• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, January 22, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

Littafin TAYA NI MU GYARA A Da’irar Nazari Da Sharhi

SHARHIN LITTAFI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
January 17, 2024
in Adabi
0
Littafin TAYA NI MU GYARA A Da’irar Nazari Da Sharhi

Littafin Taya Ni Mu Gyara da Marubuciya Zuwaira Dauda Kolo

107
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Littafin TAYA NI MU GYARA A Da’irar Nazari Da Sharhi

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut’a

Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut’a

January 17, 2026
SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

December 23, 2025

~~~~~~~
Sunan Littafi: Taya Ni Mu Gyara.
Marubuciya: Zuwaira Dauda Kolo.
Shekarar Wallafa: 2023.
Yawan Shafuka: 72.
~~~~~~~

Gabatarwa:

A lokacin da na kammala karatu da nazarin wannan mashahurin littafi, Taya Ni Mu Gyara, wanda ƙarami ne a yawan shafuka amma babba ne ta fuskar muhimmanci da ma’ana, na samu kaina cikin shauƙi da son rubuta tsokaci tare da sharhi, musamman domin sake fito da muhimmancin wasu daga cikin saƙonnin da ya ƙunsa.

Littafin Taya Ni Mu Gyara da Marubuciya Zuwaira Dauda Kolo

A rayuwar Musulmi, babu abin da ya kai ilimi muhimmanci, musamman domin shi ne jigo kuma jagorar kowace ibada, ballantana ma abin da ya ta’allaƙa da hanyar samar da al’umma – aure.

Abu ne sananne cewa ayar Alƙur’ani ta farko da Allah Ya saukar ita ce “Iƙra’a.” Ma’ana “yi karatu.” Hakan ke nuna cewa lallai neman ilimi shi ne ƙashin bayan kowane al’amari. Haka kuma, dole ne ga kowane baligi da baliga su nemi ilimi, domin gudanar da kowace mu’amala ta rayuwa. Kamar yadda mai Ahlari ya faɗa, cewa ba ya halatta ga muƙallafi ya aikata wani abu, har sai ya san hukuncin Allah da manzonSa a kansa. Don haka idan ana batun ibadar aure, ya zama wajibi ga ma’aurata su san sharuɗɗa da dokokin Allah a game da auren da zamantakewa tun kafin ma su tunkari juna da nufin ƙulla wannan babbar ibada.

Ga duk mace da namijin da ke nufin tunkarar aure, babu shakka wannan littafi na Taya Ni Mu Gyara abin buƙata ne, domin kuwa zai taimaka wajen haska masu hanya, domin cin ma gamsassar nasara a zamantakewar aure da juna. Dalili kuwa shi ne, littafin ya samar da muhimman turaku na ilimi da shawarwarin yauƙaƙa da inganta zamantakewa a tsakanin juna. Dalili ke nan ma a wannan sharhi, zan fi maida hankali da yin ishara ga muhimman darussan da littafin ya ƙunsa.

Muhimman Darussan Littafin:

A cewar marubuciyar littafin: “Na rubuta wannan littafi ne domin ganin na ba da tawa gudunmowar ni ma, musamman a kan abin da ke faruwa na yau da kullum a gidajen ma’aurata.” – Shafi na 3.

Tabbas abubuwa marasa daɗi da tada hankali suna faruwa a gidajen aure, waɗanda suka haɗa da yawan rabuwar aure, faɗace-faɗace tsakanin ma’aurata da ‘yan uwansu da ma sauran matsaloli birjik da ba za su lissaftu a nan ba. Don haka wannan littafi ke yin kira da babbar murya ga maza da mata da iyaye, domin su “taya juna wajen kawo gyara ga al’amarin.”

Tun a shimfiɗar littafin, a shafi na 4 zuwa na 5, marubuciyar littafin nan ta fara kintsa masu niyyar aure, inda ta bayyana dalla-dalla ma’anar aure. Ta samar da gamsasshen bayani tare da ƙwaƙƙwarar hujja daga Shari’ar Musulunci.

Marubuciyar ta ci gaba da ilimantar da maza da mata domin su fahimci irin junansu da za su nema da aure, domin samun dace. Tun daga shafi na 5 zuwa na 8, ta baje kolin siffofin maza da matan da suka dace da aure.

Shin wace ce mace tagari kuma yaya siffofinta suke? Duk marubuciyar ta zayyana su. Haka ma ta zayyana amsoshin tambayar shin wane ne miji nagari? Ke nan idan mace ce take shirin aure, to an haska mata irin mazan da za ta zaɓa ta darje. Haka shi ma idan namiji ne, an sanar da shi irin matar da zai tunkara da aure, domin zaɓa wa ‘ya’yansa uwa tagari. Ba haka nan sasakai ta kawo bayanan ba, sai da ta ɗaure su da ayar Alƙur’ani mai girma.

Saboda irin manyan matsaloli da ƙalubale iri-iri da zawarawa ke fuskanta, marubuciyar nan ta kawo muhimmin ‘Saƙo Na Musamman Ga Zawarawa’ daga shafi na 14 har zuwa na 16. Wannan zai taimaki duk wata da ta samu kanta a matsalar zawarci, yadda za ta kauce wa shiga mummunan yanayi.

Daga shafi na 16 zuwa na 26 kuwa, marubuciyar ta ci gaba ne da yin jagora ga MA’AURATA gaba ɗaya, inda ta bijiro da muhimman batutuwa da shawarwari na bai-ɗaya ga maza da mata, domin yauƙaƙa zamantakewarsu ta ibadar aure.
Haka kuma, wasu muhimman batutuwa da aka ilimantar da mutane a littafin nan sun haɗa da fayyace wasu abubuwa da aka gargaɗi maza da su kauce wa aikatawa ko saɓa yin su ga matansu na aure. An fayyace bambance-bambancen da ke tsakanin Auren Da da kuma Auren Zamani.

Marubuciyar nan ta yi bincike sannan ta gano wasu manyan matsaloli guda 10 da suke gurgunta aure, tare da kawo mafita domin a kauce wa faɗawa cikinsu. Ta bayyana su tare da yin bayani gamsasshe a dukkan su, daga shafi na 28 zuwa na 32.

Wasu bayanan da aka tattauna tare da ilimantar da ma’aurata dangane da su, sun haɗa da batun tarbiyyar yara, kwalliyar ma’aurata ga juna (mata da maza), rashin fahimtar yaren juna da kuma abin da ƙazanta ke haifarwa ga dukkan ɓangarorin na ma’aurata maza da mata.

KISHI, na ɗaya daga abubuwan da kan illata aure, har ma yake haddasa munanan al’amura tsakanin ma’aurata. Sanin haka ya sanya marubuciyar littafin nan ta yi gamsasshen bayani, tun daga shafi na 38, har zuwa na 72.

Abubuwan da aka tattauna dangane da maudu’in kishi a littafin nan sun haɗa da kishin ƙwarai, ma’anar kishi, kishi ibada ne da kuma matsayin kishi a addini.

Sauran bayanan su ne, kishi a al’ada, kishi na ɓangaren mata, kishi na soyayya kafin aure, kishin magabata, makomar kishi a zamanin nan da kuma jerin abubuwan da ke kawo kishi a tsakanin ma’aurata.

Akwai bayani game da ma’anar kishiya. Shin me ke sanya maza auren mace fiye da ɗaya? Haka kuma an amsa wannan tambayar ga matan da suke cewa: “Me Zan Yi In Zauna Ni Ɗaya A Wajen Mijina? Akwai bayanin yadda ya dace namiji ya gudanar da tsarin gidansa. Akwai kuma dubaru 10 da mace za ta yi a ɗauka ta asirce mijinta.

Duk dai a cikin wannan maudu’i na kishi, marubuciyar ta kawo bayani kan ɗabi’un wasu ‘yan mata kafin aure. Shin idan namiji zai ƙara aure, me ya kamata ya yi? An bayyana dalla-dalla. Haka kuma an jero lissafin nau’ukan kishi masu muni da ke akwai guda uku, kamar kuma yadda aka zayyano abubuwa biyar na kishi mai kyau.

Sauran bayanan sun haɗa da hikimomin da za su taimaka a zamantakewa da kuma rawar da iyaye za su taka wajen kishi.

Wasu Kurakurai A Littafin:

Babu shakka marubuciyar littafin nan ta yi ƙoƙari matuƙa, musamman yadda ta samar da babban ilimi a cikin taƙaitattun warƙoƙin littafi mai shafi 72. Sai dai kasancewar ɗan Adam ajizi ne kuma da cewa hannun marubuci makaho ne, akwai wasu ‘yan kurakurai na ɗab’i ko na nawahu da suka bayyana nan da can, kodayake ba su taka kara suka karya ba. Haka kuma, na lura da cewa, duk da ƙima da darajar littafin nan, babu Lambar Ingancin Littafi Ta Duniya (ISBN).
A shafi na 23, shawara ta 13, marubuciyar ta ce: “Don Allah kada ki kasance mai yawan roƙo, ko Allah ba Ya so, kuma yawan roƙo yana kawo jin haushi da gundura…”

Duk da cewa wannan shawara mai kyau ce ta ɓangaren mace da mijinta, amma kuskure ne a ce “Allah ba Ya son roƙo” domin kuwa roƙon Allah ma ibada ne. Allah Yana son a roƙe shi kuma a dogara da shi, kasancewar Shi Allah Rahman ne, Mai Kyauta kuma Rahim, Mai Jin Ƙai. Wajibi ne a roƙi Allah kuma rashin roƙon Allah ma laifi ne.

A shafi na 39, inda marubuciyar ke bayyana ma’anar kishi, ta ce: “Kishi, wani yanayi ne da mutum ko aljani (mace ko namiji) kan tsinci kansu da burin mallakar…”

A ina marubuciyar ta fahimci rayuwar aljanai da har za ta doka misali da yanayin auratayyarsu? Kamata ya yi bayani ya tsaya kan mutane kaɗai, domin su ne zahiri kuma su ake wa bayani, ba aljanai ba.

A shafi na 47, an rubuta sunan ɗaya daga matan Manzon Allah (saw) da kuskure. An rubuta “Zainab bintu jahaz” maimakon “Zainab Bint Jahash.”

Kammalawa:

Babu shakka littafin nan babban kandami ne na ilimi, wanda zai amfani al’umma, musamman ma jagora ne ga maza da mata da ke niyyar aure da ma ma’auratan da ke cikin da’irar aure. Ina shawartar marubuciyar da ta yi ƙoƙarin inganta shi a bugu na gaba, wajen gyara ‘yan kurakuran da idona ya hango. Haka kuma ina kira ga hukumomin ilimi da makarantu da ɗakunan karatu da gidauniyoyin tallafin ilimi da iyaye maza da mata da su tanadi wannan littafi, domin kuwa babban jagora ne na inganta da gyara zamantakewar aure.

~~~~~~~
Bashir Yahuza Malumfashi, Babban Editan Mujallar Taskar Gizago (Laraba 05-07-1445 BH, 17-01-2024).
~~~~~~~

Previous Post

Shugaba Tinubu Ya Naɗa Minista Idris Cikin ‘Yan Kwamitin Garambawul

Next Post

Da Alama Super Eagles Za Su Kawo Kofin AFCON Bana

Related Posts

Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut’a
Adabi

Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut’a

January 17, 2026
SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)
Adabi

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

December 23, 2025
Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine
Adabi

Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine

December 6, 2025
Next Post
Da Alama Super Eagles Za Su Kawo Kofin AFCON Bana

Da Alama Super Eagles Za Su Kawo Kofin AFCON Bana

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

My Takeaways from IBB’s Autobiography

My Takeaways from IBB’s Autobiography

March 18, 2025
TUKUR BURATAI: Janar, Malamin Makaranta, Marubuci Kuma Saraki

TUKUR BURATAI: Janar, Malamin Makaranta, Marubuci Kuma Saraki

August 7, 2023
Ƙarin Albashi: ‘Yan Siyasa Za Su Fara Girbi Cikin Damina

Ƙarin Albashi: ‘Yan Siyasa Za Su Fara Girbi Cikin Damina

June 22, 2023
Shin Ka Kuwa Kalli Fim Ɗin The Lord of the Ring

Shin Ka Kuwa Kalli Fim Ɗin The Lord of the Ring

May 29, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)
  • Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya
  • Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut’a

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

January 21, 2026
My 83rd Birthday and the Kindred Spirit

Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya

January 19, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.