Gasar Kofin Ƙwallon Ƙafa Ta Duniya: Jibi Ne Fa
Daga Bashir Yahuza Malumfashi
__________
Yayin da jibi Alhamis ake fara Gasar Kofin Kwallon Ƙafa Ta Duniya (FIFA 2026) a ƙasashen Amurka, Kanada da Mexico, ana sa ran za ta kasance ɗaya daga cikin manyan gasa mafi ƙayatarwa a tarihin ƙwallon ƙafa.
Kamar yadda Kamfanin Dillacin Labarai na Reuters ya ruwaito, wannan ne karo na farko da za a samu ƙasashe 48 da za su fafata a gasar, maimakon ƙasashe 32 da aka saba da su; lamarin da zai ba ƙarin ƙasashe damar nuna bajintarsu. Hakan zai sanya gasar ta ƙara zafi, armashi da kuma ɗaukar hankali, tun daga matakin rukuni har zuwa wasan ƙarshe.
Daga cikin fitattun ‘yan wasan da ake sa ran za su haskaka a gasar, akwai Kylian Mbappé, Erling Haaland, Jamal Musiala, Lionel Messi, Cristiano Ronaldo, da kuma Neymar. Duk da cewa wasu daga cikinsu sun manyanta amma har yanzu suna da ƙwarewa da gogewar da za su iya sauya sakamakon wasa a kowane lokaci.
Idan aka duba ƙasashen da ake ganin za su yi abin kirki a gasar, ƙasashen Turai suna kan gaba. Spain, France, England, Germany da Portugal suna cikin manyan waɗanda masana da masu hasashen sakamako ke ganin za su iya kai wa matakin ƙarshe. Haka kuma ba za a manta da Argentina da Brazil ba, domin suna da babbar ƙungiya, wacce ta goge a fafatawa a manyan gasa.

Kafar talabijin ta CBS Sports ta ruwaito cewa, a nahiyar Afirka kuwa, ƙasar da mafi yawan masana ke hasashen za ta taɓuka abin kirki, ita ce Morocco. Bayan ta yi nasarar wasan kusa da na ƙarshe a gasar 2022, Morocco ta ci gaba da nuna bajinta a wasannin neman gurbin shiga gasar ta duniya kuma tana cikin ƙasashen Afirka da ake ganin za su iya sake girgiza manyan ƙasashe.
A rahoton BBC kuwa, masana sun ce baya ga Morocco, ana sa ran Senegal za ta yi ƙoƙari sosai, duk da ta samu kanta a cikin rukunin ƙasashe masu ƙwarewa. Ƙungiyar tana da gogaggun ‘yan wasa da suka saba buga manyan wasanni kuma za ta iya kai wa zagaye na gaba, idan ta yi amfani da damar da za ta samu.
Haka kuma ƙasar Egypt tana da kyakkyawar damar yin bajinta a gasar ta bana saboda kasancewar Mohamed Salah cikin tawagar, yayin da Ivory Coast ke da haziƙan matasan ‘yan ƙwallo masu iya ba da mamaki.
Wani abin da zai iya ba da mamaki a gasar, shi ne yadda ƙananan ƙasashe za su yi amfani da sabon tsarin gasar mai ƙungiyoyi 48. A tarihin kofin duniya, kusan kowace gasa tana samar da wata ƙasa da ba a yi tsammani ba, wadda take samun nasarar isa mataki mai nisa. Saboda haka, ba abin mamaki ba ne idan muka ga ƙasashe irin su Japan, Norway ko wasu daga Afirka suna girgiza manyan ƙasashe.
A taƙaice, idan za a yi hasashe, ƙasashen France, Spain, Brazil da Argentina su ne ke da damar lashe kofin gasar ta bana. A Afirka kuwa, Morocco ce take da mafi girman damar kai wa matakin kusa da na ƙarshe a gasar, yayin da Senegal da Egypt za su iya taka muhimmiyar rawa; idan suka samu kyakkyawar sa’a a wasanninsu na farko.
Idan hakan ta faru, akwai yiwuwar mu ga wata ƙasar Afirka ta sake kafa sabon tarihi a wannan gasa. A bana dai za a gurza leda, ba tare da Ƙungiyar Super Eagles ta Najeriya ba, domin kuwa “Giwar ta Afirka” ta kasa kai bantenta na zuwa gasar.











