• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, April 24, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

BAKIN JAƁA (1)

(Labarin Cin Amana)

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
August 30, 2025
in Adabi
1
BAKIN JAƁA (1)

Jummalo 'Yarkaka

84
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

BAKIN JAƁA (1)
(Labarin Cin Amana)

Daga Bashir Yahuza Malumfashi
_______________
Gabatarwa:
Wannan labari ne na gaskiya a haƙiƙa, wanda ya taɓa faruwa. Kodayake an sarrafa shi a siga ta daban da ainihin yadda ya faru. An jirkita sunayen waɗanda labarin ya faru da su, da sunayen garuruwa da wuraren da abin faru. Haka kuma an ƙara wasu abebaɗai, a matsayin gishirin da zai zaƙaƙa miyar labarin. Amma tabbas, akwai darussan rayuwa abin dubawa da yawa a labarin.
_______________

Related posts

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

April 11, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
Jummalo ‘Yarkaka

Jummalo ‘Yarkaka tana zaune a bakin gado, ta rungume kumatunta cikin tagumin takaici. Abin duniya ya gama dagule mata, ta rasa tudun dafawa. Caraf sai ta ɗauki wayarta samfurin Samsung, ta fara daddanawa.

“Kash! Ashe ma ba ni da Data.” Abin da ta faɗa ke nan bayan ta buga wani uban tsaki wanda ya yi kama da na wata gawurtattar tsaka. Nan da nan ta ƙara shiga cikin wani takaicin. Ƙwaƙwalwarta ta cunkushe da tunani, gami da zullumi iri-iri.

“Wohoho! Wannan wace irin rayuwa ce? Shin wane laifi na yi wa Allah da ya jarabce ni da waɗannan…”

‘Yarkaka, ba ta ida kammala jimlar ba sai ta ji saukar zazzafan hawaye a kumatunta. Kafin ta ankara, har ta fara kuka, gami da shessheka.

Cikin ƙanƙanen lokaci, ƙwaƙwalwarta ta shiga zarabtu da kai komo bisa abubuwan da suka yi ta faruwa da ita a rayuwa. Tunanin nata ya gawurta, inda ya riƙa shigar giza-gizai. Da zarar ta tuno da wannan abin takaici, sai zaren tunanin ya tsinke. Kafin daƙiƙa ɗaya, sai kuma wani sabon zaren takaicin ya sake saƙa kansa a zuciyarta. Ba za ta ida shi ba, sai kuma wani ya sake yin kutse.

Jidali noman Barka – da baya, da baya ya zoƙale. Wannan shi ne yanayin da ‘Yarkaka take ciki. Ba ita ta gushe ba cikin gogoriyon tunani, har sai da ta ɗauki kanta zuwa rayuwarta ta makarantar boko. Ta koma baya yadda ta yi auren fari, wanda dudu bai wuce wata biyar ba suka sallama wa juna da mijinta. Ta yi ninƙaya cikin nazarin yadda wannan aure nata ya samar mata da haihuwar yaro guda ɗaya tilo, da yadda ta sha wahalar rainonsa a gidan iyayenta.

Haka kuma ta ci gaba da zancen zucci, yadda ta ƙaƙara ta koma makaranta domin karatun gaba da sakandare . A nan ne tunani ya gitto da hoton yadda rayuwarta ta samu tagomashi a Kwalejin Ilimi ta Zariya. Ta tunano irin ƙawaye da abokai da ta yi mu’amalar ɗalibta da su.

Rayuwa tamkar hankaka ce, mai launukan fari da baki. A daidai lokacin da ‘Yarkaka take kan tunano rayuwar makaranta, sai kuma zaren tunanin ya katse, wani sabo ya tsiro. Ta hasko yadda ta yi kutse ta tsunduma cikin ƙungiyoyin masu harkar shirya finafinan Hausa. Nan ma ba ta gushe ba sai da ta ƙarƙare komai…

A haka kuma ta koma tunanin yadda ta samu kanta a duniyar zawarci. Irin yadda ta yi faɗi tashi da manema – na ƙarya da na gaskiya. Sannu a hankali har tunanin nata ya ƙaraso zuwa wannan yanayi da take ciki, inda sabon auren da ta yi ya mutu cikin ƙanƙanen lokaci.

“To, ni yanzu ta ina zan fara kuma ina na nufa? Na ƙarar da komai a wajen auren nan, wanda ya kawo ƙarshe cikin wata biyar. Na yi zaton miloniya na aura… ashe hangen dala na yi.”

“Ke Jummalo!” Mahaifiyarta ce ta ƙwala mata kira, a lokacin da ta ga yanayin da take ciki na hawaye tare da maganganun da suka yi kama da sambatu.

“Me ya faru da ke ne?” Mahaifiyar tata ta ci gaba da tambayar jin bahasi. “Kada fa ki je ki halaka kanki. Shin a kanki ne aka fara mutuwar aure? Wa ya gaya maki ƙarshen duniya ke nan?”

Jummalo saurarenta kawai take yi amma ta kasa furta komai. Ta dai ƙura wa mahaifiyarta hajar mujiya, a yayin da ƙwalla ke ta malala a kumatunta.

(Za mu ci gaba)
_______________

Previous Post

GASAR RUBUTUN HAUSA TA GIDAUNIYAR ZANNA/WALI (2025)

Next Post

Dr. Bukar Usman, Emir of Daura, and the 2025 World Hausa Day Celebration

Related Posts

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza
Adabi

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

April 11, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)
Adabi

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
Let’s Speak Our Mother Tongue
Adabi

Mu Yi Kishi Da Alfahari Da Harshen Uwa

March 6, 2026
Next Post
Dr. Bukar Usman, Emir of Daura, and the 2025 World Hausa Day Celebration

Dr. Bukar Usman, Emir of Daura, and the 2025 World Hausa Day Celebration

Comments 1

  1. Maryam sani lawan says:
    8 months ago

    😂

    Reply

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Rebooting Nigeria: Nigeria 2.0 Under Review

Rebooting Nigeria: Nigeria 2.0 Under Review

September 21, 2023
Za Mu Inganta Rayuwa Da Ayyukan ‘Yan Jarida – Minista Idris

Shugaba Tinubu Ya Naɗa Sababbin Shugabannin Hukumomin Yaɗa Labarai

October 21, 2023
Tarihin Ƙungiyar Hamas

Tarihin Ƙungiyar Hamas

October 13, 2023
Ni Bazawara Ce: To Kuma Sai Me?

Ni Bazawara Ce: To Kuma Sai Me?

September 14, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Duniya Ba Gidan Zama Ba
  • Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi
  • Governor Dikko Radda Commissions Community Development Projects Built by Muntari Sagir in Malumfashi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

April 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.