KO YANZU ZA A IYA FARA KARATU A BABBAR KWALEJIN NOMA TA NABANJE – Malam Labiru Ƙafur
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

A kwanakin baya, Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da kafa Kwalejin Noma Da Ƙere-Ƙere a garin Nabanje, Ƙaramar Hukumar Ƙafur, Jihar Katsina. A tattaunawarmu da ɗaya daga cikin mambobin hukumar gudanarwar kwalejin, Malam Labiru Musa Ƙafur, mni, ya bayyana cewa za a iya fara karatu a makarantar, tun kafin a kammala gina mazauninta, sannan ya fayyace irin fa’idojin da al’umma za su samu daga wannan babbar makaranta da aka samu a yankin. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
TG: Za mu so ka yi mana bayani a taƙaice game da wannan babbar makaranta ta koyar da noma da ƙere-kere.
Malam Labiru: Da farko dai, kamar yadda ka sani, ina ɗaya daga cikin mambobin hukumar gudanarwa ta wannan makaranta mai suna Federal College of Agriculture & Technology. Mai girma Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR ya naɗa mu. Ita wannan makaranta ta Gwamnatin Tarayya ce. An samar da ita ce da nufin a riƙa koyar da harkokin noma, kiwo da kimiyya da ƙere-keren abubuwan da suka danganci wannan harka. Haka kuma akwai batun ilimin sarrafa abinci da sauransu.
TG: Ashe makarantar tana da faɗi haka?
Malam Labiru: Lallai kam, kasancewarta ta gaba da sakandare, makarantar babba ce. Ba kawai harkar noma tsuransa za a tsaya ba, shi ya sanya aka kira ta da sunan Federal College of Agriculture & Technology. Akwai wasu tsarin ayyuka da sana’o’i waɗanda suka jiɓinci noma, kamar sarrafa kayan gona, ƙera kayan aikin gona da sauransu. Wannan makaranta tana nan a ƙauyen Nabanje, kilomita 4 ne daga garin Ƙafur, a kan hanyar Zariya. Kamar dai yadda aka kafa Federal Polytechnic ta Efuru, wacce ta ta’allaƙa ga kimiyyar mai da iskar gas, to ita wannan ta danganci noma da kiwo da dangoginsu.
TG: Ita wannan an kafa ta don bunƙasa noma a Arewa ke nan?
Malam Labiru: Haka ne, kasancewar Arewa, nan ne harkokin noma da kiwo suke da ƙarfi. Don haka wannan makaranta, za ta amfani al’ummar Ƙafur da kewaye da Jihar Katsina da Arewa, da ma Najeriya baki ɗaya ta fuskar koya fasahar noma da kiwo na zamani kuma a ilimance, domin bunƙasa ƙasa da abinci da samar da ayyukan yi da sana’o’i.

TG: Ko akwai wani shiri na fara karatu da sauri a makarantar, duk da cewa ba a gama gina mazauninta na dindindin ba?
Malam Labiru: Fatanmu ne mu ga makarantar ta fara aiki nan ba da daɗewa ba. Ka san ba za ta fara ba, har sai hukumomin da ke kula da al’amarin sun ba da izinin haka. Amma akwai wuraren da suka dace na wucingadi da za a iya fara karatu, idan an ba da izinin. A nan ƙauyen Nabanje, akwai wata makarantar koyon sana’o’i (Skills Acquisition Centre), akwai asibiti babba, wanda ba a fara aiki da shi ba, akwai makarantar sakandaren rana-rana. Duk waɗannan wuraren, za a iya amfani da su domin fara karatu, kafin kammala ginin makarantar na dindindin. Kuma shi Hon. Ibrahim Kabir Masari, akwai wuraren da zai iya tanada a cikin garin Masari da Ƙafur, domin samar da gidajen kwana ga malamai, na wucin-gadi, kafin makarantar ta samu nata.
Kuma koda za a fara yanzu, babu wata damuwa. Ya zuwa yanzu dai Hukumar NBTC (mai kula da kwalejijin kimiyya da ƙere-kere) sun zo har karo biyu, sun duba wuraren da na gaya maka. Kuma sun gamsu da cewa za a iya fara karatu. Haka su ma jami’an gudanarwa sun zo sun duba kuma sun ce lallai za a iya fara karatu a wuraren na wucin-gadi. Yanzu abin da kawai ake jira, shi ne hukumomin da ke da ikon ba da izini da kuma kuɗin gudanarwa daga Gwamnatin Tarayya.
TG: Wane irin muhimmanci ya kamata al’ummar Yankin Karaɗuwa ya kamata su ba wannan makaranta?
Malam Labiru: Kamar yadda ka faɗa, ya kamata mutane su san cewa, wannan makaranta ta Gwamnatin Tarayya ce, don haka ta ‘yan Najeriya ce baki ɗaya. Ke nan ɗan ƙasa zai iya zuwa daga kowane yanki yake. Amma dai ai an ce da arziƙi a garin wasu, gara a ce garinku ne. Don haka ina kira ga al’ummarnu da su shirya amsar baƙi daga dukkan sassan ƙasar nan. Hakan ma kaɗai zai bunƙasa yankin namu, baya ga sauran abubuwan amfani marasa adadi.
TG: A faɗaɗa mana bayani, yallaɓai.
Malam Labiru: Kamar yadda na ce, wannan makaranta ta kowa ce a Najeriya. Ta fannin ɗaukar ma’aikata da ɗalibai da sauransu, za a duba cancanta ne da dacewa, domin nagarta ake so da biyan buƙata domin bunƙasa al’umma ta fannin noma da kiwo da sana’o’in da suka dangance su, amma kasancewar a nan yankin take, lallai akwai wani tagomashi na musamman da al’ummarmu za su samu mai yawa. Misali, hatta ta fannin sana’o’i da ayyukan yi za su ƙaru a wannan yanki, albarkacin makarantar nan, domin baƙi za su shigo daga sassa daban-daban.

Kuma ina ba da shawara da cewa mu ba da haɗin kai da goyon baya, ta yadda al’amarin zai amfane mu sosai. Kada mu damu da cewa dole sai wane ɗan nan zai zama shugaba kaza da kaza. Abin da ake buƙata shi ne bin doka da oda da ƙa’ida. Zan ba ka misali da Jami’ar Ahmadu Bello Zariya. Lokacin da aka gina ta, Sardauna Ahmadu Bello, daga ƙasar Newzealand ya ɗauko VC (Shugaban Jami’a), ba ma daga Ingila ba, wacce ita ce uwa ga Najeriya a lokacin. Wannan ke nuna, madamar mutum ya cancanta kuma zai bayar da abin da ake bukata da nagarta, to babu damuwa da inda ya fito. Muna fatan dai a samu nasara, yaranmu su samu ilimi, al’ummarmu ta samu cigaba, ƙasarmu ta bunƙasa da arziƙin noma da kiwo da sauransu.
_______________













