KAMUN LUDAYIN JEMAGE (26-08-2023 da 02-09-2023)
~~~~~~~
Shanshani ya waiga ya ɗauko kuttun waya, ya ƙwala wa Malam Na Fagge waya. “Shin wannan makon, me ake ciki ne?” Ga abin da yake cewa:
~~~~~~~
GAJEREN LABARI: Wannan makon muna neman afuwar masu karatu, sakamakon lamura, ba za mu samu kawo tattaunawa tsuntsaye ba. Sai dai ga wani gajeren labari da zai nishaɗantar da ku:
Baƙin A Daidaita Sahu
Lokacin da hare-haren Boko Haram suka yi ƙamari a Kano, har ta kai gwamnati ta yi umarnin hana Acaɓa da goyo a mashin; wannan mataki ya cille mutane da dama cikin matsi. Sai dai ba yadda za a yi, don zaman lafiya aka ce ya fi zama ɗan sarki.
Wannan doka ta shafe ni, da ni da wasu ‘yan uwana biyu ƙwarai da gaske. Rayuwarmu ta takura ƙwarai, duk da dai mu dai ba Acaɓa muke ba amma dokar ta hana mu zirga-zirga a cikin gari.
Daga ƙarshe sai muka yi mitin mu uku, muka yanke shawarar mu sayi A Daidaita Sahu kawai. Kamar wasa, muka je inda ake sayar da gwanjo.
Aka nuna mana wani, aka ce gangariya ne. Aka ce Naira dubu 280. Muka lale kuɗi muka ba da. Aka ba mu takarda. Ba mu wuce ko’ina ba sai wajen mai fenti. Muka ce a yi mana baƙin fenti, don ya bambanta da na haya.
A haka muka dinga zirga-zirga mu cikin kwanciyar hankali. Duk inda za mu sai dai kawai mu buga shi mu je.
An ce daɗi bai fiye ɗorewa ba. Ai kuwa ba a yi mako biyu ba, sai A Daidaita Sahunnan ya fara ba mu matsala. Yau makanike ya ce matsalar filogi ce, gobe sai a ce ta wayarin ce. Mashin dai ya sako mu gaba, duk kuɗin da muka samu sai ya ƙare a wajen mashin ɗin nan. In muka yi wa makanikenmu ƙorafi, sai ya ce “mashin ɗin ku lafiyarsa lau, kawai ‘yan ƙananan gyare-gyare ya ke buƙata.”
Ko kuma ya ce “mashin ɗin ku mai kyau ne, kawai ɗan huƙuri za ku yi zai goge.”
Da dai muka ga mashin na shirin tatike mu, sai muka yi shawarar mu sayar da shi kawai mu huta. Muka koma inda muka saya da fari. Daga ganin mu, masu saye suka taso, suka bincika mashin. Daga ƙarshe suka ce sun saya kan Naira dubu 75. Sai muka ga ai rainin hankalin ya yi yawa. Ƙaƙa mashin ɗin da muka saya Naira dubu 280, ɗari biyu da tamanin, ko wata biyu ba a yi ba, a ce wai Naira dubu 75!
Ko tsayawa shawara ba mu yi ba, muka ja mashin. Hanyar komawa gida, muka haɗu da sojoji a “check point” suka tsayar da mu, amma ina… sai mashin ya ƙi tsayawa!
Sojoji da suka ga mashin ya yi kansu da gudu, duk sai suka kauce! Ba su ko biyo mu ba, don lokacin kowa a tsoroce yake! Ranar na zaci mutuwa ce ta zo!
Ganin dai mun auna arziƙi, ya sa muka ɗau alwashin gobe mu amshi kuɗin mashin ɗin nan kawai. Kashegari muka koma inda ake sayar da mashin. Muka ce a ba mu Naira dubu 75 ɗin nan. Ai ko sai suka ce cinikin jiya ya tashi, yau sabo za a yi. Suka ƙara bincika mashin, suka ce sun saya Naira dubu 35!
Cikin fushi muka ja mashin. Ahanya ya mutu, muka ba da ajiyar sa, muka tafi gida.
Bayan na dawo, ina tsaye a ƙofar gida, sai ga wasu mutane biyu sun matso kusa da ni. Su ka yi mani sallama na amsa. Ɗaya daga cikinsu ya ce “mun ji an ce za ku sayar da A Daidaita Sahunku.” Na ce “eh, haka ne!”
Ɗayan ya ce “muna so mu ci arziƙi, don Allah a sayar mana.”
Na ce “mashin ɗin nan yana da matsala.” Suka ce su sun ji kuma sun gani. Suka kawo Naira dubu 65, suka ba ni. Na ce su tsaya, bari in je in taho masu da shi. Na je inda muka ba da ajiya, da ƙyar mashin ɗin nan ya tashi.
Ina zuwa inda suke, ban ko kashe shi ba, na ce su hau su tafi, don ina tsoron kar in kashe shi ya ƙi tashi, a warware ciniki. Ni kuwa ga shi har na kasafta Naira dubu 65 ɗin su a zuciyata. Suka hau, ɗayan har da cewa, “mashin ɗin nan kawai fenti za mu canza, mu fara haya da shi.”
Ban bar wajen ba sai da na ga sun sha kwana. Na juya zan shiga gida ke nan, sai na ga ɗaya daga cikin mutanen ya shawo kwana a guje. Gabana ya faɗi ras! A zuciyata na ce “shi ke nan sun fasa!” Ai kuwa mutumin nan yana zuwa sai ya ce mun: “Takardar mashin ɗin nan za ka ba mu.”
A guje na shiga gida na ɗauko na ba shi. Ya kuwa ƙara juyawa a guje. Na yi wata ajiyar zuciya, don na san mun rabu da ƙaya!
~~~~~~~
Shanshani ya sake waiwayar Malam Na Fagge a yau Asabar (02-09-2023), domin jin inda aka kwana da batun shaguɓen Kamun Ludayin Jemage. Ga ɗan abin da ya aiko, yana cewa:
~~~~~~~
Alhudahuda ya kalli tsuntsaye ya ce: “A daidai lokacin da mu tsuntsaye mabiya a wannan nahiyar ke jin tsoron yunwa da talauci, to su ma shugabannin tsuntsaye nahiyar nan yanzu hankalinsu a tashe yake, don tsoron rasa mulkinsu.
“Nasihata ga tsuntsaye duka ita ce, kowa ya ji tsoron Allah! Yau ba za mu tsawaita hira ba, kowa ya nufi sheƙarsa ya ji tsoron Allah!”
Tsuntsaye kowa ya miƙe ya nufi sheƙarsa, sai dai an jiyo tsuntsaye suna ta yin Allah Ya isa bisa almundahanar shuka bishiyoyi da aka yi, lokacin mulkin Babba-da-Jaka.
~~~~~~~
Malam Mukhtar Mudi Sipikin, marubuci, sha’iri, ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa; yana aiko rubutunsa daga Kano.
~~~~~~~













