• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, April 26, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

Nazarin Littafin Da Ke Bayyana Gaskiyar Lamari Dangane Da Badaƙalar Kuɗaɗe A Tsakanin Ƙasashen Duniya

SHARHIN LITTAFI

Mu 'azu Umaru by Mu 'azu Umaru
December 3, 2025
in Adabi
0
Global Standards and Regional Realities: The Evolution of Anti-Money Laundering… Under Review

Daga Hagu: Marubucin littafin, Farfesa Abdullahi Y. Shehu, Bangon littafin da kuma Nazari, Muazu Umaru

52
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Nazarin Littafin Da Ke Bayyana Gaskiyar Lamari Dangane Da Badaƙalar Kuɗaɗe A Tsakanin Ƙasashen Duniya

Daga Mu’azu Umaru

Related posts

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

April 11, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
Daga Hagu: Marubucin littafin, Farfesa Abdullahi Y. Shehu, Bangon littafin da kuma Nazari, Muazu Uma

_______________

Sunan Littafi: Global Standards and Regional Realities: The Evolution of Anti-Money Laundering and Countering the Financing of Terrorism Frameworks in West Africa

Marubuci: Farfesa Abdullahi Y. Shehu
Manazarci: Mu’azu Umaru

_______________

Maii Girma Mataimakiyar Shugabar Ƙungiyar Ƙasashen ECOWAS,

Mai Girma Babban Lauyan Gwamnatin Ƙasar Liberia,
Darakta-Janar na Ƙungiyar GIABA,
Tsoffin Manya da Mataimakan Manyan Daraktoci,
Manyan Baƙi Maza da Mata,

Tare da dukkan girmamawa da fatan alheri, a yau nake tsaye a gabanku da nufin gabatar da nazarin wannan gagarumin aiki da Farfesa Abdullahi Y. Shehu ya rubuta. Amma kafin in tsunduma kacokan cikin sharhin littafin, ku ba ni dama in fara bayyana muku wani abu game da marubucin. Wannan kuwa saboda fahimtar marubucin littafin, shi ne matakin farko na fahimtar hikimomi da dunƙulalliyar basirar da ke ƙunshe a babban aikin nasa.

Tarayya Da Zumuncin Shekaru 27:
Na fara haɗuwa da Farfesa Shehu ne a 1998. A cikin waɗannan shekaru 27, na samu damar aiki a ƙarƙashin kulawarsa. A lokuta daban-daban, nakan samu kaina cikin nutsuwa, wani lokacin kuma cikin tsoro! Na yi aiki da shi a wasu lokuta a Kwalejin Hukumar EFCC da ke Karu, Abuja. A nan na fahimci cewa shi mutum ne mai tsantsenin bin ƙa’ida, wanda ke aiki cikin ƙwarewa da inganci. Kuma haka yake buƙatar duk wani da ke ƙasansa ya kasance. Ba ya son aiki da mutum mai kasala ko mai amaja a aiki.

Bayan haka, a tsawon shekaru fiye da goma ina halartar taron Hukumar Kula Al’amuran Muggan Ƙwayoyi ta Duniya a birnin Vienna. Na yi tunanin shi ke nan mun rabu da shi, kwatsam sai ga shi mun sake haɗuwa. A wannan karon, shi ne jami’in tuntuɓa, mai ba da shawara a hukumar ta UNODC.

Haƙiƙa shi jagora ne nagari kuma yana da zuciyar alheri. Ba zan taɓa mantawa da zamanmu a Vienna ba. A duk lokacin da ya lura mun fara kewar gida a Vienna, sai ya kai mu wani gidan cin abinci na ‘yan Najeriya guda ɗaya da ke cikin birnin. Har yanzu ina iya tuna ɗanɗanon jollof ɗin nan. Kodayake na kasa rarrabewa, shin daɗin abincin nake tunawa ko kuma zaman tare mai armashi da muka yi da shi? Ina ganin dukkan biyun nake tunawa. A irin waɗannan lokuta ne, da muke kasancewa da shi, na fahimci halaye da falsafarsa. Na fahimci cewa, shugabanci ba wai tsaurara dokoki da bin ƙa’idoji ba ne, amma shugaba ya ja na ƙasa da shi a jiki cikin mutunci da girmamawa, sannan ya zama mai kwantar masa da hankali; yadda zai ji kamar a gida yake, ba a bakuwar ƙasa ba.

Lokacin da ya gayyace ni in bi shi aiki zuwa Ƙungiyar GIABA, ina da masaniyar kowane ne shi da kuma irin aikin da zan tarar. Tsawon shekaru huɗu na yi a ƙarƙashin shugabancinsa. Na koyi manyan ilimi iri uku: Na koyi muhimman abubuwan da ban taɓa zaton zan koya ba. Na koyi jajircewa da yin aiki tukuru fiye da tunanina. Kuma na samu canjin rayuwa mai kyau kuma mai amfani. Daga bisani ma dai da iyalina duka muka karɓe shi a matsayin ɗan uwanmu. Ba mu da wani zaɓi fiye da haka, domin kuwa ya taka muhimmiyar rawa a rayuwarmu da ba za mu taɓa mancewa ba. A duk lokacin da kake buƙatar wata shawara ko ƙarfafa gwiwa daga gare shi, komai dare ka tuntuɓe shi, a shirye yake ya share maka hawaye. Idan kana buƙatar jagoran da zai faɗa maka gaskiya komai ɗacinta, to ka nemi Farfesa Shehu.

Littafin Da Ya Taskance Hikima Da Tarihi:
Wannan littafi ne da ya feɗe biri har wutsiya dangane da haƙiƙanin gaskiyar lamarin da ya shafi badaƙalar kuɗaɗe a tsakanin ƙasashen duniya. An rubuta shi da Ingilishi da taken: Global Standards and Regional Realities… Littafin ba wai rubutun bincike ne irin na jami’a ba kaɗai, kodayake ya cika wannan ƙa’ida har ma da ɗoriya. Marubucin ya rubuta shi ne cikin armashi da gwanancewa, tamkar dai wasiƙar soyayya zuwa ga Afirka ta Yamma daga masanin da ya san ƙabli da ba’adin yaƙi da badaƙalar da ke tattare da tu’ammali da kuɗaɗen haramun, ta’addanci da kuma laifukan da suka shafi rashawa da almundahana. Mutumin da ya shafe shekaru masu yawa a wannan fage, wanda ya san hawa da sauka, ya sha marƙabu da ƙalubale a wannan yanki namu na Afirka. Shi ne masani mai Digirin-Digirgir (Ph.D.) na farko a fannin yaƙi da cin hanci da almundahanar kuɗaɗe daga fitacciyar Jami’ar Hong Kong.

Tun daga sunan littafin kansa, mai karatu zan iya tantance nagartar bayanan da aka tanadar a cikinsa: Global Standards and Regional Realities. A cikin kalmomin nan biyar, Farfesa Shehu ya taskance manyan batutuwan da suka fassara manyan ayyukan da Ƙungiyar Ƙasashen Afirka ta Yamma Mai Yaƙi da Badaƙalar Kuɗaɗe da Masu Ɗaukar Nauyin Ta’addanci (GIABA: Inter-Governmental Action Group against Money Laundering in West Africa) ta jagoranci gudanarwa na tsawon shekaru 25. Ta yaya za ka aiwatar da shawarwarin da Hukumar FATF ta tsara a birnin Paris kuma su yi tasiri a kasuwannin Dakar, titunan Legas da unguwannin Monrovia da maƙwabtansu? Ta yaya za ka buƙaci cikakkun bayanan kamfanoni da harkokin kasuwanci da mamallakansu na ainihi, a ƙasashen da ake aiki cikin rashin tsari kuma ba a rubuce ba? Ta yaya za ka buƙaci tsarin bibiyar ma’amaloli kai tsaye a wuraren da babu wadatattar wutar lantarki? Wannan littafin duk ya samar da amsoshin waɗannan tambayoyi cikin bayani mai sauƙin fahimta kuma da ƙwarewa ba da molonka.

Sashe na Ɗaya: Bayanai Daga Tushe
Sashe na farko ya samar da cikakken bayani kan tsarin duniya na yaƙi da badaƙalar kuɗaɗen haram da masu ɗaukar nauyin ta’addanci (AML/CFT). Abin da ya bambanta littafin nan da sauran rubuce-rubuce irinsa, shi ne yadda Farfesa Shehu ya iya sauƙaƙe bayanai ba tare da wata sarƙaƙiya ba. Mutum zai fahimci yadda tsarin yake gudana a duniya cikin sauƙi. Misali, marubucin ba kawai zai bayyana mana abin da Hukumar FATF ta faɗa a Shawara ta 10 ba, sai ya bayyana dalilin da ya sa aka samar da shawarar da kuma ƙa’idojin sanin abokin hulɗa, wanda tsari ne da ya samo asali daga bankunan ƙasar Switzerland. Farfesa Shehu ya yi bayani dalla-dalla, ta yadda za a tafiyar da lamurran, koda a ce hulɗa ta haɗa da ɗan kasuwar da ke bakin iyaka, wanda bai taɓa samun wasu takardun shaidar hulɗar kasuwanci ba.

Bayanansa kan tarihin Ƙungiyar ECOWAS na musamman ne. Lokacin da na karanta babi na farko, sai na tuna da farkon aikina, lokacin da muka yi ta yunƙurin nuna buƙatar a samar da hukuma mai zaman kanta. Wannan yunƙuri ne ya haifar da kafa Ƙungiyar GIABA a 2000; tare da yakinin cewa Afirka ta Yamma na iya gina tsarin AML/CFT mai ƙarfi. Rubutunsa game da Muradun ECOWAS na 2050 tare da matsalolin zahiri da suke a ƙasa, waɗanda suke haifar da yanayi mai tada hankali. Wannan shi ne buri ba tare da ruɗu ba, suka ba tare da saka takaici ba.

Sashe na Biyu: Ƙashin Bayan Batun
Idan Sashe na Ɗaya na littafin nan shi ne tushen ginin, to Sashe na Biyu shi ne ɗakin zama kuma madalla, domin ginin ya yi kyau! Babin da ya yi bayani game da kafa Ƙungiyar GIABA (Babi na 6), wanda ya yi masa laƙabi da: “Saboda Da Hannuna A Ciki.” A nan ne muka ga ainihin bayyanar basirar Farfesa Shehu cikakka. Babu shakka, lallai mun shaida yana da hannu sosai a ciki kuma mun gode Allah da samuwar hannun nasa a ciki.

Tarihin da ya bayar na kafa Ƙungiyar GIABA ya ƙunshi ɓangarori. Wani na tarihin kafa ƙungiyar, wani tarihin shi kansa da kuma muhimman bayanan abubuwai ga duk wanda ke sha’awar fahimtar wannan hukuma. Ya tuna da rawar da ya taka wajen duba dokar da ta kafa Hukumar EFCC da kuma irin gudunmawar Malam Nuhu Ribadu (Shugaban Hukumar EFCC na farko) wajen buɗe ƙofar kafa Ƙungiyar GIABA. Babu shakka ya tuno mana da tarihi abin tunawa. Abin kamar jiya ya faro. Lallai tsufa ya kama mu!

Babin da ya yi bayani kan siyasar naɗe-naɗen muƙamai a Ƙungiyar ECOWAS (Babi na 8), babi ne da ya kamata duk wanda ke tababar yadda ƙungiyoyin duniya suke aiki cikin tsantsar cancanta ya karanta. Farfesa Shehu ya feɗe biri har wutsiya, ta yadda sai wanda aka dama da shi ne zai iya samar da waɗannan bayanai.

Wani muhimmin ilimi da na koya daga Farfesa Shehu, shi ne sashen da ya shafi nazarin hanyoyin da suka shafi laifukan almundahanar kudi. Kuma hakan ya tabbatar da abu ɗaya da na fahimta daga wurinsa, cewa lallai shi malami ne. Ba ya ɓoye ilimi domin amfanin kansa shi kaɗai, nufinsa kowa ya fahimta. Shi ya sa ya dage cewa a yi nazarin wannan sashi na typologies, ko da babu masu tallafawa da kuɗi, ko da ƙasashe mambobi ba su sha’awa. Wannan ya ƙara tabbatar mana da yadda ya ɗauki cewa ilimi shi ne jigon nasarar kowane aiki. Ya zaɓile ni da in jagoranci wannan yunƙuri a 2010. Kan haka na sauya daga mai farautar ’yan ta’adda zuwa farautar ilimi. Kuma a gaskiya, har zuwa kawo yau, ban taba yin nadamar wannan zaɓi ba.

Sashe na Uku: Aiki Ga Mai Ƙare Ka
A nan ne Farfesa Shehu ya ture gafakar jami’a, ya rubutu kai tsaye, ya amayar da fasahar da ke kunshe a zuciyarsa. Maudu’in “Tsinkaye Da Darussan Da Na Koya” (Reflections and Lessons Learned), duk da cewa ya kamata a ce ya tsaya ga bayanin nasarorin da ya samu ko kuma koɗa kansa amma ina, malamin sai ya zuba madarar ilimi cikin hikima da basira.

Salon da ya ɗauka na baje kolin ƙa’idojin asali da ake buƙata a aiki, gaskiya, jajircewa, haɗa kai, da inganci, ya yi armashi. Farfesa ba kawai ya gabatar da su a matsayin kalmomi na rubutu ba, amma ya warware zare da abawa, wanda hakan ke nuna ƙwarewarsa a shugabanci da sanin yadda ake tunkarar ƙalubalensa. Idan yana fashin baƙi dangane da gaskiya, ba naƙaltowa yake daga wani kundin ilimin shugabanci ba ne. A’a, yana tuno lokutan da ya zartar da irin wannan hukunci ne cikin juriya da bin ƙa’ida ta hanya mai tsauri, ba mai sauƙi ba, tare kuma da bayyana dalilansa na yin haka.

Babin da ya shafi tantance aikinsa a matsayin Darakta-Janar (2006–2014) ya ƙara wa littafin ƙima, duk da cewa da wasu marubuta ne, tsallake wurin za su yi, don suna ganin kamar za a ce masu sun zama magori mai wasa kansa da kansa. Amma shi Farfesa ba haka yake ba, ba ya barin duk wani abu mai muhimmanci. Shi ya saba da salon cewa, idan akwai bayanai, to ka gabatar. Idan kana da wani ilimi da za ka koya, to ka koya. Idan akwai labarin da zai amfani wasu, to ka bayar da shi. Wannan tsari na tantancewa ya nuna abin da muka sani tun tuni a kan Farfesa Shehu – cewa shi ne ya sauya Ƙungiyar GIABA daga jaririya zuwa babbar hukumar da ta samu nasara da karɓuwa.

A makonni kaɗan da suka gabata, ina cikin duba daftarin littafin nan, tare da ƙara bitar da aka nema in yi, sai na duba kundina da nake ajiye muhimman bayanai, nan na ci karo da daftarin wata wasiƙa, wadda Farfesa Shehu ya taɓa sanya ni na rubuta, domin aikawa ga Shugaban Ƙungiyar ECOWAS na lokacin. Bayan na aika masa, sai Farfesa ya yi wasu ‘yan gyare-gyare a takardar. Na duba gyararrakin da ya yi, na fahimta da cewa ashe na yi sassauci sosai, domin na bi salon lalama a rubutuna. Shi kuwa yana son in fidda magana kai tsaye ba tare da nuƙunuku ba, kamar yadda ƙa’idarsa take ta magana ɗaya-kaifi-ɗaya. Nan take na tuno da cewa, lallai dattijai masu gaskiya ba sa yin waskiya.

Rai Dangin Goro Sai Da Ban Iska:
Yanzu bari a wannan gaɓar in bijiro da wani batu, wanda duk ya san Farfesa Shehu zai fahimta: Ga littafi dai an samar ba na wasa ba. Shafi-bayan-shafi, babu abin da suka ƙunsa sai al’amura masu tsauri da suka shafi lamurran kuɗi, dokoki da tsare-tsaren aikin hukumomi da ma’aikatu irin su FATF da hanyoyin tantancewa, tasiri ko rashin tasirin aiki da sauransu – mutum da ganin wanda ya samar da bayanan nan, ya san bai zo da wasa ko barkwanci ba. Kuma gaskiya ne, lallai babu mai musun cewa bayanan nan suna da muhimmanci.

Amma ni, kasancewar wanda na taɓa yin aiki da shi, na san yana da wata ɗabi’a ta son barkwanci. Akwai wani lokaci, muna tsaka da tattaunawa kan wani aiki, mun zo daidai kan wata gaɓa game da Shawarar Hukumar FATF Mai Lamba 23, kanmu ya ɗauki zafi sai Farfesa Shehu ya karkatar da mu zuwa wani barkwanci, ya ce: “Shin wai ko FATF ma suna tuna abin da suka rubuta?” Wannan barkwanci da ya jefo mana ya sanya muka nishaɗantu, muka samu natsuwa. Ƙwaƙwalwarmu ta yi sanyi.

Irin waɗannan barkwancin ba su samu gurbi ba sosai a littafin nan, kasancewar wannan aiki ne na nazari. Ni ma na kawo shi ne nan domin misali kawai, irin yadda Farfesa ya iya tafiyar da jama’a a yayin aiki. Shi mutum ne mai ɗaukar aikinsa da muhimmanci, amma kuma ba ya da tsauri. Yakan yi iya matuƙar ƙoƙarinsa a kowane aiki.

Mece Ce Manufar Wannan Littafi?
Babu abin da ke cikin littafin nan, illa tsagwaron tarihin da ke cewa lallai za a iya nasara ta hanyar aiki tuƙuru. Yana tabbatar da abin da mutane da dama suka ce ba zai yiwu ba: cewa Afirka ta Yamma za ta iya gina tsarin AML/CFT mai tsafta, cewa GIABA za ta zama wacce duniya ke mutuntawa, cewa ƙasashenmu za su inganta, su samar da abin da ake buƙata; duk kuwa da irin ɗimbin matsalolinmu.

Haka kuma littafin mai gargaɗi ne. A ƙarshe, Farfesa Shehu ya yi magana kan raunin ci gaban da aka samu cikin shekaru 25. Ya ce ƙudurin siyasa ba mai ɗorawa ba ne, musamman abin da ya shafi jimirin aiwatar da ƙudurorin hukumomin AML/CFT. Don haka wajibi ne a ci gaba da bibiyar su. Ya nuna damuwa kan wannan raunin, kuma yaba da hujja a kan haka, musamman idan aka yi la’akari da gajiyawar masu tallafawa, maida hankali kan abubuwa marasa muhimmanci da kuma wahalar da ke tattare da aiki. Wannan kan iya samar da koma-baya.

Wannan littafin dai kira ne ga neman a tashi tsaye a yi aiki. Tamkar dai wata hanya ce da Farfesa Shehu ke aika saƙon cewa: “Ga abin da muka gina tare. Ga dalilin da ya sa aikin yake da muhimmanci. Ga kuma abin da ya rage mu yi a gaba.”

Tsokacina A Mahangata:
Ƙunshiyar littafin yana kama da tarihin aikina. Kowane babi yakan tuna mani abubuwa, musamman dararen da muke kashewa a wurin taruka, nasarori da gazawar da muka samu. Nakan kalli rayuwata a cikin littafin nan, duk da cewa ba a ambaci sunana ba kai tsaye. Amma a duk lokacin da Farfesa Shehu ya ce “mu” a lokacin da yake bayyana ayyukan da suka shafi Ƙungiyar GIABA, nakan samu kaina tsundum a ciki.

Wannan shi ne kyauta da sadaukarwarsa ga shugabanci: Shi mutum ne da yakan mayar da aikinsa da cewa “namu” ne. Bai taɓa mallake nasarar aikin Ƙungiyar GIABA ga kansa shi kadai ba, domin kuwa ya san cewa aikin hukuma tamkar ɗaukar jinka ne, kowa da hannunsa a ciki. Kuma yana da masaniyar cewa, aiki irin wannan, duk da irin wahalarsa, bai cika jawo yabo a fili ƙarara, a kafafen labaru ba. Amma sannu a hankali, yakan samar da canjin da ake buƙata, na inganta al’umma.

A littafin nan, a duk lokacin da ka ji Farfesa yana magana kan “jajirtattun ma”aikatan da suke sadaukar da kansu wajen yaƙi da masu almundahanar kudi,” to yana nufin mutane irinmu da ku da muke zauren taron nan. Haka kuma yana nufin dubban ma’aikata da jami’ai masu bincike a sassa daban-daban na Afirka ta Yamma. Wannan littafin nasu ne, kamar kuma yadda yake nasa.

Matsayata Game Da Littafin:
Shin littafin nan kammalalle ne? A’a. Shi da kansa Farfesa Shehu yana da masaniyar wuraren da za a iya faɗaɗawa ko ingantawa. Haka halinsa yake, bai cika gamsuwa da tsaka-tsaki ba. Kullum nufinsa ya samar da abu mafi kyau da inganci.

Shin littafin ya ƙunshi komai? Eh, matuƙa! Waɗannan kuwa sun haɗa tun daga Yarjejeniyar Vienna zuwa Ayyanawar Yaundé, daga Shawarwarin FATF 40 zuwa tsarin doka na Ƙungiyar ECOWAS. Farfesa Shehu ya samar da rumbun ilimi dangane da abin da ya shafi ayyukan ƙungiyoyi da hukumomin AML/CFT a Afirka ta Yamma.

Shin littafin nan yana da daɗin karatui? Batun gaskiya idan kana neman littafin da za ka karanta a bakin teku, domin nishaɗi, to ba wannan ba ne. Amma idan kana son sanin yadda manyan ƙasashen duniya suka tanadi ƙa’idojin tu’ammali da kuɗi da kuma dangantakarsu ta gaskiya da sauran nahiyoyi, idan kana son sanin yadda aka sha gwagwarmayar shekara 25 domin kafa hukumomi da cibiyoyi irin GIABA da sauransu, idan kana son koyon wannan ilimin daga masani na haƙiƙa, wanda kuma ya rayu a cikin harkar; to tabbas wannan littafin naka ne. Zai ba ka dukkan abin da kake buƙata kuma za ka ji daɗin karanta shi.

Shin littafin nan yana da muhimmanci? Tabbas kuwa, yana da matuƙar muhimmanci. Nan da shekaru 25 masu zuwa, idan ɗaliban ilimi za su yi binciken sanin yadda Afirka ta Yamma ta yaki almundahanar kuɗaɗe da masu ɗaukar nauyin ta’addanci a ƙarni na 21, wannan littafin za su buƙata. Dalili kuwa shi ne, marubucin littafin nan ganau ne, jiyau ne kuma da shi aka dafa kuma aka sauke tukunyar tarihin al’amuran.

Gaba Ta Fi Baya Yawa:
Yayin da GIABA ke murnar cika shekaru 25 da kafuwa, wannan littafi ya iso a daidai lokacin da ya kamata. Yana ba mu damar mu yi waiwaye da nazari mai zurfi. Haka kuma yana yi mana ishara da hanyoyin da za mu ci gaba daga inda aka tsaya, domin kuwa baya ta wuce, gaba ita ke da saura kuma ita ta fi yawa.

Farfesa Shehu ya kammala littafinsa da wani azancin magana da ke cewa: “Idan kana son tafiya da sauri, ka tafi kai kaɗai. Idan kana son tafiya nesa, ka tafi cikin ayari.” Ta tabbata cewa Ƙungiyar GIABA ta zaɓi tafiya mai nisa kuma ta shirya domin cin ma zango na gaba.

Kammalawa: Saƙona ga Marubuci
Yallaɓai Farfesa Shehu, lokacin da ka gayyace ni domin aiki tare da kai a Ƙungiyar GIABA a 2007, sannan na iso a 2009, ka gaya mani cewa zan fuskanci ƙalubale. Ka yi gaskiya, domin na shaida girman ƙalubalen. Ka ce zan koyi abubuwa. Ka yi gaskiya, domin na koyi abin da ban taɓa zato ba. Amma abin da baka faɗa faɗa mani ba a lokacin shi ne, ba kawai shugaban aiki zan samu ba, amma har da jajirtaccen jagora. Ba jagora kaɗai ba, amma mai tallafa mani a lokacin da nake buƙatar tallafi a rayuwa. Haka kuma ba ka ce mani zan samu ɗan uwa, wanda iyalinsa za su ni’imta da shi a matsayin ɗan uwansu na jini, kamar dai yadda ka kasance a gare mu – Ɗan uwa!

Wannan littafi ya dace da kai, domin wani babban abin yabawa ne. Ya fito da hazaƙarka da ƙwarewarka a fagen koyarwa a jami’a, kamar kuma yadda ya bayyana hikimarka ta zahiri. Ya kuma nuna irin natsuwarka da tsantseni wajen tantance bayanai da killace su, kamar kuma yadda ya nuna irin hangen nesanka da girmamawarka ga hukumomi da cibiyoyi. Ya kuma nuna fahimtarka, cewa cibiyoyi da hukumomi ana kafa su ne domin hidima ga al’umma.

Wannan littafi, wani babban goro ne ka ba Afirka ta Yamma. Amma a gare mu, ka ba mu kyautar da ta fi wannan ƙima. Kamar mu da muka yi aiki tare da kai cikin kusanci, ka sadaukar mana da rayuwarka cikin hidima. Mun yi faɗi-tashi, mun koyi ilimi mai yawa daga gare ka. Mun ci, mun sha tare. Ka gayyace mu taruka da tattaunawa iri-iri a Vienna, a Dakar da Paris, wasu lokutan a gidanka ko a ofis ko wuraren taro. Idan muka yi waige kan irin waɗannan manyan hidindimu, lallai wannan littafi, duk da girmansa amma ya tattaro wani yanki ne kaɗan na irin waɗannan sadaukarwa da ka yi wa al’umma.

Muna matuƙar godiya da ka rubuta wannan littafi. Muna godiya da irin namijin aikin da ka yi wa al’umma, wanda shi ne ya haifar da bayanan da ka rubuta a littafin. Muna kuma matuƙar godiya da ka gayyace mu cikin wannan baban aiki.

Shawarata Ta Karshe:
Ga shugabannin Ƙungiyar GIABA na yau da gobe, ga masu tsara doka, ga ɗaliban ilimin tsaro da yaƙi da zamba da almundahanar kuɗaɗe, ga duk wanda yake son fahimtar yadda yankuna ke iya samar da sauyi duk da girman matsaloli da ƙalubalensu, ku nemi littafin nan ku karanta.

Ku nemi littafin nan, ba saboda ya kammala komai ba amma saboda yana ƙunshe da gaskiyar lamari. Ba saboda ya yi sauƙi ba, amma saboda abin buƙata ne da ya wajaba. Ba don marubucin littafin, Farfesa Shehu yana buƙatar jin yabo ba, amma saboda mu muna buƙatar hikimarsa da fasaharsa.

Mahalarta taro, maza da mata, ina farin cikin gabatar muku da wannan littafi mai taken: “Global Standards and Regional Realities: The Evolution of Anti-Money Laundering and Countering the Financing of Terrorism Frameworks in West Africa” na Farfesa Abdullahi Y. Shehu, littafin da ya zo a kan lokaci, wanda marubucinsa ya sadaukar da rayuwarsa wajen tabbatar da tsaro, gaskiya da aminci a yankinmu.

Babu shakka littafin nan abin buƙata ne don nazari. Allah ya sanya wannan aiki ya zama haske ga jami’ai da ma’aikatan Cibiyoyi da hukumomin AML/CFT na Afrika ta Yamma masu zuwa nan gaba. Na gode.
__________
An gabatar da wannan sharhi a bikin cika shekaru 25 na Ƙungiyar GIABA da aka gudanar a otel ɗin Farmington Hotel, Unification Town, Margibi County, Liberia a ranar 21 ga Nuwamba, 2025.

Taƙaitaccen Tarihin Manazarci:
Muazu Umar ya shafe kusan shekaru talatin yana aiki a hukumomi da cibiyoyi daban-daban, tun daga Hukumar Yaƙi da Muggan Ƙwayoyi (NDLEA) da Ƙungiya Mai Yaƙi da Almundahanar Kuɗaɗe ta Afrika ta Yamma. Ya yi aiki a ƙarƙashin Farfesa Shehu, da farko a Kwalejin Hukumar EFCC Academy (ma’aikacin wucin-gadi), sannan a kuma a Ƙungiyar GIABA (cikakken ma’aikaci). Shi ƙwararre ne a fannin yaƙi da jabun magunguna a duniya. Ya sha wakiltar Najeriya da Ƙungiyar GIABA a manyan tarukan duniya, kamar taron Hukuma Mai Yaki da Muggan Ƙwayoyi ta Majalisar Ɗinkin Duniya a Vienna, tarukan Hukumar ‘Yan Sandan Ƙasa Da Ƙasa, tarukan Hukumar FATF da sauran su. A kwanan nan Shugaban Ƙungiyar ECOWAS ya naɗa shi muƙamin Muƙaddashin Sakatare.
_______________

Previous Post

Ministan Tsaro Janar Christopher Musa: Shawara Da Fatan Alheri

Next Post

NANA Rahma Abdulmajid Ta Bankaɗo Sharrin Hausawan Bogi

Related Posts

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza
Adabi

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

April 11, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)
Adabi

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
Let’s Speak Our Mother Tongue
Adabi

Mu Yi Kishi Da Alfahari Da Harshen Uwa

March 6, 2026
Next Post
NANA Rahma Abdulmajid Ta Bankaɗo Sharrin Hausawan Bogi

NANA Rahma Abdulmajid Ta Bankaɗo Sharrin Hausawan Bogi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

My Takeaways from IBB’s Autobiography

My Takeaways from IBB’s Autobiography

March 18, 2025
An Karrama Ɗanmadamin Yusufari Da Kambin Yabo Da Girmamawa

An Karrama Ɗanmadamin Yusufari Da Kambin Yabo Da Girmamawa

November 13, 2023
TUNAWA DA JARUMI: Laftanar-Kanar Abu Ali

TUNAWA DA JARUMI: Laftanar-Kanar Abu Ali

November 7, 2023
Malam Nasir El-Rufa’i: Guga Sha Kwaramniya

Wa Ke Tsoron Malam Elrufa’i Ya Zama Minista?

August 9, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Duniya Ba Gidan Zama Ba
  • Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi
  • Governor Dikko Radda Commissions Community Development Projects Built by Muntari Sagir in Malumfashi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

April 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.