• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Saturday, April 18, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Sarauta

Betaran Biu Janar Buratai Ya Samu Sarautar ‘Baakoren Akure’

Anas Saminu Ja'en by Anas Saminu Ja'en
October 17, 2023
in Sarauta
0
Betaran Biu Janar Buratai Ya Samu Sarautar ‘Baakoren Akure’

Baakoren Akure, Janar Buratai (mai ritaya)

32
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Betaran Biu Janar Tukur Yusuf Buratai Ya Samu Sarautar ‘Baakoren Akure’

Janar Buratai tare da Oba na Akure da sauransu, jim kaɗan bayan naɗinsa

Daga Anas Saminu Ja’en

Related posts

Galadiman Katsina Ya Karrama Ni Matuƙa – Waziri Shehu Musa

Galadiman Katsina Ya Karrama Ni Matuƙa – Waziri Shehu Musa

October 26, 2025
Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina

Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina

October 22, 2025

~~~~~~~
A ranar Asabar 14 ga watan Oktoba, 2023 ce aka naɗa Janar Tukur Yusufu Buratai, CFR Sarautar ‘Baakoren Akure.

An gudanar da bikin naɗin ne a yayin babban bikin al’ada na shekara-shekara mai taken “Ulefunta Festival” na 2023 da aka saba yi a garin Akure.

Laftanar-Janar Tukur (mai ritaya), shi ne tsohon Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya. Shi ne Betaran Biu kuma Garkuwan Keffi, haka kuma tsohon Jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin.

Mai Martaba Sarkin masarautar Akure, Oba (Dokta) Aladetoyinbo Ogunlade Aladelusi, CFR Odundun II, Deji ne ya yi ba shi wannan muhimmiyar sarauta ta ‘Baakoren Akure’ kuma aka naɗa shi, a yayin ruguntsumin bikin.

Kamar yadda Masarautar Akure ta bayyana, a yayin naɗin nasa, “an ba ka wannan sarauta ta ‘Baakoren Akure’ bisa la’akari da irin ƙoƙarinka da jajircewarka, a lokacin da kake shugabancin sojojin Najeriya da kuma yadda ka riƙe Jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin.”

Ɗaya daga cikin ayarin Janar Buratai da suka halarci bikin naɗin, Ibrahim Dahiru Ɗanfulani, ya ce wani mai wasan al’adun gargajiya a Akure’, mai suna Taye Jonson ya bayyana farin cikinsa da wannan karramawa da aka yi wa Buratai da aka naɗa shi Sarautar ‘Baakoren Akure.

Ya ce haƙiƙa girmamawa ce ga ita kanta Masarautar Akure, da ta samu mutum kamar Buratai a cikinta, a matsayinsa na wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajan bai wa ƙasa gudummawa a lokacin da yake jagorancin rundunar sojojin Najeriya. Ya ƙara da cewa ya cancanta da wannan sarauta, duba da irin ayyukan da ya gabatar wa al’umma.

Kazalika, Ita ma, Alaja Fatimo Abdulraheem, wacce babbar ‘yar kasuwa ce, ta nuna jin daɗi bisa yadda masarautar ta ba shi wannan sarauta. Haka kuma ta buƙaci Sarkin Akure da ya ci gaba da zaɓo mutane nagartattu irin Buratai zuwa cikin masarautarsu saboda irin gudummawar da za su bayar wajan ci gaban masarautar.

A lokacin gudanar da wannan biki na naɗi, Oba Aladelusi ya ƙara ƙarfafa gwiwar Buratai, inda ya shaida masa cewa wannan sarauta ta ‘Baakoren Akure’ wata kyauta ce ta karramawa daga masarautar tasu. “Saboda haka ne muka naɗa ka, domin bayar da misali da kai, a matsayinka na ɗan ƙasa nagari; wanda ya yi wa ƙasarsa hidima. Haka kuma mun san za ka yi ƙoƙari a wannan masarautata, a matsayinka na Baakoren Akure.”

A yayin da yake gabatar da nasa jawabin, Ambasada Buratai ya bayyana farin cikinsa bisa wannan girmamawa da aka yi masa na naɗa shi a Sarautar ‘Baakoren Akure.’ Sannan ya sake bayyana godiyarsa bisa irin karɓar da aka yi masa da godiya da irin karamcin da mutanan gari suka yi masa wajan ba shi wannan matsayi. Ya kuma tabbatar musu cewa ba za su yi nadama ba da suka ba shi wannan sarauta.

Ita dai wannan sarauta ta ‘Baakoren Akure’ a al’adance tana nufin wani mutum mai samar da ci gaba ta fannin noma da samar da abinci da tsaro ga al’ummar Akure.

Bikin naɗin dai ya gudana cikin nasara kuma ya samu halartar manyan mutane da suka ya haɗa da mayan ma’aikatan gwamnati da masu masana’antu da masu riƙe da sarautun gargajiya da tsofaffin jami’an tsaron soji da ‘yan uwa da abokan arziki.
~~~~~~~

Previous Post

FAƊA DA ‘YAN TA’ADDA: Malam Dikko Kada Ka Shiga Daji – Abdullahi Mahuta

Next Post

Za Mu Inganta Rayuwa Da Ayyukan ‘Yan Jarida – Minista Idris

Related Posts

Galadiman Katsina Ya Karrama Ni Matuƙa – Waziri Shehu Musa
Sarauta

Galadiman Katsina Ya Karrama Ni Matuƙa – Waziri Shehu Musa

October 26, 2025
Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina
Sarauta

Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina

October 22, 2025
KWATAM HUBA HALIMA TAHIR: Tattaunawa Da Fitattar ‘Yar Jarida Basarakiya
Sarauta

KWATAM HUBA HALIMA TAHIR: Tattaunawa Da Fitattar ‘Yar Jarida Basarakiya

August 19, 2023
Next Post
Za Mu Inganta Rayuwa Da Ayyukan ‘Yan Jarida – Minista Idris

Za Mu Inganta Rayuwa Da Ayyukan 'Yan Jarida - Minista Idris

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

THE PUNCH EDITORIAL ON BENUE: A FABRICATION IN SEARCH OF A SCAPEGOAT

THE PUNCH EDITORIAL ON BENUE: A FABRICATION IN SEARCH OF A SCAPEGOAT

June 18, 2025
YADDA SHARA TA MAMAYE BIRNIN KATSINA

YADDA SHARA TA MAMAYE BIRNIN KATSINA

September 18, 2023
RAMADAN KARIM: 20-1447

RAMADAN KARIM: 20-1447

March 9, 2026
ABDU SALA MALUMFASHI: MUN YI RASHIN ƊAN UWA/ABOKI

ABDU SALA MALUMFASHI: MUN YI RASHIN ƊAN UWA/ABOKI

June 20, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Ko Me Ya Sa Manyan Mata Ke Auren Yara?
  • Mu Ji Tsoron Allah
  • Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Ko Me Ya Sa Manyan Mata Ke Auren Yara?

Ko Me Ya Sa Manyan Mata Ke Auren Yara?

April 18, 2026
Mu Ji Tsoron Allah

Mu Ji Tsoron Allah

April 17, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.