• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, January 22, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Shanshani

Wa Ke Tsoron Malam Elrufa’i Ya Zama Minista?

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
August 9, 2023
in Shanshani
0
Malam Nasir El-Rufa’i: Guga Sha Kwaramniya

Malam Nasir El-Rufa'i

352
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Wa Ke Tsoron Malam Elrufa’i Ya Zama Minista?

Malam SHANSHANI, wai shin don Allah wane ne ke jin tsoron ganin Malam Nasiru Elrufa’i ya zama Minista a Gwamnatin Tinubu?

Related posts

SABON ZUMUNCI: KWANKWASO DA GANDUJE SUN YI SULHU

SABON ZUMUNCI: KWANKWASO DA GANDUJE SUN YI SULHU

December 22, 2023
KAMUN LUDAYIN JEMAGE

KAMUN LUDAYIN JEMAGE (26-08-2023 da 02-09-2023)

September 2, 2023

Wannan tambaya ce wani ya yi inda ni kuma ba tare da ɓata lokaci ba, na shiga nazari, na tanadar masa da waɗannan bayanan a matsayin amsa:

Na farko dai, manyan waɗanda ke tsoron ya zama Minista, su ne Manyan Dillalan Makamashi, waɗanda suka haɗa har da wasu attajirai da ke mallakar kamfanonin raba wutar lantarki a Najeriya.

Babban abin da waɗannan mutane suke tsoro shi ne, suna da kyakkyawan zaton za a ba shi Ma’aikatar Makamashi ne. Kuma suna sane da irin himmarsa da jajircewarsa a duk inda ya samu kansa. Don haka idan ya zama Minista a wannan ma’aikata, zai kawo masu cikas. Zai tabbatar da cewa an yi duk abin da ya dace wajen daƙile cuwacuwar da ake yi a samar da lantarki a ƙasar nan. Zai tabbatar da cewa lallai duk wani mai kawo matsala a wadata lantarki a ƙasar nan, an yi maganinsa. Wannan shi ne dalilin tsoron nasu kuna dalili ke nan suke ta haƙilon ganin Majalisar Dattijai ba ta wanke shi ba

Rukuni na biyu da suke adawa da Malam Elrufa’i, su ne wasu ‘yan siyasa da suke ganin zai hana su rawar gaban hantsi a Gwamnatin Tinubu, musamman ma suna ganin yana da tasiri a wasu jihohin Arewa.

A kan haka, wasu ‘yan siyasa a Jihohin Kaduna da Kano, ba su son ganin Malam Elrufa’i ya zama Minista. Misali a Kano, an san cewa yana da alaka da fahimta tsakaninsa da Gwamna Abba Kabir Yusuf. Haka kuma an san irin zumunci da amanar da ke tsakaninsa da Sarkin Kano (murabus), Malam Muhammadu Sanusi II.

Waɗannan mutane suna tsoron idan Elrufa’i ya zama Minista, komai na iya faruwa a siyasance a Kano. Kuma suna tsoron zai iya taka rawa wajen ganin an mayar da aminin nasa a gadon Sarautar Kano.

Wasu mutane kuma da suke adawa da Malam Elrufa’i, su ne ‘yan Shi’a, waɗanda suke ƙullace da shi saboda rawar da ya taka wajen korar Malam Elzakzaky daga Zaria.

‘Yan Shi’a ba za su riƙe hannu su ga Malam Nasiru ya samu nasarar zama Minista ba. Dalili ke nan ma lokacin da aka ambata sunansa, suka shirya zanga-zangar nuna rashin amincewa da shi, suka je har kofar Majalisar Tarayya, ɗauke da kwalayen da ke ɗauke da rubuce-rubucen adawa.

Wasu kuma da ke adawa da Malam Elrufa’i kuma suke tsoron ganin ya zama Minista, su ne wasu “cabal” na tsohuwar Gwamnatin Muhammadu Buhari.

Irin waɗannan mutanen, suna tsoron kada Elrufa’i ya zama Minista, domin zai iya rikita masu lissafinsu na siyasa, musamman a Arewa, a zaɓe na gaba.

Ana zargin cewa, irin waɗannan rukunnan mutane ne suke ta haƙilo da faɗi-tashi, suke bin hanyoyin daƙile aniyar Malam Nasiru ta zama Minista. Su ne suke bin kwanoni a Majalisar Tarayya, suke ɗaukar nauyin rubuce-rubucen ɓatanci a kafafen watsa labarai, domin cin ma manufarsu.

Abin jira a gani shi ne, shin za su yi nasara? Shin Shugaba Tinubu zai jefar da Elrufa’i haka, duk da cewa shi ba ƙashin yadawa ba ne? Kowa dai ya san irin gwagwarmayar da ya sha wajen ganin Shugaba Tinubu ya yi nasara.

Previous Post

SHIRIN FIM: Furodusa Nafseen Ya Shirya Taron Fitattun ‘Yan Wasa

Next Post

Shugabanci A Aikace: Gwamna Raɗɗa Ya Jagoranci Jami’an Tsaro Wajen Farautar ‘Yan Ta’adda

Related Posts

SABON ZUMUNCI: KWANKWASO DA GANDUJE SUN YI SULHU
Shanshani

SABON ZUMUNCI: KWANKWASO DA GANDUJE SUN YI SULHU

December 22, 2023
KAMUN LUDAYIN JEMAGE
Shanshani

KAMUN LUDAYIN JEMAGE (26-08-2023 da 02-09-2023)

September 2, 2023
KAMUN LUDAYIN JEMAGE
Shanshani

KAMUN LADUYIN JEMAGE (19-08-2023)

August 20, 2023
Next Post
Shugabanci A Aikace: Gwamna Raɗɗa Ya Jagoranci Jami’an Tsaro Wajen Farautar ‘Yan Ta’adda

Shugabanci A Aikace: Gwamna Raɗɗa Ya Jagoranci Jami'an Tsaro Wajen Farautar 'Yan Ta'adda

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

AREWA (A Poem)

AREWA (A Poem)

August 19, 2024
TARON JIGAJIGAN KATSINA ALHERI NE

TARON JIGAJIGAN KATSINA ALHERI NE

September 16, 2025
Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina

Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina

October 22, 2025
Rasuwar ‘Yar Kannywood Jidda Fulani: Ko Furodusa Aminu Saira Ya Kyauta?

Rasuwar ‘Yar Kannywood Jidda Fulani: Ko Furodusa Aminu Saira Ya Kyauta?

December 27, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)
  • Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya
  • Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut’a

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

January 21, 2026
My 83rd Birthday and the Kindred Spirit

Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya

January 19, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.