• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Saturday, May 2, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Ibtila’in Ambaliya Ya Cinye Mace Da Goyonta A Zariya

BABBAN LABARI

Daga Wakilinmu by Daga Wakilinmu
September 10, 2025
in Babban Labari
0
Ibtila’in Ambaliya Ya Cinye Mace Da Goyonta A Zariya

Daga hagu: Fatima Sani, Haneefa da Yusuf Surajo, waɗanda suka rasa rayukansu a ibtila'in

21
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Ibtila’in Ambaliya Ya Cinye Mace Da Goyonta A Zariya

Daga Wakilinmu

Related posts

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

April 14, 2026
Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

April 8, 2026
An kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna ta gyaran hanyoyin ruwa a Zariya, domin magance ambaliya

 

______________

Aƙalla mutane biyu ne suka rasa rayukansu, a yayin da wasu biyun suka ɓace sakamakon ambaliya a garin Zariya, Jihar Kaduna, a ranar Litinin da ta gabata.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, lamarin ya faru ne a Unguwar Tudun Jukun, bayan saukar wani mamakon ruwan sama. An an gano gawar wata yarinya ’yar shekara 18, Fatima Sani Dan Marke, wacce ɗaliba ce a makarantar School of Basic and Remedial Studies, Funtua, da kuma wani ɗalibi, Yusuf Surajo da ake kira Abba, a gadar makarantar firamare ta Isan Nabawa a Tudun Wada, Zariya.

Marigayiya Fatima Sani

An gano gawar Surajo a ranar Litinin, sai dai ita Fatima, an samo tata a washegari Talata. Amma ƙanwar Fatima mai shekara uku, Haneefa, har yanzu ba a ganta ba. An yi jana’izarta da misalin ƙarfe 4:00 na yamma a juya Talata, a Tudun Jukun, Zariya.

Fatima ɗiyar Alhaji Sani Danmarke ce, wanda aka fi sani da ASD, babban ɗan kasuwa a harkar taki a PZ, Sabongari, Zariya. A lokacin faruwar lamarin, tana goye da ƙanwarta Haneefa mai shekara uku a bayanta. Sun fito ne daga gidan kakarsu da ke Magume zuwa gidansu a Tudun Jukun, inda tazarar ba ta da nisa sosai, ko a ƙafa za a iya takawa. Amma abin tsausayi, sai malaminsu na Islamiyya, Malam Daddy ya ɗauke su a kan babur ɗinsa da sunan rage hanya.

Marigayi Yusuf Surajo

Shaidun gani da ido sun ce ibtila’in ya auku ne a kusa da wani coci mai suna Nasara Baptist Church da ke kan titin Gaskiya a Tudun Jukun. Sun ce yayin da Malam Daddy ya tsira, ita Fatima da ƙanwarta Haneefa, ruwan ya tafi da su.

Wani shaidar gani da ido, Mustapha Badamasi Ɗanbakano, ya ce Fatima da ƙanwarta sun sauka daga babur ɗin ne a lokacin da babur ɗin malamin nasu ya bugi gaɓar kwalbati.

“Yarinyar ta yi saurin sauka daga babur, amma yayin da take ƙoƙarin ƙetare gabar kwalbatin sai ƙafarta ta zame ta faɗa cikin ruwa, tare da ƙanwarta da take goye a bayanta. Nan take ruwa ya kwashe su,” in ji shi. Ya ƙara da cewa wani mutum da ke tsaye a wajen, ya faɗa cikin ruwan da nufin don ceto su, shi ma kuma ya tafi da shi.

Marigayiya Haneefa

“Mutumin mazaunin Gidan Ɗangoma ne a Tudun Jukun, Zariya, kuma an yi masa jana’iza da safiyar yau bisa ga tsarin Musulunci,” in ji shi.

Malam Musa Umar Al-Mishawi, limamin da ya jagoranci jana’izar Yusuf Surajo a Kwarin Ɗangoma, Tudun Jukun, Zariya, ya tabbatar da cewa matashin ya samu rauni a goshinsa bayan ya bugi wani rodi da ke cikin ruwan.

Wurin da ibtila’in ya faru, a Unguwar Tudun Jukun ta Zariya, mahaɗar hanyar ruwa ce da ta taso daga Tukur Tukur zuwa Tudun Jukun, da kuma daga Magume zuwa Kwarin Ɗangoma, duk suna kusa da kogin Kubanni da aka sani tun da daɗewa yana cin rayuka. Sai dai wasu mazauna unguwar sun danganta wannan lamari na baya-bayan nan da ruwan sama mai tsanani yake mamaye magudanan ruwan.

Sun bayyana cewa daga Barewa Junction zuwa Gaskiya Corporation, an rufe magudanar amma daga can zuwa gadar kogin Kamacha, an bar ta buɗe. A wannan wurin ne aka samu wannan ibtila’i, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A cewar mazauna wurin, da a ce an rufe wannan ɓangare ma, da wataƙila an kauce wa ambaliyar kuma da lamarin bai faru ba. Sun yi kira ga hukumomi da su ɗauki matakin da ya dace, na kawo gyara domin dakatar da faruwar haka a gaba.

Previous Post

BAKIN JAƁA (3)

Next Post

Mummunar Zanza-Zanga A Ƙasar Nepal

Related Posts

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?
Babban Labari

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

April 14, 2026
Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume
Babban Labari

Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

April 8, 2026
Yadda Babban Jigon Jam’iyyar APC Daga Kano Ya Mutu A Otel
Babban Labari

Yadda Babban Jigon Jam’iyyar APC Daga Kano Ya Mutu A Otel

April 2, 2026
Next Post
Mummunar Zanza-Zanga A Ƙasar Nepal

Mummunar Zanza-Zanga A Ƙasar Nepal

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

YAMTARAWALA Ya Kama Hanyar Lashe Gasar Adabi Ta NLNG

YAMTARAWALA Ya Kama Hanyar Lashe Gasar Adabi Ta NLNG

August 31, 2023
BINCIKE:  Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

July 28, 2025
Yau Aka Ƙaddamar Da Dakarun Tsaron Al’ummar Jihar Katsina

Yau Aka Ƙaddamar Da Dakarun Tsaron Al’ummar Jihar Katsina

October 10, 2023
BIU: Ziyarar Babban Birni A Kan Tsauni (1)

BIU: Ziyarar Babban Birni A Kan Tsauni (1)

November 28, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana
  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (11)
  • General Buratai (A Poem)

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

April 28, 2026
Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (11)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (11)

April 27, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.