciya ce da take rubutu cikin harsuna biyu – Ingilishi da Hausa. Ta rubuta littattafan hikaya da dama, wasu an wallafa, wasu kuma suna kan hanya. Wakilinmu ya tattauna da ita, inda ta bayyana tarihinta, yadda take rubutu, burinta a rayuwa da kuma sauran al’amuran yau da kullum. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
__________

A taƙaice, wace ce Fatima Abba Gana?
Ni haifaffafar garin Kaduna ce kuma na girma ne a garuruwan Arewa daban-daban amma Ni ‘yar asalin Jihar Barno ce. Ta ɓangaren yare kuwa, ni Kanuri ce ta asli. Na yi karatun digirina na farko a Jami’ar Ahmadu Bello Zaria. Na yi bautar ƙasa lta a garin Osogbo, Jihar Osun, a ofishin Gwamnan jihar.
Na fara aiki a kamfanin sayar da motoci na Paki International Motors Kaduna, a matsayin Akawu na ɗan wani lokaci, kafin daga bisani na koma aikin banki a Bank PHB. Daga nan na koma Union Bank, inda har ma kai matsayin Manaja. Haka kuma na yi aiki Jaiz Bank. Na bar aikin banki, shekaru goma sha biyar da suka gabata, inda na buɗe kamfanin kasuwanci na ƙashin kaina.
Na halarci kwasa-kwasai da yawa a fannin aikin banki da da akawu, inda har na rubuta Babbar Jarabawar Harkokin Akawu (ACCA) a Ingila. Na karatu a Goethe Institute Lagos, inda na fito da takardar shaidar Difloma a yaren Jamusanci. Haka kuma na yi kwas a harkar fim a makarantar ITPAN (Independent Television Producers Association of Nigeria), inda na fito da Kwalin Shaidar rubuta labarin fim, shiryawa da ba da umurni. (Scriptwriting, Producing and Directing).
A yanzu wane aiki kike yi, tun da kin bar aikin banki?
Yanzu haka Ni ce Babbar Darakta kuma Shugabar kamfanina na SHAWULLAM NIG. LTD. wanda yake ayyukan kwangila da kuma aikin tuntuɓa dangane da harkokin kuɗi. A ƙarƙashin kamfanin, akwai ɓangaren da ke kula da harkokin adabi da al’adu da rubuce-rubuce da kuma reshen bayar da tallafi. A matsayina na marubuciya, ina son yawan tafiye-tafiye da nazari a fannin rubutu da aikin taimaka wa al’umma. Ni mamba ce a ƙungiyoyin marubuta da dama, kamar Soceity of Young Nigerian Authors (SYNW), International Women Writers Guild (IWWG USA), Association of Nigerian Authors, Abuja National Chapter (ANAN), Alƙalam Authors Kaduna, inda a yanzu haka ni ce Mataimakiyar Shugaban Kungiyar. Haka kuma ina cikin ƙungiyar Literary Association of Authors Lagos, da International Writers Association (IWA).
Tun yaushe kika fara harkar rubuce-rubuce?
Na daɗe ina harkar rubuce-rubucen ƙirƙirarrun labarai, tun ina firamare. Kuma babban burina, shi ne in ga sunana a bangon littafin da na rubuta, wanda zai amfani al’umma da darasi, wanda ko bayan bana raye zai ci gaba da amfanarwa.
Ya zuwa yanzu, waɗanne littattafai kika rubuta kuma aka wallafa?
Nakan yi rubutu ne a harsunan Hausa Turanci. Ni ‘yar gwagwarmayar bunƙasa adabi ce, manazarciya kuma mai yin aikin fassara. Nakan yi rubutu da isar da saƙo ta hanyar bayar da labarun da suke shafar ƙalubalen da mata suke fuskanta.
Wasu daga cikin littattafaina sun haɗa da:
1-Rakiba (Hausa)
2-Rakiba (Turanci)
3-Karima (Hausa)
4-Bunayya: The Zaria Impact Book 1
5-Bunayya: The Fire Beneath Book 2
6-Bunayya: The Broken Kola Book 3
7-Bunayya: The Lost Soul, The Last Rite Book 4
8-The Deceptive Heart
9-Whispers in the Heart
10-Kukan Ruhi
11-Tsarki A Cikin Guba
12- Garin Da Ba’a Barci (Gajeren Labari)
13-Labarin Sakaci (Gajeren Labari)
14-For the Sake of Love (A Dalilin So – Fassarar Littafin Badamasi Shuaibu Burji)
15-When Love Reaches Its Peak (In So Ya Yi So – Fassarar Littafin Badamasi Shu’aibu Burji)
16-Love Has No Boundary (Fassarar Littafin Hafsat S. Mohammed)
A matsayinki na marubuciya, wane alheri kika taɓa samu, wanda ba za ki mance da shi ba?
Gaskiya a matsayina na marubuciya, na samu alherai da yawa a wannan haka, waɗanda ba za su iya misaltuwa ba, sai dai godia ga Ubangiji Allah – ba sai na faɗa ba.
Ko kin taɓa ganuwa da ɓacin rai, a sanadiyyar wannan harka ta rubutu?
Gaskiya na taɓa samun ɓacin rai a harkar rubutu amma shi ma ɗin haka rayuwa take, wani ya ɓata maka; wani ya faranta maka. Wannan kuma an yi ne domin a durƙusar da ni a harkar amma sai ya ƙara min ƙarfin gwiwa. Na zage damtse, na ba da himma, domin har gidi aka yi min cewa wai ni ban da ƙwaƙwalar da zan yi rubutu har a amfana da shi; al’umma su ji suna alfahari da ni. Sai kuma na biyun da aka yi min, inda aka ce ba zan iya zama wani abu a harkar rubutu har duniya ta gani ba, idan ba wannan mutumin a cikin lamarin rubutuna. Amma sai kuma aka manta da cewa Allah yana nan kuma Allah yana tare da bawansa a kodayaushe. Alhamdu lillahi, duk wannan yanzu ya zo ya wuce kuma ya zama tarihi. A harkar rubutu, duk na wuce wannan siraɗin.

A wannan harka ta rubutu, ko akwai wani marubuci da kike koyi da shi?
Gaskiya a harkar rubutu, a cikin manyan marubuta na duniya, ni na fi koyi da rubutun John Grisham da Robert Ludlum da Sidney Sheldon da Barbara Taylor Bradford da Kathy Reiches da Danielle Steele. Amma kuma cikin marubuta na Afirka, na fi koyi da manyan marubutanmu na Arewacin Najeriya, irin su Bala Anas Babinlata da Balaraba Ramat Yakubu da Ɗan Azumi Baba Cheɗiyar ‘Yan Gurasa da Dakta Bukar Usman da Farfesa Zainab Alkali da Farfesa Razinat Muhammed. Ina koyi da su kuma ina alfahari da su tare da fatan in zama na taka matsayi irin nasu a harkan rubutu da adabi. Yadda duniya ta san su, ni ma ina son in zama haka.
Ko yaya kike ganin ƙalubalen da ya mamaye harkar wallafa, musamman yadda intanet ta kunno kai?
Gaskiya kam, inda aka ce zamani ya zo da sauyi, yadda harkoki suka koma internet, muna ƙoƙarin mu dawo da martabar rubutu ta wannan hanyar, domin ci gaba wayar da kai da faɗakarwa sosai; duk da dai wannan ba ƙaramin aiki ba ne a gabanmu. A gaskiya kuma muna buƙatar gyara a cikinta da taimakon manyanmu masu kishin adabi daga kowace kusurwa ta Arewacin Najeriya.
Cikin littatafanki, wanne ne ya fi burge ki ko kuma kika fi alfahari da shi?
Cikin littafan da na rubuta, wanda ya fi burge ni, shi ne littafina na farko a duniya, Rakiba, wanda na yi da Hausa kuma yake da shafi 447. Daga baya na yi na Turanci. Skuma Bunayya, wanda saiti ne na littattafai hudu.
Ko akwai wasu shawarwari da za ki ba gwamnati da sauran al’umma dangane da harkar rubutu?
Shawara ta ɗaya da zan ba da ga gwamnati da attajirai game da harkar rubutu da marubuta ita ce, su dinga tallafa wa marubuta masu ƙaramin ƙarfi. Su riƙa ɗaukar nauyin wallafa littattafan marubuta, a riƙa zuba su a makarantu. Haka kuma a riƙa saka littattafan a manhajar makarantu manya da ƙanana.
Shawara ta biyu, ya kamata gwamnati da ma al’umma su rungumi marubuta, a ƙarfafa masu gwiwa. A riƙa ɗaukar nauyin rubuce-rubucensu, a mayar da su fim domin faɗakarwa da wayar da kan al’umma.
Ya kamata, musamman gwamnatocin Arewa su taimaka, su yi koyi da takwarorinsu na Kudu, waɗanda sun yi mana nisa sosai a harkar rubutu da wallafa. Lallai ne Gwamnatin Tarayya ta saka hannu a cikin wannan harka, musamman yadda ƙasashen da suka ci gaba suke ba marubuta tallafi.
__________












