Zargin Tallafa Wa Ta’addanci: Hafsoshin Soja Sun Aika Kakkausan Gargaɗi Ga Sahara Reporters
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

_______________
Wani babban cece-kuce ya kunno kai a fagen tsaro da kafafen yaɗa labarai a Najeriya, bayan fitar wata takardar gargaɗi mai zafi da aka saki a madadin tsofaffin Hafsoshin Sojojin Najeriya guda biyu, watau tsohon Jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin, Laftanar Janar Tukur Yusufu Buratai (rtd), CFR, da wanda ya gaje shi kai tsaye, Laftanar Janar Faruk Yahaya (rtd), a matsayin martani ga wani rahoton Sahara Reporters da ke zargin cewa tsofaffin hafsoshin suna da alaƙa da wasu mutanen da aka bayyana a matsayin masu ɗaukar nauyin ta’addanci.
Wata sanarwa da Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman (mai ritaya), mni, fnipr, ya sanya wa hannu ta yi watsi da rahoton, inda ya bayyana shi a matsayin “ƙarya, kushe, cin zarafi da zargi marar tushe, waɗanda aka kitsa da gangan da nufin ɓata suna da mutuncin Buratai da Yahaya.”
A cewar tsoffin hafsoshin, Sahara Reporters ta dogara kacokan kan “iƙirari marar tushe daga bakin mutum ɗaya, Manjo-Janar Danjuma Ali Keffi (mai ritaya), wajen yaɗa abin da su ka kira labarin ƙage da ba shi da alaƙa da gaskiya, babu tantancewa daga hukuma. Kamar kuma yadda ikirarin ya yi watsi da kyawawan ayyukan da tsohon Jakada Buratai ya gudanar na gina ƙasa.
Sanarwar ta jaddada cewa: A kowane mataki na aikinsa a soja ko aikin jakadanci, ba a taɓa titsiye Buratai, ko gudanar da bincike a kansa, ko tuhumarsa, ko ambatonsa a kowace hukuma kan batun zargin tallafa wa ta’addanci ko ‘yan ta’adda ba.
Babu wata hukumar tsaro ta cikin gida ko ta waje, ko cibiyar leƙen asiri, ko kwamitin bincike, ko ofishin diflomasiyya da ta taɓa danganta shi da ta’addanci ko masu ɗaukar nauyinsa. Wannan zargi a kansa ya saɓa wa tarihin aikinsa na sama da shekaru arba’in da ya shafe yana yaƙi da ta’addanci.
Tsofaffin janar-janar ɗin sun nuna cewa labarin Sahara Reporters “gaba ɗayansa an ƙirƙira shi ne bisa mugun nufi,” suna mai cewa dama can Sahara Reporters ta yi ƙaurin suna wajen ɓata sunan Buratai, duk da cewa rashin hujja kan rusa labarun nasu.
Yayin da sanarwar ke ƙarin bayani game da Buratai kan abin da ya shafi yaƙi da ta’addanci, ta jaddada cewa idan akwai wani hafsan soja na Najeriya da rayuwarsa da aikinsa suka tsayu kan yaƙi da ta’addanci, to shi ne Laftanar Janar T.Y. Buratai.
Janar Kukasheka ya ce a lokacin da Buratai yake shugabancin Hafsoshin Soja, Rundunar Sojan Najeriya ta yi wa Boko Haram da ISWAP mummunan rauni, musamman tsakanin 2015 zuwa 2020. An ƙwato ƙananan hukumomi da dama da ’yan ta’adda suka mamaye a baya. An maido da ikon farar hula a yankuna masu yawa. Ɗaruruwan dubban ’yan gudun hijira sun koma gidajensu bayan shirye-shiryen tabbatar da tsaro.
Tsofaffin hafsoshin sojan sun bayyana cewa “bai dace ba kuma bai yi kama da hankali da tunani ba,” a danganta Buratai da masu ɗaukar nauyin ta’addanci ba, musamman idan aka yi la’akari da yadda ya sadaukar da dukkan rayuwarsa wajen yaƙi ta’addanci.
Hafsoshin biyu sun yi gargaɗi kai tsaye ga Sahara Reporters da Manjo-Janar Ali-Keffi (mai ritaya) da su: “Gaggauta janye labarin zargin nasu kuma su aika wa Buratai da Yahaya da cikakkiyar takardar ban haƙuri a bainar jama’a.”
Suka ce idan ba a yi haka ba, za su ɗauki matakin shari’a domin kare martabarsu, har ma da neman diyyar ɓata suna.
Wannan shi ke nuna girma da muhimmancin da tsoffin manyan hafsoshin sojan suka ɗauki batun zargin, wanda a ganinsu ka iya rikitar da jama’a da kuma lalata ƙimar hukumomin tsaro na ƙasa.
Tsohon kakakin rundunar sojan Najeriya, Janar Kukasheka, ya ce tun bayan ritaya, Buratai ya mai da hankali kan zaman lafiya, yaɗa ilimi, da ci gaban ƙasa. Ya ƙara da cewa babu abin da yake yi a yanzu sai gabatar da laccoci a jami’o’i, bayar da gudunmawa ga manufofin tsaron ƙasa, aikin samar da zaman lafiya da sasanta rikice-rikice da ayyukan jin ƙai don tallafa wa al’umma da cigaban matasa.
Haka kuma an bayyana cewa dukkan kyawawan ayyukan Buratai, “ana da su a rubuce, suna nan daram, kuma babu wani zargi ko labarin ƙarya da zai lalata su.”
Haka kuma, wannan lamari ya sake kunna muhawara dangane da tsarin aikin jarida da tsaro a ƙasa. Hakan na bayyana yadda ake samun gurɓatattun kafafen watsa labarai, waɗanda suke yaɗa labarun ƙarya, kamar kuma yadda lamarin ke samar da ƙalubale ga manyan hafsoshi da himmarsu waje yaƙi da ta’addanci.
Masana tsaro sun ce duk da cewa ’yancin faɗar albarkacin baki muhimmi ne, zargin tallafa wa ta’addanci na buƙatar ingantattun bincike sosai saboda tasirinsa kan ƙasa da kuma harkokin ƙasashen duniya.
Yayin da cece-kucen ke cigaba, kira da aka yi na a janye labarin tare da yiwuwar gurfanar da jaridar gaban kotu, lamarin ya buɗe sabon babi a dangantakar da ke tsakanin Sahara Reporters da manyan jami’an gwamnati. Abin jira a gani shi ne, shin kafar za ta tsaya kan abin da ta wallafa ko kuma ta za ta amsa buƙatar tsofaffin hafsoshin? Lokaci ne zai nuna.
Ko me ake ciki dai, Janar Kukasheka ya bayyana cewa bai kamata a ɓata sunan Janar Tukur Yusufu Buratai da Faruk Yahaya, ta hanyar danganta su da labarai marasa tushe ba. Ya jaddada cewa manyan ayyukan da suka gabatar na tabbatar da zaman lafiya da yaƙi da ta’addanci sun isa su ba su kariya daga zargi da labarun ƙarya.
_______________













