Yadda Ƙungiyar NAL Ta Karrama Dokta Bukar Usman A Legas
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

A makon da ya gabata ne Ƙungiyar Ƙwararrun Masana ta Najeriya (Nigerian Academy of Letters) ta gudanar da gagarumin bikin da ta saba gabatarwa a kowace shekara, inda ta karrama sababbi da tsofaffin membobinta, cikinsu a bana har da fitaccen masani, marubuci kuma mai tallafa wa al’umma, Dokta Bukar Usman, OON.
Tun da farko dai, Babban Kwamitin Gudanarwar Ƙungiyar Ƙwararrun Masana ta Najeriya (NAL) ce ta aiko wa Dokta Usman wasiƙar da ta sanar da shi cewa ta zaɓe shi domin ta karrama shi ya zama ɗaya daga cikin membobinta.
Wasiƙar mai ɗauke da rana da kwanan wata, 7 ga Yuli, 2024, wacce Shugaban Ƙungiyar NAL, Farfesa Sola Akinrinade, FNAL ya sanya wa hannu, ta bayyana dalilin da ya sanya aka karrama shi. Shugaban a cikin wasiƙar ya ce:
“A yayin taron Babban Kwamitin Gudanarwa da ya gudana a ranar 4 ga Yuli, 2024, an amince da zaɓen ka, domin a karrama ka, ka zama Memba na Ƙungiyar Ƙwararrun Masana ta Najeriya (Hon. FNAL).”
Shugaban ya ci gaba da cewa: “Wannan lamba ta HFNAL, ita ce mafi girma da Ƙungiyar NAL ke karrama jajirtattu kuma zaɓaɓɓun mutane da ita. Mutane waɗanda ba ‘ya’yan da’irar ba ne amma waɗanda suka yi fice wajen tallafa wa al’umma ta fuskar bunƙasa fasaha da ilimi a Najeriya. Wasu daga cikin fitattun mutane da aka taɓa karramawa da wannan lamba sun haɗa da marigayi Mista Gamaliel Onosode da marigayi Sarkin Bida, Mai Martaba Etsu Nupe, Alhaji Umaru Sanda Ndayako da marigayi Oba na Benin, Mai Martaba Omo n’Oba n’Edo Erediauwa da marigayi Malam Adamu Ciroma da Cif Emeka Anyaoku, tsohon Babban Sakataren Ƙungiyar Kasashe Rainon Ingila (Commonwealth) da kuma Babban Rabaran, Bishop, Dokta Mathew Hassan Kukah. Muna taya ka murnar zama ɗaya daga cikin waɗannan shahararrun ‘yan Nigeria.”

A nasa ɓangaren, a lokacin da yake amsa wannan abin karimci da aka yi masa, Dokta Usman, a wasiƙar da ya rubuta mai ɗauke da kwanan wata 09-07-2024, ya bayyana godiya tare da gamsuwa da wannan karramawa da Ƙungiyar NAL ta yi masa.
Kamar yadda ya ce a wasiƙar tasa: “Ina matuƙar yabawa da karimcin da aka yi mani. Bisa ga haka, ina godiya a gare ka (Shugaba) da membobin Kwamitin Gudanarwa da sauran membobin Ƙungiyar NAL da suka ga dacewa da cancanta ta, suka zaɓe ni kuma suka karrama ni. Da ikon Allah zan halarci taron.”
A ranar bikin, tun da misalin ƙarfe 9:30 na safe, mahalarta suka fara zama a kujerun da suka mamaye babban zauren taro na J. F. Ade Ajayi Auditorium da ke Jami’ar Legas. Bayan mahalarta sun kintsa, sai Shugaban Ƙungiyar NAL, Farfesa Akinrinade ya gabatar da taƙaitaccen jawabin maraba, inda ya yaba wa dukkan membobin da suka halarci wannan gagarumin taro. Haka kuma ya yi wa kowa fatan alheri, sannan ya sake jaddada ƙudurin wannan Cibiya, na ci gaba da yi wa al’ummar ƙasa hidima, ta bangaren bunƙasa ilimi.
Daidai misalin ƙarfe 10:30 sai aka gayyaci Babban Mai Jawabi na Musamman, Farfesa Alkasum Abba, MNAL, wanda ya gabatar da lacca mai taken ‘Ƙalubalen Mulkin Dimokuraɗiyya A Najeriya: Matsalar Tsarin Ne Ko Na Masu Gudanarwa?’ (The Challenge of Nigerian Democracy: Problem of the System or its Managers)?
Masanin ya ɗauki lokaci wajen zaƙulo manya da ƙananan ƙalubale da matsalolin da suka addabi tsarin gudanar da mulki a Najeriya, tun daga mulkin kai a 1960 har zuwa yau.
Ya bayyana cewa manyan matsaloli da ƙalubalen sun haɗa da ƙabilanci, ɓangaranci da kuma cin hanci da rashawa da almundaha da suka yi katutu a tsakanin shugabanni da ma’aikatan gwamnati. Ya bayyana cewa, madamar ana son ƙasar nan ta ci gaba, to dole sai an magance waɗannan matsaloli, sai an samu haɗin kai da kishin ƙasa tsakanin al’ummar ƙasa da shugabanni da ma’aikatan gwamnati.
Bayan kammala lacca, sai kuma aka tsunduma wajen wanke sababbi membobin da suka samu shiga Ƙungiyar Ƙwararrun Masana ta Najeriya na bana. A wannan fannin, an fara da Farfesa Asabe Kabir Usman, wacce tun a bara ya kamata a yi mata wankan amma ba a samu yin haka ba, dalili ke nan ta shigo cikin rukunin sababbin membobi na bana.
Daga Farfesa Asabe, sai kuma aka shiga bikin wankan sababbin membobi guda 9, waɗanda suke zaune a nan gida Najeriya. Waɗannan kuwa sun haɗa da Farfesa Anthony Esijolomi Afejuku, Farfesa Florence Orabueze, Farfesa Olukoya Ogen, Farfesa Olatunji Alabi Oyeshile, Farfesa Olusanjo Mathew Abayomi Daramola, Farfesa Emmanuel Calvin Emasealu, Farfesa Cecelia Amaoge Eme, Farfesa Landzemo Constantine Yuka da kuma Farfesa Afis Ayinde Oladosu. Dukkansu an sanya masu rigunan shahada tare da hulunansu, sannan kuma kowannensu, aka bayyana tarihinsa a taƙaice.

Rukuni na gaba da aka yi wa wanka, su ne sababbin membobin da ke zaune a ƙasashen waje. Masana uku ne a wannan rukunin kuma sun haɗa da Farfesa Abiodun Salawu, Farfesa Emerita Omofolabo A. Ajayi-Soyinka da kuma Farfesa Hakeem Ibikunle Tijani.
Daga nan kuma sai rukunin masanan da aka karrama da lambar Ƙungiyar Ƙwararrun Masana ta Najeriya ta HNAL. Waɗannan kuwa su ne jajirtattun mutane biyu da suka daɗe suna yi wa al’umma hidima ta hanyar rubuce-rubuce da bunƙasa ilimi. Waɗannan kuwa su ne Dokta Bukar Usman, OON da kuma Dokta Wale Okediran.

Haka kuma, an karrama shararren mai shirya fina-finai, Zeb Ejiro, OON, saboda albarkacin sana’arsa ta fim, wacce ya daɗe yana gudanarwa kuma ya yi fice a cikinta.
Jim kaɗan da kammala bikin, wakilinmu ya tattauna da Dokta Usman, inda ya tambaye shi ko yaya ya ji da wannan karimci da aka yi masa. Ya bayyana matuƙar murna tare da godiya ga shugabannin wannan ƙungiya ta NAL.
“Ni da Dokta Wale Okediran da aka karrama, mu kaɗai ne masu muƙamin Dokta, sauran duk Farfesa-Farfesa ne. A tsarin Ƙungiyar NAL, sai mutum ya kai muƙamin Farfesa sannan yake cancanta ya zama memba a cikinta. Kuma koda ya zama Farfesa, sai ya shekara biyar a muƙamin kuma sai ya nemi izinin shiga, sannan bayan an zaɓe shi sai a amince masa.” In ji Dokta Usman, HFNAL.
Ko wannan karimci zai ƙara masa ƙaimi wajen ci gaba da hidimar bunƙasa ilimi da ya saba kuma aka san shi da ita? Tambayar da wakilinmu ya yi masa ke nan, inda shi kuma ya amsa da cewa:
“Wannan karimci na Ƙungiyar NAL ya ƙara mani ƙaimi. Kodayake da ma tun kafin a karrama ni, ina ci gaba da rubuce-rubucena. Don haka zan ci gaba har sai inda ƙarfina ya ƙare.”
Ko wane saƙo zai ba al’umma dangane da harkar ilimi? Dokta Usman ya ce: “Ya kamata al’ummar Arewa mu tashi tsaye domin neman ilimi da bunƙasa shi. Ba a ce a daina karatun ilimin addini na tsangaya ba amma ko da mutum yana da shi, to kuma ya nemi ilimin zamani. Ka ga yaranmu da yawa suna yawo a titi, babu ilimi. Lallai ne gwamnatocin Arewa su tashi tsaye, su mai da himma wajen bunƙasa ilimin zamani a wannan yanki.”
Bikin, wanda shi ne karo na 26, ya gudana ne a babban zauren taro na J. F. Ade Ajayi Auditorium, Jami’ar Legas da ke Unguwar Yaba na birnin Legas, Najeriya, a ranar Alhamis, 8 ga Agusta, 2024. An fara bikin daidai misalin ƙarfe 10 na safe kuma aka kammala da misalin ƙarfe 12:30 na rana.
Wane Ne Dokta Bukar Usman, OON?
An haifi Dokta Bukar Usman, M.CIoD, D.Litt, OON, HFNAL a ranar 10 ga watan Disamba, 1942 a Biu, Jihar Borno. Ya fara karatun zamani tun daga shekarar 1951, inda har ya kai ga kammala karatun digiri na farko a Jami’ar Ahmadu Bello, a shekarar 1969.
Cikin makarantun da ya halarta sun haɗa da Biu Central Primary School, Yerwa Senior Primary School, Borno Provincial Secondary School, King’s College Lagos da kuma Jami’ar Ahmadu Bello Zaria.
Ta ɓangaren aikinsa kuwa, ya halarci manya da ƙananan kwasa-kwasai daban-daban na ƙarin ilimi a cikin gida da kasashen waje. Ya samu Digirin Digirgir na Girmamawa na D.Litt (St. Clements University) a shekarar 1999. Haka kuma Jami’ar Ahmadu Bello Zaria ta karrama shi da Digirin Digirgir na D.Litt a shekarar 2014.

Dokta Usman yana ɗaya daga cikin membobin ƙungiyoyi daban-daban da suka haɗa da Ƙungiyar Tsofaffin Ɗaliban King’s College (Golden Ingots/Tripartite Set 1960, 63-65), Kungiyar Marubuta ta Najeriya, Kungiyar Masu Tuntuɓa ta Kwalejin Manyan Ma’aikatan Gudanarwa, Kungiyar Makiyaya da Manazarta Kimiyya da Fasahohi Al’umma ta Najeriya da kuma Ƙungiyar Daraktoci ta Najeriya.

Ta ɓangaren aiki kuwa, ya fara aiki ne a matsayin ƙaramin jami’in ofis mai mataki na 3, a Ma’aikatar Sadarwa, a ranar 17 ga Disamba, 1965. Ya yi ta samun ci gaba da ƙarin girma a sassa daban-daban da ya riƙa aiki a Ofishin Shugaban Ƙasa, inda har daga ƙarshe ya samu muƙamin Babban Sakatare a ranar 24 ga watan Mayu, 1988. Ya yi ritaya daga aiki a ranar 30 ga watan Afrilu, 1999.
Bayan ya kammala aikin gwamnati, Dokta Usman bai zauna haka nan ba, ya ci gaba da harkokin ƙashin kansa a fagage daban-daban na rayuwa, inda daga bisani ya kafa Gidauniyar Dokta Bukar Usman a shekarar 2008, inda ta hanyarta yake taimaka wa al’umma ta fuskar bunƙasa ilimi, jin ƙai da sauransu.


Mutum mai hangen nesa, mai haƙuri kuma mai jajircewa a dukkan abin da ya sanya hannu, ya shugabanci al’amura da ƙungiyoyi daban-daban, tun yana cikin aiki, har kuma zuwa yanzu da yake zaman ƙashin kansa. A halin da ake ciki, har yanzu shi ne Daraktan Kamfanin CentrePoint Investments Limited, Shugaban Kamfanin New-Halcyon Ventures Limited, Shugaban Kamfanin Creamland (Nigeria) Limited, Editan Kamfanin Wallafa na Klamidas Classic Folktales Series, Book Writer & Publishing, Shugaban Cibiyar Raya Harshen Hausa da Al’adunsu da kuma Shugaban Kungiyar Makiyaya da Manazarta Kimiyya da Fasahohin Al’umma ta Najeriya. An shaide shi da iya shugabanci da jagoranci a dukkan inda yake shugabanci.
Dokta Usman ya samu lambobin yabo da karramawa da dama, waɗanda suka haɗa da Lambar Karramawa Ta Ƙasa ta CON (Commander of the Order of the Niger) a shekarar 1998 da Lambar OON (Officer of the Order of the Niger) a shekarar 2000.

Bayan ya yi ritaya daga aikin gwamnati, Dokta Usman ya tsunduma cikin harkokin rubuce-rubuce da wallafa, inda daga shekarar 1999 zuwa yau, ya rubuta tare da wallafa manya da ƙananan littattafai sama da 40, cikin harsunan Ingilishi, Hausa, Ajami, Igbo da Yarabanci.
Wasu daga cikin litattafan nasa sun haɗa da Democracy, Human Rights and National Stability; Folklore and History: The Twin Rivers of World Heritage; Language Disappearance and Cultural Diversity in Biu Emirate; Voices in a Choir: Issues in Democratisation and National Stability in Nigeria; Hatching Hopes; My Literary Journey; My Public Service Journey; A History of Biu; Taskar Tatsuniyoyi da sauransu.
Wani abin yabawa kuma abin sha’awa shi ne, kusan dukkan littattafan da yake wallafawa, kyauta yake raba su zuwa manya da ƙananan makarantu da cikin gida Najeriya da ƙasashen waje da ɗakunan karatu da cibiyoyin ilimi. Ga shi kuma dukkan littattafansa, ana buga su ne cikin kyau da inganci, masu ban sha’awa.
Wannan shi ne Dokta Bukar Usman, OON, HFNAL – mutum mai dattaku da karimci. Muna roƙon Allah Ya ƙara masa himma da albarka.,













