• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, May 11, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

Matsalar Tsaro A Najeriya: Madalla Da Majalisar Dokokin Amurka

TSOKACINMU NA MAKO

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
November 26, 2025
in Gizago
0
Matsalar Tsaro A Najeriya: Madalla Da Majalisar Dokokin Amurka

Zauren Majalisar Dokokin Amurka, yayin tattauna matsalar tsaron Najeriya

41
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Matsalar Tsaro A Najeriya: Madalla Da Majalisar Dokokin Amurka

Daga Dr. Adam Abaji

Related posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
Zauren Majalisar Dokokin Amurka, yayin tattauna matsalar tsaron Najeriya


                             •••••••
Yau zaman jin bahasin Majalisar Dokoki ta Amurka (Congressional Hearing) da aka gudanar a Washington DC ya zama wani muhimmin lamari a tattaunawar duniya game da matsalar tsaro a Najeriya.

A karon farko, bayan ɗaukar tsawon lokaci ana kai-komo da wannnan batu, a yau mun shaida tattaunawa mai ma’ana, wacce ta dogara da hujjoji, a gaban Majalisar Dokoki ta Amurka. Mambobi daga manyan jam’iyyu biyu sun yi tattaunawa mai zafi da kuma nuna damuwa kan halin da Najeriya take ciki, dangane da taɓarɓarewar al’amuran tsaro. Sun amince da cewa, akwai tsananin ta’addanci da kuma irin raɗaɗin da ’yan Najeriya ke sha a sassa daban-daban na ƙasar. Haka kuma sun fahimci yadda lamarin ya rikice, kamar yadda suka fahimci cewa akwai buƙatar taka-tsan-tsan dangane da irin matakan da ƙasashen waje za su iya ɗauka da sakamakon da hakan zai iya haifarwa.

Abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne, yadda suka ƙi amincewa da duk wani yunƙurin kai tsaye na tura sojojin ƙasashen waje zuwa Najeriya. Maimakon haka, sun buƙaci a samar da haɗin kai mai ma’ana, cikin fahimta da ƙwarewa, tsakanin Gwamnatin Najeriya da ta Amurka. Sun ba da shawarar a yi haɗin gwiwa wajen tantance ƙarfin Najeriya a yaƙi da ta’addanci a halin yanzu. Sun ƙarfafi gwiwar Amurka da cewa ta taimaka ta ɓangaren samar da bayanan sirri (intelligence) tare da aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin tsaron Najeriya, wajen bincikowa, tantancewa, kamawa ko kawar da ƙungiyoyin ta’addanci da ke haddasa ɓarna a sassan ƙasar.

Wannan ya haɗa da hare-haren ‘yan Boko Haram a Arewa maso Gabas da ayyukan ’yan bindiga a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya. Haka kuma da ƙungiyoyi masu tada hankali a Kudu maso Gabas da Kudu maso Yamma. Majalisar ta amince da bayanin da ke cewa, ’yan Najeriya ne gaba ɗaya suke shan wahala dangane da lamuran rashin tsaro, ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba. Kuma kowane ɗan Najeriya na da haƙƙin samun tsaro da mutunci.

Wannan sabon salo abin maraba ne matuƙa. Ya fi tsari, ya fi samar da natsuwa fiye da kiraye-kirayen baya da aka yi, na cewa a kai farmaki Najeriya. Wannan rashin tunani ne mai zurfi, domin hakan zai keta ’yancinmu na ‘yan ƙasa, sannan ya jefa rayukan fararen hula cikin haɗari. Yau mun ga wata hanya mai hikima, wadda ke mutunta Najeriya kuma take mai da hankali kan abin da ya fi dacewa. Wannan nasara ce ga diflomasiyya da duk waɗanda suka yi amanna da cewa haɗin kai mai kyau tsakanin ƙasashe ya fi tsoma bakin soji, wanda zai lalata lamurra.

Ya zama wajibi ga Gwamnatin Tinubu ta yi amfani da wannan dama. Ya kamata Najeriya ta hanzarta ƙarfafa haɗin gwiwa da Amurka da kuma ƙasashen Turai. Haka kuma dole mu fahimci wani saƙo mai muhimmanci da ya fito daga zaman Majalisar Dokokin Amurka na yau. Wannan kuwa ya haɗa da buƙatar da ke akwai ga Najeriya da ta yi gaggawar tura jakadu a muhimman ƙasashen waje. Mu gane cewa mutuncin Najeriya ya zube a idon duniya, sakamakon yaɗa bayanan ƙarya da yaudara. Muna buƙatar jakadu ƙwararru da za su tsaya tsayin daka, su kare muradunmu tare da hulɗa da shugabannin duniya, domin dawo da martabar ƙasarmu.

Haka kuma, lallai ne mu fahimta da cewa, wannan ba lokacin ba da muƙamai saboda alfarma ba ne. Lokaci ne na zaɓen mutanen da suka cancanta, mutanen da za su wakilci Najeriya cikin daraja, su yi aiki ba gajiyawa don ganin an samar da makoma mai kyau, wadda za ta samar mana da tsaro da wadata ga ’yan Najeriya duka.

Ga wasu ‘yan Najeriya da ke gida, waɗanda suka riƙa yin murna da yiwuwar a kai harin soja ga ƙasarsu, ina roƙon ku da ku sake tunani sosai. Za ku iya jin haushi ko takaici amma yana da muhimmanci ku tsaya ku yi nazari cikin nutsuwa. Irin wannan agaji na harin soja daga Amurka ko wata babbar ƙasa, ba zai gyara Najeriya ba. Harin zai halaka rayuka, ya ƙara taɓarɓara halin da muke ciki. Wannan lokaci wata dama ce ta daban, domin haɗin gwiwa da manyan ƙasashe, su samar da goyon baya da bayanan sirri da za su kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a ko’ina cikin Najeriya.

Idan muka yi amfani da wannan dama da muhimmanci kuma muka yi aiki da abokan hulɗa masu dacewa, wannan na iya share mana hanyar magance matsalolinmu. Wannan ne lokacin da Najeriya za ta tashi da mutunci, ƙarfi da haɗin kai. Lokacin da gwamnati za ta samu goyon baya wajen kare ’yan ƙasa da kiyaye ’yancin ƙasarmu. Lokaci ne da Najeriya za ta fara hikimar ɗagawa sama, maimakon a bar ta a ƙuryar baya

._______________

Dr. Adam Abaji, babban malami ne a Jami’ar Alberta, Canada (Wannan tsokaci, asalinsa da Ingilishi ne, muka fassara zuwa Hausa).

Previous Post

Ɗaliban Kebbi Sun Shaƙi Iskar ‘Yanci

Next Post

SHEIKH ƊAHIRU USMAN BAUCHI: Babban Bangon Musulunci Ya Faɗi

Related Posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi
Gizago

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
Gizago

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista
Gizago

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
Next Post
SHEIKH ƊAHIRU USMAN BAUCHI: Babban Bangon Musulunci Ya Faɗi

SHEIKH ƊAHIRU USMAN BAUCHI: Babban Bangon Musulunci Ya Faɗi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Gargaɗin Amurka kan Nijeriya na tada hankulan jama’a, kuma ya na yin illa ga tattalin arzikin ƙasa – Minista

‘Yan Nijeriya za su fara bin diddigin ayyukan da Gwamnatin Tarayya ke aiwatarwa – Minista

November 8, 2023
RAMADAN KARIM: 22-1447

RAMADAN KARIM: 22-1447

March 11, 2026
Zaɓen gwamna: Mutum 2,318,919 za su yi zaɓe a Imo, 1,833,160 a Kogi, 1,017,613 a Bayelsa, inji INEC

INEC Za Ta Gudanar Da Zaɓuɓɓukan Da Kotu Ta Soke Da Na Cike Gurabu 34 A Fabrairu 2024 – Yakubu

December 20, 2023
TABBAS SHEIKH ABDUL’AZIZ DUTESEN TANSHI BAI “MUTU” BA

TABBAS SHEIKH ABDUL’AZIZ DUTESEN TANSHI BAI “MUTU” BA

April 5, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi
  • Yan ta’addan Daji Kafirai Ne – Sarkin Musulmi
  • Farewell Ashaka

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi

Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi

May 9, 2026
Yan ta’addan Daji Kafirai Ne  – Sarkin Musulmi

Yan ta’addan Daji Kafirai Ne – Sarkin Musulmi

May 8, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.