• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, January 22, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

TAƁARƁAREWAR TSARO A AREWA: BUƊAƊƊIYAR WASIƘA ZUWA GA MALAM NUHU RIBADU

BUƊAƊƊIYAR WASIƘA

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
August 8, 2025
in Gizago
0
INSECURITY IN NORTHERN NIGERIA: AN OPEN LETTER TO NSA NUHU RIBADU

Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Ta Fuskar Tsaro, Malam Nuhu Ribadu

4
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

TAƁARƁAREWAR TSARO A AREWA: BUƊAƊƊIYAR WASIƘA ZUWA GA MALAM NUHU RIBADU

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

My 83rd Birthday and the Kindred Spirit

Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya

January 19, 2026
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (9)

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (9)

January 17, 2026

Zuwa ga Mai Girma Malam Nuhu Ribadu, Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro (NSA), Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja.

Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Ta Fuskar Tsaro, Malam Nuhu Ribadu

Yallaɓai Malam Nuhu Ribadu, Ina rubuto maka wannan buɗaɗɗiyar wasiƙa ce ba domin rashin kunya ko tozarci ba, amma saboda girman matsalolin da ke uzura wa zuciyata, tare da damuwa, damuwa game da yankinmu na Arewa, damuwa game da ƙasarmu, da damuwa game da kai kanka da mutuncinka da tarihin da kake ta ginawa a rayuwarka. Wannan wasiƙa ita ce ta uku da nake rubutowa, domin tunatar da kai irin ƙimarka da martabarka a jiya, da yadda kake a yanzu, da kuma irin tarihin da al’umma ke tsammanin za ka bari domin gobe.

Bari Mu Waiwayi Tarihi: Malam Ribadu, muna nan muna tuna yadda ka jagoranci Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), a lokacin da Najeriya ke cikin duhu. Ka kasance tamkar zaki mai gurnani, mai fatattakar azzaluman ‘yan siyasa da suka ƙazanta ƙasa da almundahana, cin hanci da rashawa. Ka fuskanci azzalumai kai tsaye, ka tona asirin muggan masu mulki da ‘yan siyasa, gurɓatattun jami’an tsaro da maha’intan ‘yan kasuwa (wasu ma ka yi nasarar hukunta su a shari’a). Ka samu goyon baya da amsuwa daga talakawa, kamar kuma yadda ka samu suna da girmamawa daga manya da ƙananan ƙasashen waje.

Ɗan Adam tara yake, bai cika goma ba. Kai ma mai kasawa ne, amma jarumtakarka ta zamo haske ga miliyoyin mutane. Sai dai kuma kash! Yanzu wannan haske na ƙwazonka da aka sani a baya, yana dusashewa — ba saboda gazawar kai karan kanka ba, amma saboda muna jin tsoron cewa yanzu kana shayin ɗaukar matakan da suka dace, kana dusashe murya a inda ake buƙatar jin gurnanin muryar taka. Wannan kuwa yana faruwa ne, saboda wasu daga cikin ‘yan siyasar da ka taɓa yaƙi da su, har ka taɓa gurfanar da su a kotu, yanzu sun zamo abokanka a cikin gwamnati.

Al’amuran Tsaro Sun Taɓarɓare, Ana Zubar da Jini — Arewa Na Cikin Ƙunci: Yau da kullum rashin tsaro ya mamaye Arewacin Najeriya. ‘Yan bindiga suna kashe mutane, suna sace su, suna karɓar kuɗin fansa da ƙarfi da yaji. Ana tagayyara iyalai a Katsina da Zamfara da Neja da sauran jihohi. Dubban al’umma sun koma ‘yan gudun hijira a cikin ƙasarsu. Ana sace yara a makarantu. Ana kashe manoma a gonakinsu. ‘Yan ta’adda suna ƙaƙaba wa ƙauyuka haraji. Al’umma suna kwana cikin fargaba, kullum suna cikin zullumin abin da ka je ya zo gobe – na firgici da tashin hankali!

Ya mai girma NSA, bari in tunatar da kai cewa, wannan fa ba ayyukan ƙananan ‘yan daba ba ne kuma ba na ‘yan tawaye kawai ba ne; wannan aika-aikar ƙasurguman ‘yan ta’adda ne na gaske. Kuma suna yankan ƙauna da uzura wa al’ummar yankunan da kai da ni muka fito – AREWA!

An Yi Biris Da Jami’an Tsaro: Ya mai girma Nuhu Ribadu, a halin da ake ciki, tabbatattun alamu da shaidu suna nuna cewa hukumomin tsaro kamar sun gaji. Abin takaici, wasu ba su da kayan aiki, kuma sun rasa ƙwarin gwiwa. Ana tura sojoji da ‘yan sanda zuwa fagen fama da tsofaffin makamai, yayin da ‘yan bindigar da suke fafatawa da su, suna amfani da manyan bindigogi da hatta jiragen durons.

Wannan tabbas ne kuma zahiri ne, ana ganin yadda ‘yan bindiga suke yawo yadda suka ga dama. Suna amfani da kayan sadarwa na zamani, kamar wayoyin andiroyid, intanet, kuma suna sha’aninsu da bushasha a kafafen sada zumunta na zamani. Shin yallaɓai, wai mene ne dalilin da ke hana a bibiye su zuwa mafakarsu, domin yaƙar su Hukumomin leƙen asiri na iƙirarin suna aiki, amma me ya sa waɗannan ‘yan ta’adda suke cin karensu ba babbaka, suna sharafinsu a dazukan da aka san su da daɗewa?

Sai dai kuma yallaɓai NSA, ga wani abin mamaki – Me ya sa idan wani talaka ya yi rubutu a Facebook ko Twitter yana sukar ɗan siyasa ko saraki, ake iya zaƙulo shi ko’ina yake, a yi ram da shi cikin ƙanƙanen lokaci? Ba za a manta da abin da ya faru kwanan nan da wani saurayi a Kano da ake wa laƙabi da “Sultan” ba, wanda aka cafke cikin hanzarin saboda zargin “wai” ya tozarta manya a Soshalmidiya. Tambaya a nan ita ce: Me ya sa ba za a yi amfani da irin wannan fasaha wajen bin diddigin ‘yan ta’adda, masu sacewa, kashewa, da tozarta mutane suna karɓar kudin fansa ba?

Kira Na Musamman Ga Malam Ribadu: Ya NSA, ka sani, kai fa ba “tsuran mutum” kawai ba ne. Kai tambari ne mai amo – jagora abin koyi na haƙiƙa ne. Har yanzu muna daraja ka saboda irin rawar da ka taka a EFCC. Wannan ne ya sa muke kiran ka yau, ba kawai a matsayin NSA ba, amma a matsayin Nuhu Ribadu;  jarumin mutumin nan da ya taɓa fatattakar tawagar maha’inta, mahandama kuma mawawura dukiyar al’umma. Har yanzu muna kallon ka a matsayin kai ba ka san tsoro ko ja da baya ga azzalumai ba.

Wannan shi ne lokacinka na biyu da Allah ya ƙara sahale maka. Dole ne ka tashi tsaye. Dole ka sake buɗe murya irin wacce muka san ka da ita a baya. Tarihi na kallon ka. Al’ummar Arewa suna zubar da hawaye. Mutane suna mutuwa saboda gazawar tsaro. Jinin ‘yan ƙasa yana kwarara. Mutanen da suka san ka a baya, suke yaba wa ƙwazonka da gaskiyarka, waɗanda suka taɓa yarda da kai, a yau sun fara sanya shakku a kanka.

Har yanzu kana da damar canja taku. Yallaɓai NSA, ka yi amfani da ofishinka, iliminka, da ƙwarewarka wajen ɗaukar matakan da suka dace. Ka kafa wa shugabannin tsaro ƙahon zuƙa. Ka dage sosai wajen amfani da na’urorin leƙen asiri na zamani da fasahar zamani. Ka tabbatar da cewa jami’an tsaro suna samun kyautatawar da ta kamace su, yadda za su zama cikin kishi da shirin kare lafiya da dukiyar al’ummar ƙasa, ba kawai yadda suke biyayya da kare Shugaban Ƙasa da sauran ‘yan siyasa ba.

Ya NSA, ka ƙara ƙoƙari da azama fiye da yadda ka yi a shekarun baya, lokacin da ka ahugabanci EFCC. Yanzu ne al’umma ke da ƙishirwar aikinka, suke buƙatar ganin sawun ofishinka na NSA. Lallai Arewa ba za ta kunyata ba a hannun wasu tsirarun ‘yan ta’adda. Najeriya ba za ta tozarta ba, ba za ta gaza ba – Wannan shi ne ƙalubalen da ke gabanka da ofishinka.

Muna roƙon Allah ya ƙarfafe ka, ya ba ka hikima da fasahar ɗaukar matakan da suka dace, domin kawo ƙarshen matsalolin tsaron da ke damun yankinmu na Arewa da ma ƙasa baki ɗaya. Amin-Summa-Amin!

Naka da girmamawa.

Bashir Yahuza Malumfashi
Marubuci/Sha’iri kuma, Editan Mujallar Taskar Gizago (online), Abuja.

Previous Post

KO YANZU ZA A IYA FARA KARATU A BABBAR KWALEJIN NOMA TA NABANJE – Malam Labiru Ƙafur

Next Post

Nigeria 2027: The Best Way to Defeat President Tinubu

Related Posts

My 83rd Birthday and the Kindred Spirit
Gizago

Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya

January 19, 2026
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (9)
Gizago

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (9)

January 17, 2026
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (8)
Gizago

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (8)

January 13, 2026
Next Post
Nigeria 2027: The Best Way to Defeat President Tinubu

Nigeria 2027: The Best Way to Defeat President Tinubu

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Amina Gambo Ta Yi Bankwana Da Freedom Radio

Amina Gambo Ta Yi Bankwana Da Freedom Radio

July 31, 2023
Komawar Kwankwaso Zuwa APC: Gaba Kura Baya Sayaki

Komawar Kwankwaso Zuwa APC: Gaba Kura Baya Sayaki

July 21, 2025
Lost Heritage Series #1 – Mazari [Spindle]

Lost Heritage Series #1 – Mazari [Spindle]

September 19, 2023
Gobara Daga Kogi: Malamin Islamiyya Ya Lalata Ɗalibansa 9 Da Luwaɗi

Gobara Daga Kogi: Malamin Islamiyya Ya Lalata Ɗalibansa 9 Da Luwaɗi

December 14, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)
  • Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya
  • Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut’a

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

January 21, 2026
My 83rd Birthday and the Kindred Spirit

Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya

January 19, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.