SANATA BELLO MANDIYA: Mun Yi Babban Rashi – Gwamnan Katsina
Daga Bashir Yahuza Malumfashi
___________
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya nuna matuƙar kaɗuwa da alhini bisa rasuwar tsohon Sanatan da ya wakilci Katsina ta Kudu, Sanata Bello Mandiya, wanda ya rasu a Litinin da ta gabata, 7 ga Satumba, 2026, yana da shekaru 62 a duniya.
Gwamna Radda ya bayyana rasuwar Sanata Mandiya a matsayin babban rashi ga Jihar Katsina, musamman al’ummar Katsina ta Kudu da kuma ɓangaren siyasa.
“Na samu labarin rasuwar Sanata Bello Mandiya cikin matuƙar kaɗuwa da baƙin ciki. Rasuwarsa babban rashi ne ga Jihar Katsina da Najeriya,” in ji Gwamna Radda.
Ya bayyana marigayin a matsayin jajirtaccen ma’aikacin gwamnati wanda ya bayar da gudunmawa wajen ci gaban Jihar Katsina da Najeriya.

“Sanata Mandiya ya sadaukar da wani ɓangare na rayuwarsa wajen yi wa al’umma hidima, inda ya yi wa jama’armu aiki da kishin ƙasa da jajircewa. Gudunmawar da ya bayar za ta ci gaba da kasancewa abin tunawa,” in ji shi.
Gwamna Radda ya tuna cewa Sanata Mandiya ya taɓa riƙe muƙamin Shugaban Ma’aikatan Gwamna (Chief of Staff) a lokacin tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, kafin daga bisani aka zaɓe shi zuwa Majalisar Dattawa, inda ya wakilci Katsina ta Kudu daga shekarar 2019 zuwa 2023.
“Ƙwarewarsa da hidimar da ya gudanar a matakin jiha da tarayya, za su ci gaba da kasancewa wani ɓangare na tarihin rayuwarsa,” in ji Gwamnan.
Gwamna Radda ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayi Sanata Bello Mandiya da tsohon Gwamna Aminu Bello Masari da al’ummar Katsina ta Kudu da abokan aikinsa da abokan siyasa da ‘yan uwa da abokan arziki da kuma takwarorinsa na Majalisar Dattawan Najeriya ta 9.
“Ina roƙon Allah Maɗaukakin Sarki ya gafarta masa kurakuransa, ya saka masa da alherin ayyukan da ya aikata, ya kuma ba shi Aljannatul Firdausi. Allah ya bai wa iyalansa da waɗanda suke ƙaunarsa ƙarfin zuciyar jure wannan babban rashi mai raɗaɗi,” in ji Gwamna Radda.
__________













