• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, January 22, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Tarihin Rayuwar Sabon Shugaban Rundunar Sojojin Ruwa Na Najeriya Rear Admiral Idi Abbas

BABBAN LABARI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
October 28, 2025
in Babban Labari
0
Tarihin Rayuwar Sabon Shugaban Rundunar Sojojin Ruwa Na Najeriya Rear Admiral Idi Abbas

Shugaban Rundunar Sojojin Ruwa Ta Najeriya, Rear Admiral Idi Abbas

45
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Tarihin Rayuwar Sabon Shugaban Rundunar Sojojin Ruwa Na Najeriya Rear Admiral Idi Abbas

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

January 14, 2026
Kishin Ilimi Ya Sa Ni Tallafa Wa Ɗalibai 110 A Malumfashi Da Ƙafur – Dokta Tukur Tingilin

Kishin Ilimi Ya Sa Ni Tallafa Wa Ɗalibai 110 A Malumfashi Da Ƙafur – Dokta Tukur Tingilin

January 4, 2026


                             •••••••

Rear Admiral Idi Abbas, sabon Babban Hafsan Rundunar Ruwa ta Najeriya, an haife shi a ranar 20 ga Satumba, 1969. Shi ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Nassarawa da ke Jihar Kano ne. Ya shiga Babbar Makarantar Tsaro ta Najeriya (NDA) a ranar 12 ga Satumba, 1987, inda aka ba shi matsayin Sub-Lieutenant a ranar 10 ga Satumba, 1993, a matsayin ɗan Ajin 40 na NDA, tare da samun digiri na farko a fannin Chemistry.

Ya fara karatunsa a Makarantar Firamare ta Gwagwarwa, Kano, daga nan kuma ya tafi Airforce Military School, Jos, daga 1981 zuwa 1986, kafin ya samu gurbin shiga NDA a 1987.

Rear Admiral Abbas ƙwararren jami’i ne a fannin Dubarar Yaƙin Bisa Ruwa (Above Water Warfare-AWW), kuma ya halarci darussa da dama na soja a gida da waje. Wasu daga cikinsu sun haɗa da Sub-Lieutenant Technical Course a NNS QUORRA (1994), Junior & Senior Staff Courses a Armed Forces Command and Staff College, Jaji (2001 da 2005). Daga Janairu zuwa Disamba, 2003, ya halarci Officers’ Long Course (OLC XII) a NNS QUORRA, Apapa, Lagos, inda ya ƙware a fannin AWW. Ya kuma halarci United Nations Military Observer Course a Tanzania (2009), sannan ya kammala karatu daga National Defence College (NDC), Abuja, a 2014 (Course 23).

A rayuwar aikinsa, Rear Admiral Abbas ya riƙe muhimman muƙamai da dama a Rundunar Sojojin Ruwa ta Najeriya. Bayan an naɗa shi jami’i a 1993, ya yi aiki a jiragen ruwa da dama kamar NNS ARADU, NNS DAMISA, da NNS AYAM, a matsayin Watch-Keeping Officer. A 1998, ya zama Naval Assistant ga mataimakin kwamandan Armed Forces Command and Staff College, Jaji. Daga 1999 zuwa 2002, ya halarci wasu muhimman kwasa-kwasan soja, sannan ya koma aiki a NNS DAMISA. A Janairu 2004, ya zama Staff Officer III, Marine Services a Naval Headquarters, kuma daga baya Gunnery Officer a NNS OHUE (2006). A 2007, ya zama malami a NNS QUORRA, sannan a 2008, aka naɗa shi Commanding Officer na Burma Battalion a NDA.

Daga nan, Rear Admiral Abbas ya zama Base Administrative Officer a NNS PATHFINDER, sannan Naval Contingent Commander na Joint Task Force Operation SAFE HAVEN a 2010 da 2012. A 2015, aka naɗa shi Maritime Guard Commander (MGC) a NIMASA, sannan a 2017 ya zama Commander Task Group (CTG) na aikin Operation TSARE-TEKU. Daga 2018 zuwa 2022, ya yi aiki a Central Naval Command a matsayin Command Administrative Officer (CAO) da kuma Chief Staff Officer (CSO), kafin daga bisani a naɗa shi Flag Officer Commanding (FOC) Central Naval Command. A wannan lokaci kuma, ya shugabanci NNS VICTORY a Calabar (2020). A Yuli 2023, ya zama Chief of Naval Safety and Standards (CNASS) a Naval Headquarters, sannan a Fabrairu 2024, aka naɗa shi Chief of Defence Civil-Military Relations (CDCMR) a Defence Headquarters. A Janairu 2025, aka tura shi Nigerian Army Heritage Centre a matsayin Senior Research Fellow, kafin daga bisani a naɗa shi Babban Hafsan Rundunar Ruwa na 25 (25th Chief of the Naval Staff).

Rear Admiral Abbas gogaggen jami’in ruwa ne, kuma ƙwararren Seaman Executive Officer. Ya hau matakan muƙamai kamar haka: Midshipman (18 Satumba 1992), Sub-Lieutenant (1993), Lieutenant (1996), Lieutenant Commander (2001), da Commander (2006). Ya zama Navy Captain a Satumba 2011, Commodore a 2016, sannan Rear Admiral a 10 Satumba 2020.

Saboda girmamawa ga aikin da ya yi wa ƙasa, Rear Admiral Idi Abbas ya samu lambobin yabo da dama, ciki har da Passed Staff Course (psc), Fellow Defence College (fdc), Forces Service Star (fss), Meritorious Service Star (mss), Distinguished Service Star (dss), Grand Service Star (gss), da Defence General Service Medal (DGSM). Har ila yau, memba ne na Nigerian Institute of Management (NIM) da International Institute of Professional Security (IIPS).

Baya ga rayuwar aikin soja, Rear Admiral Idi Abbas yana da sha’awar buga ƙwallon gora da tuƙa mota. Musulmi ne mai bin koyarwar addini sau da ƙafa. Yana da matar aure ɗaya, Hajiya Aisha Abbas kuma Allah Ya albarkace su da ’ya’ya maza biyu.

_______________

Previous Post

Marigayi Sarkin Labaran Daura: Tunawa Da Mutumin Kirki Mai Zumunci

Next Post

Happy Birthday Sir: A Tribute to Malam Labiru Musa Ƙafur

Related Posts

Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna
Babban Labari

Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

January 14, 2026
Kishin Ilimi Ya Sa Ni Tallafa Wa Ɗalibai 110 A Malumfashi Da Ƙafur – Dokta Tukur Tingilin
Babban Labari

Kishin Ilimi Ya Sa Ni Tallafa Wa Ɗalibai 110 A Malumfashi Da Ƙafur – Dokta Tukur Tingilin

January 4, 2026
Mawaƙi Kizz Daniel Ya Amshi Musulunci
Babban Labari

Mawaƙi Kizz Daniel Ya Amshi Musulunci

January 3, 2026
Next Post
Happy Birthday Sir: A Tribute to Malam Labiru Musa Ƙafur

Happy Birthday Sir: A Tribute to Malam Labiru Musa Ƙafur

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

MANYAN MATA: Fim Ɗin Da Ya Nazarto Matsalolin Rayuwar Malam Bahaushe

MANYAN MATA: Fim Ɗin Da Ya Nazarto Matsalolin Rayuwar Malam Bahaushe

June 24, 2024
TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNKASA MALUMFASHI DA KEWAYE (7)

TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNKASA MALUMFASHI DA KEWAYE (7)

August 25, 2025

Buratai Bags Another Doctorate Degree

November 25, 2023
No, Mr. President: An Open Letter to Donald J. Trump

No, Mr. President: An Open Letter to Donald J. Trump

November 1, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)
  • Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya
  • Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut’a

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

January 21, 2026
My 83rd Birthday and the Kindred Spirit

Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya

January 19, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.