• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, September 10, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Labarai

Garin Zango Ya Samu Babban Asibiti na Farko A Tarihi

DIKKON KATSINAWA

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
August 7, 2026
in Labarai
0
Garin Zango Ya Samu Babban Asibiti na Farko A Tarihi

Dikkon Katsinawa (04)

16
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Garin Zango Ya Samu Babban Asibiti na Farko A Tarihi

Daga Bashir Yahuza Malumfashi
__________
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON, ya ƙaddamar da sabon Babban Asibiti a Zango, wanda shi ne babban asibiti na farko da aka kafa a tarihin Ƙaramar Hukumar.

Related posts

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

September 8, 2026
Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda

Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda

September 6, 2026

An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne a jiya Alhamis, 6 ga Agusta, 2026, inda gwamnatin jihar ta bayyana aikin a matsayin wani muhimmin mataki na inganta tsarin kiwon lafiya da kuma faɗaɗa ayyukan jinya ga al’ummar jihar.

A jawabin maraba, Kwamishinan Lafiya na Jihar Katsina, Hon. Musa Adamu Funtua, ya ce ƙaddamar da sabon asibitin wani gagarumin ci gaba ne a ƙoƙarin gwamnatin jihar na samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga jama’a. Ya bayyana cewa aikin ya nuna irin jajircewar Gwamnatin Malam Dikko Umaru Radda wajen bunƙasa harkar lafiya a faɗin jihar.

Da yake jawabi, Gwamna Radda ya gode wa Allah Maɗaukakin Sarki bisa bai wa gwamnatinsa damar kammala aikin, yana mai bayyana cewa an samar da sabon asibitin ne ta hanyar ɗaga darajar tsohuwar Cibiyar Kiwon Lafiya ta Matakin Farko da ke Zango zuwa cikakken Babban Asibiti.

An ƙaddamar da Babban Asibiti na farko a tarihi, a Zango

Ya bayyana cewa an tanadi asibitin da sabbin kayan aikin lafiya na zamani domin gudanar da ayyukan jinya da tiyata cikin inganci. A cewarsa, hakan zai rage yawan tura marasa lafiya zuwa manyan asibitoci da ke nesa tare da sauƙaƙa samun ingantacciyar kulawar lafiya ga al’ummar Zango da maƙwabtan ƙananan hukumomi.

Gwamnan ya jaddada cewa harkar lafiya na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta bai wa fifiko, tun bayan hawansa mulki. Ya lissafo nasarorin da aka samu cikin shekaru uku da suka gabata, waɗanda suka haɗa da ɗaga darajar cibiyoyin kiwon lafiya guda huɗu zuwa Manyan Asibitoci, inganta wasu cibiyoyin lafiya, gyaran manyan asibitoci da ɗakunan tiyata, farfaɗo da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko (PHCs) sama da 280, da ɗaukar sabbin ma’aikatan lafiya guda 804 aiki.

Sauran nasarorin da ya bayyana sun haɗa da gina cibiyar wankin ƙoda ta zamani (Dialysis Centre), kafa cibiyar sarrafa magunguna da kuma faɗaɗa amfani da wutar lantarki ta hasken rana a asibitocin gwamnati, domin tabbatar da ci gaba da gudanar da ayyukan lafiya.

Har ila yau, Gwamna Radda ya sanar da cewa gwamnatin jihar ta fara shirin horar da likitoci (Medical Residency Training) a fannoni shida na likitanci a manyan asibitocin jihar. Ya ƙara da cewa gwamnati na ci gaba da ɗaukar nauyin karatun ɗaliban fannin likitanci a jami’o’in cikin gida da na ƙasashen waje domin magance ƙarancin ƙwararrun ma’aikatan lafiya.

Tun da farko, Babban Manajan Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Katsina, Dr. Muhammad Nazir, ya tabbatar da cewa za a gudanar da sabon asibitin bisa ƙa’idojin ƙwarewa da inganci domin samar wa al’umma ingantattun ayyukan kiwon lafiya.

Shi ma Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Katsina, Dakta Bishir Gambo Saulawa, ya yaba wa gwamnatin jihar kan ci gaba da zuba jari a fannin kiwon lafiya da sauran sassan ci gaba. Ya bayyana ƙaddamar da asibitin a matsayin cika wani muhimmin alƙawarin gwamnati na inganta rayuwar al’ummar jihar.

A nasa jawabin, Shugaban Ƙaramar Hukumar Zango, Hon. Babangida Yardaje, ya gode wa Gwamna Radda bisa samar da asibitin, yana mai tabbatar masa da cewa al’ummar yankin za su ba da cikakken haɗin kai wajen kula da kayan aikin asibitin da tabbatar da dorewar ayyukansa.

A ƙarshe, Gwamna Radda ya yi kira ga al’ummar Ƙaramar Hukumar Zango da maƙwabtan yankunan, da su kare wannan katafaren asibiti tare da ba ma’aikatan lafiya cikakken haɗin kai, domin tabbatar da ingantaccen aikin kula da lafiyar jama’a.

Bikin ƙaddamar da asibitin ya samu halartar Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Rt. Hon. Nasir Yahya Daura; Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati, Hon. Abdulkadir Mamman Nasir; Mai Ba Jam’iyyar APC Shawara ta Fuskar Shari’a, Barista Murtala Aliyu Kankia; Kwamishinan Yaɗa Labarai, Dr. Bala Salisu Zango; ‘yan takarar jam’iyyar APC; shugabannin ƙananan hukumomi; ‘yan majalisar dokoki; ‘yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki.
__________

Previous Post

Zango Local Government Enjoys First-Ever General Hospital

Next Post

Hukuma Ta Kafa Sabbin Sassa Domin Bunƙasa Al’umma A Jihar Katsina

Related Posts

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin
Labarai

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

September 8, 2026
Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda
Labarai

Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda

September 6, 2026
Katsina A Makon Jiya (Daga 24 Zuwa 30-08-2026)
Labarai

Katsina A Makon Jiya (Daga 24 Zuwa 30-08-2026)

August 31, 2026
Next Post
Hukuma Ta Kafa Sabbin Sassa Domin Bunƙasa Al’umma A Jihar Katsina

Hukuma Ta Kafa Sabbin Sassa Domin Bunƙasa Al'umma A Jihar Katsina

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

MALUMFASHI/KAFUR: Dr. Aminu Waziri Steps Forward

MALUMFASHI/KAFUR: Dr. Aminu Waziri Steps Forward

April 19, 2026
Ana Tuhumar Sanata Da Yi Wa Wata Yarinya Fyaɗe

Ana Tuhumar Sanata Da Yi Wa Wata Yarinya Fyaɗe

October 4, 2025
Deepening Security Crisis: Buratai Calls for Emergency Measures

Deepening Security Crisis: Buratai Calls for Emergency Measures

June 14, 2026
₦16,000 Za Mu Sayar Da Taki A Jigawa – Gwamna Namadi

₦16,000 Za Mu Sayar Da Taki A Jigawa – Gwamna Namadi

July 26, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai
  • Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?
  • SANATA BELLO MANDIYA: Mun Yi Babban Rashi – Gwamnan Katsina

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

September 10, 2026
Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

September 9, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.