• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Tuesday, May 12, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

Zuwa Ga Gwamna Abba Kabir Yusif

BUƊAƊƊIYAR WASIKA

Hamisu Lamiɗo Iyantama by Hamisu Lamiɗo Iyantama
August 9, 2024
in Gizago
0
Zuwa Ga Gwamna Abba Kabir Yusif

A hagu, Gwamna Abba Kabir Yusif tare da su Hamisu Lamiɗo Iyantama a gefen dama

15
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Zuwa Ga Gwamna Abba Kabir Yusif

Daga Hamisu Lamiɗo Iyantama

Related posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026

Kamar kullum, ina mai ƙara jinjina maka bisa namijin ƙoƙari da kake ta yi domin ganin ka tabbatar wa da mutanen Kano kai na ƙwarai ne kuma mai kishin jiharka da al’ummar cikinta.

Shawarwari:

√ Domin sauƙaƙa wa mutanen jiharka ta Kano sauƙin tsadar rayuwa, dangane da kayan masarufi; ina ba da shawara ga mai girma da ya duba yiwuwar dawo da Kano Cooperatives, wadda ta yi tasiri wajen sauƙaƙa wa masu ƙaramin ƙarfi a wani lokaci da ya gabata.

A kafa Cooperatives a kowace ƙaramar hukuma. A ɗauki tsauraran matakai domin tabbatar da cewa tsarin ya tafi yadda ya kamata. Na san ka fahimci abin da nake nufi.

√ Mai girma Gwamna, ka zauna da masu manyan kanfanoni da ke Kano da wajen Kano, domin duba yadda gwamnati za ta dinga karɓar kayan masarufi daga wajensu a farashi mai sauƙi. Ita kuma Gwamnati ta tura su zuwa Cooperatives, domin sayarwa ga al’ummar gari cikin sauƙi. Wannan zai taimaka sosai wajen rage yawan tashin farashin da ‘yan kasuwa ke yi wa al’ummar gari na ba gaira ba dalili.

√ Mai girma Gwamna, ka zauna da Dangote da BUA da su Mangal, da duk wani mai hannu da shuni, domin ganin sun mara wa wannan ƙuduri na kafa Hukumar Sayar Da Kayan Masarufi Cikin Sauƙi Ga Al’umma, su dinga raba wa Cooperatives; kamar yadda suke raba wa ‘yan kasuwa.

√ Yallaɓai, a ƙirƙiro tsarin da da ma’aikata na jiha da ƙananan hukumomi za su dinga sayen kayen abinci ta wannan tsari a duk wata. Duk ma’aikacin da ke da buƙatar sayen kayan abinci cikin rahusa, sai ya nuna, ya sanar da hukumar da yake aiki da ita. Ita Kuma hukumar ta tsara yadda za a dinga tura wa kanfanoni kuɗaɗensu. Shi kuma mai’aikacin a cira a cikin albashinsa, abin da ya yi saura sai a tura masa cikin asusunsa na banki.

√ A duba wuri kamar Ado Bayero Mall, a tanadi wurare na musamman, kamar guda 15 a Kano, a ba su tsaro na musamman, a jibge kayan masarufi, wanda zai bai wa masu sayan kayan masarufi na yau da kullum damar samu cikin sauƙi ga al’ummar gari. Amma ban da sayar wa masu sari.

√ Wata kuma shawarar ita ce, a dakatar da fitar da kowanne nau’i na kayan masarufi zuwa wasu jihohi, har zuwa wani lokaci. Domin fitar da kayan zuwa can yana ɗaya daga cikin abin da yake haifar da hauhawar farashin. Kuma a dakatar da shigowar kowane irin kayan masarufi da za a sayar a nan Jihar Kano, har sai gwamnati ta tabbatar da cewa za a sayar a kan farashi da jama’a za su iya saye, ba tare da sun takura ba.

√ Ranka ya daɗe, a daure a kafa hukumar da za ta dinga saita farashin kayan masarufi a duk shekara, domin wannan hukuma na da muhimmancin gaske, idan har an samu masu tsoron Allah a cikinta.

√ A irin tallafin da kake bayarwa ga al’ummar Jihar Kano domin su samu sauƙin rayuwa da rage raɗaɗin tsadar rayuwa; a kafa mana hukuma da za ta dinga bayar da tallafi da sassauci a kan kayan abinci kawai lokaci zuwa lokaci. Kuma a tabbatar da cewa talaka ko mai ƙaramin ƙarfi zai fi kowa morar wannan tsari, duba da yadda gwamnatin jiha da ta tarayya ke ta turo kayan abinci amma ba sa kai wa ga waɗanda ya kamata su mora.

√ Mai girma Gwamna, na ga ka yi ƙoƙari sosai wajen tabbatar da ba da takin zamani kyauta ga manoma kuma mafiya yawa sun samu tagomashin. To yallaɓai a ƙara duba yiwuwar ba su tallafin kayan feshi da sabbin iri da ke kawo amfani mai yawan gaske. Amma a yi masu takunkumin cewa za su sayar da kayan da suka noma cikin farashi mai sauƙin gaske. Sannan a tare kayan da suka noma domin amfanin al’ummar jiha kawai. Idan kowa ya wadata a gida, babu laifi a sayar wa da na waje. Waɗannan hanyoyin za su taimaka wajen rage hauhawar farashin ba gaira ba dalili da manyan ‘yan kasuwa suke yi.

√ Mai girma Gwamna, za a iya amfani da Hukumar Consumer Protection Agency ta Jihar Kano wajen aiwatar da waɗannan shawarwari.

√ Ina ƙara yaba maka ganin yadda ka ɗauki matakin zama da manyan ‘yan kasuwa, ganin yadda suka zaburar da farashin kayan masarufi cikin lokaci ƙanƙani. Allah Ya sa zaman ya haifar mana da alheri.

√ Waɗannan matakai, a tunanina, su ne kawai za a yi wa gyara ko kuma a canja su zuwa abin da ya fi dacewa. Akwai ƙarin haske a kowacce shawara idan an buƙaci hakan daga gare ni.

Daga ƙarshe, ni ne dai wannan masoyin wannan gwamnati mai albarka, wadda muka wahalta mata ba dare ba rana da tunaninmu da faɗa-a-jin-mu da Jama’armu da rubuce-rubuce masu ɗaukar hankali har Allah Ya ba mu nasara.

Har kullum dai ni Kano ce a gabana. Mai girma Abba Kabir Yusif nake wa fatan alheri.

Allah Ya sa wannan sako na shawarwari sun zo gare ka – Amin.
__________
Hamisu Lamiɗo Iyantama, Kano

Previous Post

VENOM

Next Post

SHAWARA TA FI MUHAWARA

Related Posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi
Gizago

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
Gizago

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista
Gizago

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
Next Post
SHAWARA TA FI MUHAWARA

SHAWARA TA FI MUHAWARA

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (3)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (3)

January 27, 2026
Ɗan Iyan Galadiman Katsina Emerges Chairman of Arewa Consultative Forum

Ɗan Iyan Galadiman Katsina Emerges Chairman of Arewa Consultative Forum

June 19, 2025
Buhari & Tinubu Era: Lingering Debt, Nigeria’s Woes and the Suffering Masses

Buhari & Tinubu Era: Lingering Debt, Nigeria’s Woes and the Suffering Masses

July 31, 2025
KUSKUREN MASU JUYIN MULKIN KASAR NIJAR

KUSKUREN MASU JUYIN MULKIN KASAR NIJAR

August 9, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (12)
  • Malumfashi An Yi Babban Rashi
  • Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (12)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (12)

May 12, 2026
Malumfashi An Yi Babban Rashi

Malumfashi An Yi Babban Rashi

May 11, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.