• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Saturday, May 2, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

Ministan Tsaro Janar Christopher Musa: Shawara Da Fatan Alheri

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
December 3, 2025
in Gizago
0
Ministan Tsaro Janar Christopher Musa: Shawara Da Fatan Alheri

Ministan Tsaro, Janar Christopher G. Musa

16
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Ministan Tsaro Janar Christopher Musa: Shawara Da Fatan Alheri

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
Ministan Tsaro, Janar Christopher G. Musa


                         •••••••
Ta tabbata dai Janar Christopher Gwabi Musa shi ne sabon Ministan Tsaron Najeriya. Wannan kuwa ya biyo bayan wata wasiƙa da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio. Shugaban ya miƙa sunan Janar Musa domin ya gaji Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, wanda ya yi murabus a ranar Litinin da ta gabata.

Janar Musa, mai shekaru 58, soja ne ƙwararre wanda ya yi aiki a matsayin Babban Hafsan Tsaro daga 2023 zuwa Oktoba 2025. Ya taɓa lashe Kambin Colin Powell a shekarar 2012 saboda ƙwarewarsa a aikin na soja.

An haifi Janar Musa a Sokoto a 1967, kuma ya yi makarantar firamare da sakandare a can kafin ya halarci College of Advanced Studies da ke Zariya. Ya kammala karatu a 1986 sannan ya shiga Nigerian Defence Academy a shekarar nan take, inda ya samu Digirin Farko a fannin Kimiyya, a shekarar 1991.

An ɗaura wa Janar Musa muƙamin Sakan Laftanar a 1991 kuma tun daga lokacin ya ci gaba da kyakkyawar tafiya a harkar soja. Daga cikin ofisoshin da ya taɓa riƙewa a gidan soja, suna haɗa da: General Staff Officer 1, Training/Operations a Hedikwatar Runduna ta 81 da Commanding Officer, Battalion ta 73 da Assistant Director, Operational Requirements, Department of Army Policy and Plans da Infantry Representative/Member, Training Team, HQ Nigerian Army Armour Corps.

A 2019, ya yi aiki a matsayin Deputy Chief of Staff, Training/Operations, Hedikwatar Infantry Centre and Corps. Ya taɓa zama Kwamandan, Sector 3, Operation Lafiya Dole da Kwamandan Sector 3, Multinational Joint Task Force a yankin Tafkin Chadi.

A 2021, an naɗa Janar Musa a matsayin Kwamandan Yaƙi na Operation Haɗin Kai. Daga baya kuma ya riƙe mukamin Kwamandan Rundunar Sojan Ƙasa, kafin daga bisani Shugaba Tinubu ya naɗa shi muƙamin Babban Hafsan Tsaro a 2023. Ya yi ritaya daga aikin soja a cikin watan Nuwamba da ya gabata.

Babu shakka Janar Musa ya samu shaidar nagarta daga sassa daban-daban na ƙasar nan. An shaide shi da cewa nagartaccen mutum ne da ba ruwansa da ƙabilanci. Haka kuma a lokacin da aka sanar da naɗa shi wannan muƙami na Ministan Tsaro, mutane da dama sun yi masa fatan alheri kuma sun ba da tabbacin cewa lallai an ajiye ƙwarya a daidai gurbinta.

A yayin da muke yi masa fatan alheri, bari kuma in ba shi wasu ‘yan shawarwari, domin ya fuskanci wannan sabon muƙami da gasken gaske. Wannan kuwa saboda la’akari da yanayin da ake ciki dangane da taɓarɓarewar harkokin tsaro a ƙasar nan fiye da tunanin mai tunani.

Ya Janar, ka fi ni sanin babban ƙalubalen tsaro da ke addabar ƙasar nan. A Arewa, ta’addancin ‘yan Boko Haram da takwarorinsu ba ɓoyayye ba ne a gare ka. Haka kuma kana sane da balahirar ‘yan bindiga, masu satar mutane domin kuɗin fansa. Haka ma a Kudancin Najeriya, kana sane da masu tada ƙayar baya domin kafa ƙasar Biyafara da sauransu. Lallai ne sai ka yi jan ido, ka haɗa kan jami’an tsaro, domin ganin an samu nasarar daƙile su.

Lallai ne ka yi duk mai yiwuwa, ka haɗa kai da masana tsaro da dukkan masu ruwa da tsaki a harkar tsaro domin shawara da kuma ɗaukar matakan da suka dace, domin samun nasara.

Muna yi maka fatan alheri tare da addu’ar Allah ya ba ka nasarar yin duk abin da ya dace, domin samar da zaman lafiya da ingantaccen tsaro a Najeriya.
_______________

Previous Post

Shawara Ga Gwamnonin Arewa

Next Post

Nazarin Littafin Da Ke Bayyana Gaskiyar Lamari Dangane Da Badaƙalar Kuɗaɗe A Tsakanin Ƙasashen Duniya

Related Posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi
Gizago

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
Gizago

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista
Gizago

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
Next Post
Global Standards and Regional Realities: The Evolution of Anti-Money Laundering… Under Review

Nazarin Littafin Da Ke Bayyana Gaskiyar Lamari Dangane Da Badaƙalar Kuɗaɗe A Tsakanin Ƙasashen Duniya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

WHEN THE SPIRIT WHISPERS: Littafin Tsarkake Tunani Da Samar Da Saita Rayuwa

WHEN THE SPIRIT WHISPERS: Littafin Tsarkake Tunani Da Samar Da Saita Rayuwa

October 11, 2025
Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

April 8, 2026
TSOKACINMU NA YAU (08)

TSOKACINMU NA YAU (08)

March 8, 2025
VENOM

VENOM

August 6, 2024

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana
  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (11)
  • General Buratai (A Poem)

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

April 28, 2026
Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (11)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (11)

April 27, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.