• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, September 20, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

BABBAN LABARI

Daga Wakilinmu by Daga Wakilinmu
September 9, 2026
in Babban Labari
0
Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

Marigayi Ibrahim Khalil Ɗan Shagamu

124
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

Daga Wakilinmu

Related posts

Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta

Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta

September 3, 2026
KATSINA_2026: Bikin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya

KATSINA_2026: Bikin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya

August 29, 2026
Marigayi Ibrahim Khalil Ɗan Shagamu


__________
Kafar Sadarwar Intanet, Sahara Reportes ta ruwaito cewa an k@she shahararren mai sharhi kan al’amuran siyasa a kafafen sada zumunta, Ibrahim Khalil Ɗan Shagamu, a gidansa da ke Jihar Kano.

Ɗan Shagamu, wanda aka fi sani da laƙanin “Ɗan Shagamu International,” ya shahara ne ta hanyar sharhi da yake yi a fayafayen bidiyo kuma yake wallafawa a kafafen sada zumunta, ya shahara a da kuma sharhi kan harkokin siyasa, addini da al’amuran al’umma, musamman da suka shafi Jihar Kano da Arewa da ma ƙasa baki ɗaya.

Ƙungiyar Amnesty International Nigeria ta tabbatar da kis@n nasa a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X a yau Laraba, inda ta ce an gano gawarsa cikin jin! a gidansa da ke Kano.

Ƙungiyar ta ce: “Amnesty International ta yi Allah-wadai da kis@n mai sharhin siyasa a kafafen sada zumunta, Ibrahim Khalil Ɗan Shagamu, wanda aka gano g@warsa a yau cikin j!ni a gidansa da ke Kano.”

Ta ƙara da cewa: “An yank@ shi cikin mugun yanayi, bayan waɗanda suka k@she shi sun rinjaye shi.”

Har zuwa yanzu da aka haɗa rahoton nan, ba a samu cikakkun bayanai kan yanayin da ya kai ga kis@n nasa ba.

Rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta sun ce an k@she Ɗan Shagamu cikin mummunan yanayi, inda wasu suka bayyana yadda aka yi masa “yank@n rago,” wato y@nke maƙogwaro.

Amnesty International ta yi kira ga hukumomin Najeriya da su gudanar da cikakken bincike kan kis@n, tare da tabbatar da cewa an gurfanar da duk waɗanda ake zargi da hannu a lamarin a gaban ƙuliya, domin su fuskanci hukunci.

Ƙungiyar ta ce: “Dole ne hukumomin Najeriya su gudanar da bincike kan wannan lamari, tare da tabbatar da cewa an gurfanar da waɗanda ake zargi da alhakin kis@n a gaban shari’a.”

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta kuma bayyana damuwarta kan abin da ta kira, ƙara yawaitar barazana da tsoratarwa masu alaƙa da siyasa yayin da zaɓe ke ƙaratowa.

Amnesty ta ce: “Yayin da zaɓe ke ƙaratowa, muna ci gaba da samun rahotanni masu tayar da hankali kan barazanar kis@ da tsoratarwa da ke da alaƙa da siyasa.”

Labarin rasuwar Ɗan Shagamu ya jefa mabiyansa da mazauna yankin cikin jimami, inda da dama suka shiga kafafen sada zumunta domin bayyana kaɗuwarsu tare da yi masa addu’o’in neman rahama da gafara.

Abin tambaya a nan shi ne, shin wane ne ya k@she Ɗan Shagamu kuma laifin me ya aikata da ya cancanci ɗaukar r@nsa? Hukumomin tsaro ne kadai ke da alhakin binciko amsoshin wadannan tambayoyi.
__________

Previous Post

SANATA BELLO MANDIYA: Mun Yi Babban Rashi – Gwamnan Katsina

Next Post

Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

Related Posts

Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta
Babban Labari

Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta

September 3, 2026
KATSINA_2026: Bikin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya
Babban Labari

KATSINA_2026: Bikin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya

August 29, 2026
Ɗalibin Jami’ar Sojoji Ya Ƙera Robot Mai Kashe Gobara
Babban Labari

Ɗalibin Jami’ar Sojoji Ya Ƙera Robot Mai Kashe Gobara

August 12, 2026
Next Post
Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

RANAR HAUSA TA DUNIYA

RANAR HAUSA TA DUNIYA

August 26, 2023
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
KAMUN LUDAYIN JEMAGE

KAMUN LUDAYIN JEMAGE

August 13, 2023
NAJERIYA: Wannan Ba Lokacin Shagala Ba Ne

NAJERIYA: Wannan Ba Lokacin Shagala Ba Ne

May 31, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso
  • JAGORA: Leader of the Masses
  • MALAM SULE LAMIDO: Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

September 20, 2026
JAGORA: Leader of the Masses

JAGORA: Leader of the Masses

September 17, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.