• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, January 16, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

BAKIN JAƁA (3)

Labarin Cin Amana

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
September 9, 2025
in Adabi
0
BAKIN JAƁA (3)

Bakin Jaɓa (3)

44
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

BAKIN JAƁA (3)
(Labarin Cin Amana)

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

December 23, 2025
Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine

Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine

December 6, 2025
Bakin Jaɓa (3)

 

                     _______________
Lokacin da auren iyayenta ya rabu, Jummalo sai ta ci gaba da zama a gidan kakarta, wacce dama tun farko ita ce ta shagwaɓa ta fiye da mahaifiyarta. A irin wannan rayuwa ta shagwaɓa da tarairaya da rashin kwaɓa ta samu kanta har ta kai ga kammala sakandare. Dama can mahaifinta ne yake ƙoƙarin saita mata tarbiyya, amma tun da ta samu kanta a ƙarƙashin kulawar uwa da kaka, shi ke nan sai yaƙin ruwa ya iske sakaina. Kamar yadda masu hikimar magana suka ce, sai yi, wai gwauro ya yi toshi.

Rayuwarta a makaranta sai ta ɗauki sabon salo. Maimakon a can baya da ta kasance yarinya mai hazaƙa da saurin ɗaukar karatu, sai ta koma in ban da sharholiya babu abin da ta sanya gaba. Ba ta kula da karatu kuma a mafi yawan lokuta, a makare take shiga makaranta. Wasu ranakun ma da gangan sai ta ƙi zuwa kuma babu mai tambayar ta bahasi. Iyaka idan kakar ko mahaifiyar ta tambaye ta, sai ta ce ba ta lafiya ko kuma ta samu wata gurguwar ƙarya ta faɗa masu. Kuma shi ke nan ruwa ta sha.

Batun makarantar islamiyya kuwa, tuni ta daina zuwa gaba ɗaya. Tun da suka baro gidan mahaifinta, ƙafarta ba ta ƙara taka islamiyya ba. Ɗan karatun da ta samu na baya, da shi take yin salla, kodayake ba kasafai ma take ba da farali ba. Takan yi wa khamsussalawati shan ruwan tsuntsaye. Wani lokaci ta yi Sallar Asuba, ta ƙetare sauran, sai da dare ta yi Isha’i. Wasu lokutan ma ba ta yi gaba ɗaya kuma babu mai cewa tashi ki yi.

Maganar ragaita da raƙashewa kuwa wurin Jummalo ‘Yarkaka, sai in ba ka yi. A duk ƙarshen mako ba ta kwana gida. Idan ranar Asabar ba ta je fati ba, to tana can gidan saurayinta – wani matashi ɗan ajinsu, wanda shi ma iyayensa suke matuƙar nuna wa gata. Mamman shi ne yake matuƙar mutuwar son ta. Tun suna aji biyu alaƙarsu ta soyayya ta ƙullu. Duk makarantar ma babu wanda bai san da wannan soyayya ba.

Shi Mamman, wanda ake wa laƙabi da Big Boy, mahaifinsa shi ne Ma’ajin ƙaramar hukuma. Yana nuna masa gata iya gata. Tun yana aji uku a sakandare ya fara saya masa babur roba-roba, irin na ‘yan ƙwalisa. Da shi yake zuwa makaranta, a yayin da akasarin ɗalibai suke zuwa a ƙasa ko kuma a keke.

A lokacin da ya shiga aji biyar, baban nasa sai ya saya masa mota. A cikinta ne ma, shi da abokansa suka taɓa maido da Jummalo gida a galabaice, lokacin da ta bugu da kayan maye a wajen fati. Haka kuma ya gina masa matsakaicin gida a ɓangare daban. Duk wata sharholiya da yake so, nan suke tattaruwa da abokansa su yi.

A haka Jummalo da saurayinta suka kammala sakandare. A ranar da suka yi fatin murnar kammala karatun ne wani abin tarihi ya faru a tsakaninsu. A daren wata Asabar ne Mamman da abokansa suka haɗa wannan fati. Daidai misalin ƙarfe ɗaya na dare, bayan sun yi rawa sun gaji liƙis, sai ya kama hannun Jummalo suka fito ƙofar gida suka zauna suna hira.

“Ni fa tun da mun gama makaranta, zuwa gobe zan kwaso kayana gaba ɗaya in tare gidanka.” Cikin wata murya ta shagwaɓa da nishin maye Jummalo take magana.

Mamman ya ƙyalkyace da dariya. “Haba my baby, ko dai kin fara hauka ne…?”

“Hauka kuma?” Ta tambaya cikin mamaki, a yayin da ta ɗago kai ta fuskance shi, fuska-cikin-fuska.

“To idan ba hauka ba, ina kika ga amarya ta tare tun kafin a ɗaura aure?”

“To ni ina ruwana da wani ɗaura aure, wane ne a duniyar nan bai san ni taka ba ce?” Bakinta a turɓune, ya yi zoɓoɓo ta faɗi haka.

Suna cikin wannan tattaunawa mai kama da shirme sai suka ji ana ihu tare da rusa kuka a cikin gida. Nan take suka bazama cikin gidan. Abokan Mamman ne biyu suka ruƙume faɗa da juna, a kan wata yarinya ɗaya, wacce suka yi tarayya a son ta. Kafin a kai ga raba su, ɗaya ya make ɗaya da wata kujerar ƙarfe. Nan take ya faɗi ƙasa sumamme. Dalili ke nan sauran samari da ‘yan matan suka shiga koke-koke.

A daren nan, haka mutanen unguwa suka yi tururuwa a ƙofar gidan. Da ƙyar aka samo rayuwar wannan saurayi. Sauran batu kuwa sai da safe aka ƙarƙare shi a wajen ‘yan sanda.

Da daɗi, ba daɗi, a haka aka tattara aka ɗaura auren Jummalo da masoyinta Mamman. An kuwa yi ƙasaitaccen biki na kece raini. Kuɗi kam sun yi kuka, domin makaɗa da mawaƙa sun kwashi rabonsu daga lalitar Ma’aji Baban Mamman da abokansa. Cikinsu har da Shugaban Ƙaramar Hukuma da sauran jigajigan jam’iyyarsu, wacce ke kan mulki. Wasu manyan baƙin ma, musamman Ma’aji-Ma’aji na ilahirin ƙananan hukumomin jihar sai da suka halarta. Kuma kowannensu ya baza iya ƙoƙarinsa na nuna kuɗi wajen bikin.

Amarya Jummalo da ƙawayenta, tsawon mako guda suka ɗauka suna raƙashewa. Cikin ƙawayen nata, har da fitattar ‘yar fim ɗin nan mai suna Kandala. Ita ce ma ta fi ɗaukar hankali a yayin bikin. Duk inda ta gitta, yara ne maza da mata ke biye da su, kamar ƙudaje a kwata.

(Za Mu Ci Gaba)
_______________

Previous Post

SHIRIN KATSINAWA DIKKO YA AIKO NI: Jan Hankali Da Ƙarin Haske Ga Umar Tata

Next Post

Ibtila’in Ambaliya Ya Cinye Mace Da Goyonta A Zariya

Related Posts

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)
Adabi

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

December 23, 2025
Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine
Adabi

Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine

December 6, 2025
Yau Take Juma’a: Allah Ka Albarkace Mu
Adabi

Yau Take Juma’a: Allah Ka Albarkace Mu

December 5, 2025
Next Post
Ibtila’in Ambaliya Ya Cinye Mace Da Goyonta A Zariya

Ibtila'in Ambaliya Ya Cinye Mace Da Goyonta A Zariya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

YAU 40: ALLAH YA JI ƘAN HAJIYA ZAINAB AHMAD

YAU 40: ALLAH YA JI ƘAN HAJIYA ZAINAB AHMAD

June 26, 2024
KAMUN LUDAYIN JEMAGE

KAMUN LUDAYIN JEMAGE

July 16, 2023
A Harkar Rubutu: Na Fi Fuskantar Matsala Daga Mata – Uwa Idris

A Harkar Rubutu: Na Fi Fuskantar Matsala Daga Mata – Uwa Idris

July 4, 2023
RAYUWA (Sadaukarwa Ga Talakawan Najeriya)

RAYUWA (Sadaukarwa Ga Talakawan Najeriya)

September 5, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation
  • Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco
  • Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

January 15, 2026
Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

January 14, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.