• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, October 12, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Labarai

Gamayyar Ƙungiyoyin Tsofaffin Ɗalibai Sun Roƙi Gwamnan Katsina Ya Girke Jami’ar Kimiyyar Lafiya A Malumfashi

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
June 27, 2023
in Labarai
0
EFCC Ta Kai Farmaki Jihar Katsina
121
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Daga Wakilinmu

Gamayyar Ƙungiyoyin Tsofaffin Ɗaliban Jihar Katsina sun yi kira ga Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa da ya ajiye mazaunin Jami’ar Nazarin Kimiyyar Lafiya a garin Malumfashi, Shiyyar Sanatan Kudancin Katsina.

Related posts

Janar S.K. Usman Ya Zama Dakta A Fannin Nazarin Tsaro

Janar S.K. Usman Ya Zama Dakta A Fannin Nazarin Tsaro

September 26, 2026
Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

September 8, 2026

Da yake magana a madadin ƙungiyar, ɗaya daga cikin shugabanninta, Badamasi Haiba ya ce, idan aka yi duban nazari, garin Malumfashi yana tsakiyar ƙananan hukumomi 11 da ke cikin Shiyyar Sanatan Kudancin Katsina, don haka nan ya kamata a ajiye mazauninta domin amfanin kowa cikin sauƙi.

Ya ƙara da cewa kuma ajiye jami’ar a Malumfashi shi ne daidai da adalci, domin hakan zai sauƙaƙa wa ɗaukacin ɗaliban da suka fito daga kowane lungu na shiyyar.

“Idan aka lura, sauran ƙananan hukumomi da ke Kudu Maso Kudancin shiyyar, suna maƙwabtaka da Jami’ar Ahmadu Bello da kuma Asibitin Koyarwa na ABU da ke Shika, ga kuma Kwalejin Share Fagen Shiga Jami’a (SBRS) da ke Funtuwa. Don haka Malumfashi ne garin da ya fi cancanta a ajiye wannan sabuwar jami’a da ake son kafawa,” in ji Badamasi.

Ya ce kuma hakan zai taimaka wa ƙananan hukumomin yankin Karaɗuwa da ma na maƙwabtansu na Jihar Kano.

“Malumfashi a matsayinsa na Hedkwatar Masarautar Katsina a shiyyar, yana dukkan gine-ginen da ake buƙata da sauran abubuwan rayuwa domin riƙe jami’ar, kuma hakan zai sauƙaƙa wa Gwamnatin Tarayya kashe kuɗi yayin kafa mazauninta,” a cewarsa.

Badamasi ya tunatar da Gwamna Raɗɗa cewa an haramta wa Shiyyar Sanatan Kudancin Katsina samun wata babbar makaranta mai darajar ba da digiri ko wata cibiyar ilimi babba, kasancewar duk an tara manyan makarantun, an kafa su a Tsakiya da Arewacin Katsina.

“Ya mai girma Gwamna, lokaci ya yi da za ka karya wannan ƙwarin, ka rubuta sunanka da ruwan gwal, ta hanyar amincewa da kafa Jami’ar Nazarin Kimiyyar Lafiya ta Gwamnatin Tarayya a Malumfashi, a Shiyyar Sanatan Kudancin Katsina, kasancewar yanki ne mai yawan al’umma, wanda ya fi kowane yankin yawan ƙuri’u a Jihar Katsina.” Kamar yadda Badamasi ya jaddada.

Previous Post

Tinubu Ya Karrama Fitattun ‘Yan Arewa

Next Post

Ɓarayin Fetur Sun Kwashi Kashinsu A Hannun Sojojin Najeriya

Related Posts

Janar S.K. Usman Ya Zama Dakta A Fannin Nazarin Tsaro
Labarai

Janar S.K. Usman Ya Zama Dakta A Fannin Nazarin Tsaro

September 26, 2026
Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin
Labarai

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

September 8, 2026
Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda
Labarai

Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda

September 6, 2026
Next Post
Ɓarayin Fetur Sun Kwashi Kashinsu A Hannun Sojojin Najeriya

Ɓarayin Fetur Sun Kwashi Kashinsu A Hannun Sojojin Najeriya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Ƙuncin Rayuwa: Matasa Ku Tashi Ku Nemi Ilimi Da Sana’a – In Ji MAK

Ƙuncin Rayuwa: Matasa Ku Tashi Ku Nemi Ilimi Da Sana’a – In Ji MAK

August 15, 2023
Babban Burina A Rubutu: In Bar Baya Mai Kyau – AHA

Babban Burina A Rubutu: In Bar Baya Mai Kyau – AHA

November 4, 2023
COMMENDATION: Essence of Loyalty to a Principal

COMMENDATION: Essence of Loyalty to a Principal

August 20, 2025
Israel/Palestine Conflict: TY Buratai Foundation Calls for Permanent Ceasefire

Israel/Palestine Conflict: TY Buratai Foundation Calls for Permanent Ceasefire

November 29, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Kwamishina Ɗahiru Ya Harzuƙa Maryam Jan Kunne
  • NASIHARMU TA YAU (18)
  • Rikici Ya Kacame Tsakanin Moofy Da Tage A Kan Pantami

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Kwamishina Ɗahiru Ya Harzuƙa Maryam Jan Kunne

Kwamishina Ɗahiru Ya Harzuƙa Maryam Jan Kunne

October 11, 2026
NASIHARMU TA YAU (18)

NASIHARMU TA YAU (18)

October 11, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.