Ɗalibin Jami’ar Sojoji Ya Ƙera Robot Mai Kashe Gobara
– Aikin Janar Buratai Ya Yi Tasiri
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

__________
A wani gagarumin abin misali na ƙirƙire-ƙirƙire da ƙwarewar fasahar zamani, wani ɗalibi a fannin Fasahar Sadarwa (Information Technology) a Jami’ar Sojojin Najeriya da ke Biu (NAUB), Muhammad Inuwa Abdullahi, ya ƙera wani saƙago (robot) mai kashe gobara kai-tsaye (Autonomous Firefighting Robot), wanda aka tsara shi domin gano gobara a cikin gine-gine tare da kashe ta ba tare da sa hannun mutum ba.
Muhammad, wanda ya fito daga Pantami a Jihar Gombe, ya ƙera wannan na’ura mai fasaha a matsayin aikin kammala karatunsa, inda ya yi amfani da tsarin “Arduino Uno microcontroller” wajen gina ta.
Na’urar, an gina ta ne tare da ba ta damar ta gano harshen wuta, ta hanyarta tafiya da kanta zuwa inda gobarar take, sannan ta kunna famfon ruwa domin kashe ta, a yayin da take faruwa a cikin gida ko wani wuri da aka rufe, kafin ta bazu ta haddasa babbar asara.
Wannan aiki ya nuna yadda za a iya amfani da “embedded systems, robotics, automation da artificial intelligence” wajen magance ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da ke barazana ga tsaron rayuka da dukiyoyi a cikin al’umma.
Da yake bayani kan abin da ya zaburar da shi wajen ƙirƙirar na’urar, Muhammad ya ce an ƙera robot ɗin ne, domin nuna yadda za a iya amfani da fasaha wajen kare rayuka da dukiyoyi ta hanyar gano gobara da wuri da kuma ɗaukar matakin gaggawa.

“Na gina wannan robot ne domin nuna yadda fasaha za ta iya taimakawa wajen ceto rayuka da dukiyoyi kafin gobara ta bazu. Wannan ita ce gudunmawata wajen magance matsalolin da suke faruwa a zahiri a cikin al’ummarmu,” in ji shi.
A cewar matashin mai ƙirƙire-ƙirƙiren, wannan aiki yana da matuƙar fa’ida kuma ana iya amfani da shi a gidaje, makarantu, ofisoshi, ɗakunan gwaje-gwaje, ɗakunan karatu, ɗakunan ajiya, asibitoci da sauran gine-ginen da aka rufe, inda ɗaukar matakin farko kan gobara cikin gaugawa zai iya rage yawan asarar dukiya, tare da ceton rayuka.
Wannan ƙirƙira ta jawo yabo, kasancewar ta ƙara zama wani misali na yadda al’adun ƙirƙire-ƙirƙire ke ƙara bunƙasa tsakanin matasan Najeriya, duk da ƙalubalen tattalin arziki da na ababen more rayuwa da ake fuskanta a ƙasar.
Nasarar ta kuma nuna amfanin ƙara mayar da hankali kan bincike, fasaha da samar da hanyoyin magance matsaloli a aikace a Jami’ar Sojojin Najeriya da ke Biu, wadda ke ci gaba da bunƙasa a matsayin cibiyar ƙwarewa wajen ilimin da ya shafi tsaro, kimiyya, injiniyanci da ƙirƙire-ƙirƙiren fasaha.
Samar da jami’ar ita kanta, yana daga cikin manyan ayyukan ci gaba da gina al’umma da suka kasance wasu daga cikin ƙoƙarin tsohon Shugaban Sojojin Najeriya, Laftanar-Janar Tukur Yusufu Buratai (mai ritaya), CFR, wanda a ƙarƙashin jagorancinsa Sojojin Najeriya suka taka muhimmiyar rawa wajen samar da wannan cibiya ta ilimi.

An tsara Jami’ar NAUB a matsayin wata muhimmiyar cibiyar ilimi mai zurfi da za ta haɗa tazarar da ke tsakanin ayyukan soji, binciken ilimi, kimiyya, fasaha da ci gaban ƙasa. Janar Buratai ya yi hangen nesa na samar da jami’a mai daraja a duniya, wadda za ta samar da ƙwararrun ma’aikata, ta inganta bincike na zamani, tare da haɓaka ƙirƙire-ƙirƙiren fasaha da za su iya taimakawa wajen magance matsalolin tsaro da na zamantakewa da tattalin arziki da Najeriya ke fuskanta.
A yau, manyan ayyukan ƙirƙire-ƙirƙire irin na robot ɗin kashe gobara kai-tsaye da Muhammad Inuwa Abdullahi ya ƙera, suna nuna cewa jami’ar na ci gaba da cika wannan buri ta hanyar horar da matasa masu ƙwarewar ƙirƙira, waɗanda za su iya samar da hanyoyin magance matsalolin rayuwa na zahiri.
Masana sun yi imanin cewa ayyuka irin na robot ɗin kashe gobara na Muhammad, suna iya zama tubalin samar da ƙarin ingantattun tsarin magance matsalolin gaugawa, ta hanyar haɗa Ƙirƙirarriyar Fasaha (Artificial Intelligence – AI), Tsarabe-Tsaraben Intanet (Internet of Things – (IoT) da kuma fasahar gine-gine masu amfani da tsarin zamani.
Yayin da Najeriya ke ƙoƙarin ƙarfafa ƙirƙire-ƙirƙiren cikin gida da rage dogaro da fasahohin da ake shigo da su daga ƙasashen waje, saƙagon da Muhammad Inuwa Abdullahi ya ƙirƙira, wani babban abin tunatarwa ne da ke ishara da cewa, za a iya samar da fasahohin da suka kai matsayin na duniya a cikin jami’o’in Najeriya, idan aka gano baiwa, aka tallafa mata, sannan aka ƙarfafa masu ita.
Matashin mai ƙirƙirar na’urar, ya bayyana fatan cewa baje kolin wannan aiki nasa zai zaburar da ƙarin ɗaliban Najeriya su rungumi bincike, ƙirƙire-ƙirƙire da hanyoyin magance matsalolin al’umma ta amfani da fasaha, domin sauya rayuwar al’ummomi da kuma bayar da gudunmawa wajen ci gaban ƙasa.
__________













