Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta
• Ba Ta Taɓa Shiga Birni Ba
• Tana Buƙatar Miji
Daga Wakilinmu
__________
Wata kyakkyawar budurwa da ta taso a wani ƙauye, cikin tsaunuka, ta amshi addinin Musulunci a hannun Sheikh Adam Ashaka da Shekih Haruna Baban Chinese, a yayin da suke yawon da’awa a sassan Arewa maso Gabashin Najeriya.
Budurwar mai suna Ƙauna ta bayyana cewa ba ta taɓa shiga birni ba, duk tsawon rayuwarta a wannan tsaunuka take, ita da iyayenta suna bautar dodanni. Haka kuma ta buƙaci shi Malam Ashaka da ya samo mata mijin aure daga cikin gari.
Kamar yadda Sheikh Ashaka ya bayyana a shafinsa na Facebook, ya ce: “Iyayenta suna bautanmr Dodo, ta karɓi addinin Musulunci. Ta ce in sama mata miji, wanda Zai koya mata addinin Musulunci, ya kula da ita, ya riƙe ta amana.”
Dangane da wannan bukata, Ashaka ya ba da sanarwa, yana cewa: “Duk wanda zai iya auren ta daga jama’a, fisabilillahi, ya yi mani magana. In sha Allahu za mu ba shi ita fisabilillahi amma da sharaɗin za ka yi haƙuri da halaye da ɗabi’unta, kafin ta saba; domin ba ta taɓa rayuwa cikin jama’a ba. Tun da aka haife ta, a jeji, can kan duwatsu ta rayu. Ta haka ne za mu riƙa dawo da su cikin addinin Musulunci, jama’a.”
Ya zuwa haɗa rahoton nan dai, akwai waɗanda suka nuna sha’awarsu ta auren ta, kamar yadda suka bayyana a ƙasan rubutun Sheikh Ashaka.
Akwai Al’amin Samfur, wanda ya ce: “Zan aura in sha Allah.”
Shi ma Masoyin Shafi’u Kazaure, har rantsuwa ya yi, sannan ya ce: “Wallahi, wallahi, inabson ta tsakanina da Allah.”
Shi kuwa Umar B. Maikuɗi, ga abin da ya ce: “Malam Adamu Ashaka, ina son ta kuma zan aure ta, in sha Allahu.”
__________














