• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Tuesday, September 15, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Hassan Maina Kaina Ya Zama Babban Editan Africa Radio International Na Farko

BABBAN LABARI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
October 9, 2025
in Babban Labari
0
Hassan Maina Kaina Ya Zama Babban Editan Africa Radio International Na Farko

Babban Editan ARI na farko, Hassan Maina Kaina

218
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Hassan Maina Kaina Ya Zama Babban Editan Africa Radio International Na Farko
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Hassan Maina Kaina


                       _______________
Hukumomin sabon Gidan Rediyon Afrika (Radio International – ARI), wanda zai fara gabatar da shirye-shiryensa a gobe Juma’a, ya naɗa shahararren ɗan jarida, Hassan Maina Kaina a matsayin Babban Edita kuma Shugaban Hukumar Gudanarwa (Editor-In-Chief/CEO).

Related posts

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

September 9, 2026
Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta

Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta

September 3, 2026

Haka kuma, Hukumar gudanarwar, a wata takardar manema labarai da ta saki, ta sanar da sunayen shugabannin da za su jagoranci tashar rediyon, wacce aka kafa domin ƙarfafa muryoyin ‘yan Afrika da kuma gina labaran gaskiya na nahiyar.

Bayan Hassan, wanda aka naɗa a muƙamin Babban Edita kuma Shugaban Hukumar Gudanarwa, an kuma naɗa Mohammed Abba Jami’in Tsara Shirye-shirye da Tabbatar da Gudanuwar Ayyuka (Planner/Fixer). A’isha Mu’azu, ita ce Mataimakiyar Edita, wacce za ta jagoranci ɓangaren ƙirƙira da tsara shirye-shirye a kafafen rediyo da intanet.

Sauran sun haɗa da Idriss Abdallah Bako, Edita a ƙasar Ghana, wanda shi zai kula da shirye-shiryen gidan rediyon a Yammacin Afrika. Shi kuwa Souley Mumouni Barma, shi ne Edita, a Jamhuriyar Nijar, wanda kuma zai kula da Yankin Sahel. Sai Maimunatou Sadou, Edita a Jamhuriyar Kamaru kuma za ta kula da Tsakiyar Afrika.

Yayin da take magana daga babban ofishinta da ke Washington, D.C. Manajar-Edita ta ARI, Binta Suleiman Yero ta bayyana cewa: “Tsarin wannan kwamitin shugabanci, wata babbar alama ce ta ci gaba a tafiyarmu. Mun haɗa ƙwararrun masu hangen nesa daga fannoni daban-daban na jarida, sadarwa, fasahar zamani da kuma hulɗar al’umma. Hazakarsu za ta taimaka wajen cin ma burin ARI na haɗa kan ‘yan Afrika da ke cikin nahiyar da waɗanda ke ƙasashen waje, domin su sami murya mai ƙarfi a faɗin duniya.”

Hassan Maina Kaina a bakin aiki

Sababbin shugabannin, ana sa ran za su kula da tafiyar da gidan rediyon cikin tsari, haɓaka shirye-shirye da gudanarwa, yayin da tashar ke shirin ƙaddamar da manyan shirye-shiryenta a faɗin Afrika da ma duniya baki ɗaya a gobe Juma’a.

Daga ƙarshe, ta ƙara da cewa: “Da waɗannan ƙwararrun ma’aikata da muke da su, ARI ta shirya tsaf don kafa sabon tarihi a harkar watsa labarai a Afrika. Burinmu shi ne isar da sahihan labarai, waɗanda ke da jan hankali da tattaunawar haɗin kai, waɗanda za su dace da masu sauraronmu daga sassa daban-daban na duniya.”
__________

Previous Post

Prince Abdussamad Badamasi: Allah Tashi Kafaɗarka

Next Post

Abubakar Dalhatu Zurmi: A True Picture of a Patriot

Related Posts

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?
Babban Labari

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

September 9, 2026
Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta
Babban Labari

Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta

September 3, 2026
KATSINA_2026: Bikin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya
Babban Labari

KATSINA_2026: Bikin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya

August 29, 2026
Next Post
Abubakar Dalhatu Zurmi: A True Picture of a Patriot

Abubakar Dalhatu Zurmi: A True Picture of a Patriot

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

A Review of Philip Chikwuedo Asiodu: A Legacy of Dedication and Service

Sharhi Kan Littafin Tarihin Philip Chikwuedo Asiodu

January 27, 2026
SUBHANALLAHI: ‘Yan Sanda Sun Kulle Danladi Haruna

SUBHANALLAHI: ‘Yan Sanda Sun Kulle Danladi Haruna

October 7, 2023
DAGA TEBURIN RENO OMOKRI

DAGA TEBURIN RENO OMOKRI

March 21, 2025
ZAKIN FAMA – A Poem

ZAKIN FAMA – A Poem

September 23, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • MALAM SULE LAMIDO: Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78
  • ADO GWANJA – Ya Samu Lafiya
  • SUNANTA UMMU-KHULSUM

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

MALAM SULE LAMIDO:  Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78

MALAM SULE LAMIDO: Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78

September 15, 2026
ADO GWANJA – Ya Samu Lafiya

ADO GWANJA – Ya Samu Lafiya

September 13, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.