Ana Tuhumar Sanata Da Yi Wa Wata Yarinya Fyaɗe
Daga Wakilinmu

•••••••
A yanzu haka wani Sanata yana hannun ‘yan sanda bayan ya miƙa kansa ga Sashen Binciken Manyan Laifuka na Ƙasa (FCID) a Abuja kan zargin cewa ya yi wa wata ɗaliba ‘yar shekara 13 fyaɗe, kamar yadda jaridar intanet ta Podium Reporters ta ruwaito.
Iyayen yarinyar ne suka yi zargin cewa tsohon Sanatan Adamawa ta Arewa, Sanata Elisha Abbo, ya yi wa ɗiyarsu fyaɗe a ranar 29 ga Yuni, 2025, a gidansa da ke Katampe, Abuja. Sun kuma yi iƙirarin cewa ya yi ƙoƙarin rufe batun ta hanyar ba wa mahaifin yarinyar kuɗi.
Haka kuma, iyayen yarinyar sun zargi Sanata A’ishatu Ɗahiru Ahmed, wadda aka fi sani da Binani, da ziyartar su domin ta lallashe su, domin shawo kansu, domin hana su ci gaba da fitar da bayanin a bainar jama’a.
Majiyoyin ‘yan sanda sun tabbatar da cewa ana ci gaba da binciken Sanata Abbo, inda masu bincike ke ci gaba da yi masa tambayoyi. Wani babban jami’i (an sakaya sunansa) ya ce lamarin fyaɗe babban laifi ne da ake ɗauka da muhimmanci kuma “ba za a bar komai ba a ƙasa.”
Wannan tuhuma, ba ita ce karon farko a kan Abbo ba. A shekarar 2019, a samu wani faifan bidiyo da ya bazu a Soshalmidiya, wanda ke nuna yadda ya mari wata mai tsaron shagon sayar da kayayyaki na zamani, a Abuja. A wancan lokaci, lamarin ya ɗauki hankalin jama’a a faɗin ƙasa, kasancewar wanda ake tuhumar yana kan kujerarsa ta Sanata. Haka kuma a baya-bayan nan ma, an zarge shi da ƙoƙarin yi wa wata matar aure shan kai (kamuwa) da wani faifan bidiyon baɗala, lamarin da har ya kai aka tattauna shi a shirin Brekete Family na gidan rediyon Human Rights Radio da ke Abuja.
Wannan sabuwar tuhuma ta sake tayar da hankalin jama’a da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam da na mata, waɗanda suke kira ga hukumomi su tabbatar da adalci. Ƙungiyar Child Protection Network a Legas, ta bayyana lamarin da cewa “ƙalubale ne ga tsarin shari’ar laifuka na Najeriya,” tana mai kira ga jami’an tsaro da su guji yin wasa da lamarin kuma kada su yi ƙasa a gwiwa ko kuma kada su saurari matsin lamba daga ‘yan siyasa.
Abbo, wanda ya rasa kujerarsa ta Sanata, a sakamakon wani hukuncin da kotu ta yanke a 2023, sunansa ya ci gaba da bayyana a kafafen watsa labarai saboda rigingimu.
Ya zuwa wallafa wannan rahoto, Sanata Abbo ko tawagar lauyoyinsa ba su fitar da wata sanarwa ba kuma an kasa samun wani bayani daga ɓangarensa.
_______________













