• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, July 10, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

SHAWARA TA FI MUHAWARA

WAƘEN FASAHA

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
August 15, 2024
in Adabi
0
34
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend
Shawara Ta Fi Muhawara

SHAWARA
     TA FI
MUHAWARA

Kafin ka yi magana,
Yaka ka zo nan ɗan uwa.

Related posts

Maryam ‘Yar Aljanna (2)

Maryam ‘Yar Aljanna (2)

June 22, 2026
Dakta Bukar Usman Zai Gabatar Da Sharhin Littafin Tarihin Al’ummar Lassa

Dakta Bukar Usman Zai Gabatar Da Sharhin Littafin Tarihin Al’ummar Lassa

June 21, 2026

Sai ka lura ka gane,
Maganar ina taka zuwa?

Magana zarar bunu ce,
In ta fita ba ta komuwa.

Magana iri biyu ce,
Muddin za ka batuwa.

Wata kam alheri ce.
Alherin shi ka samuwa.

Akasin ta sharri ne,
Sharrin shi ka wanzuwa.

Ɗan uwa ka lura ka gane,
Batun nan sai da kintsuwa.

‘Yar uwa ki zam dubawa,
Har kullum sai da natsuwa.

Duk idan za ku aikata,
Wani aiki duk mai bazuwa.

Shi ma a nan iri biyu ne,
Babu na ukkunsa ‘yan uwa.

Wani kam mai kyawu ne,
Na biyun mai sanya damuwa.

Shi hali zanen dutse,
Kulluyaumin ba ya goguwa.

Sai mu zamto yin kirki,
Domin shi ne gyaruwa.

Mu tsare haƙƙin addini,
Shi ne turba ta shiryuwa.

Mu yi soyayya don Allah,
Ita ce ribar da ka yaɗuwa.

Mu riƙe Manzon Allah,
Almusɗafa mai bagaruwa.

Hassada mugun ciwo,
Mu guje ta sai mu tohuwa.

Mu zam yin adalci,
Shi ne jigo a rayuwa.

Gaskiya babbar hanya,
Ita ce ke kai mu datuwa.

Mu taimaki junanmu,
Haɗin kai kama hannuwa.

Allah sanya mu mu dace,
Ka sassaita mu rayuwa!
__________
© Bashir Yahuza Malumfashi
Jumu’a, 24-12-1441 (Hijriyya)
14-08-2020 (Miladiyya)

Previous Post

Zuwa Ga Gwamna Abba Kabir Yusif

Next Post

Yadda Ƙungiyar NAL Ta Karrama Dokta Bukar Usman A Legas

Related Posts

Maryam ‘Yar Aljanna (2)
Adabi

Maryam ‘Yar Aljanna (2)

June 22, 2026
Dakta Bukar Usman Zai Gabatar Da Sharhin Littafin Tarihin Al’ummar Lassa
Adabi

Dakta Bukar Usman Zai Gabatar Da Sharhin Littafin Tarihin Al’ummar Lassa

June 21, 2026
Maryam ‘Yar Aljanna
Adabi

Maryam ‘Yar Aljanna

June 20, 2026
Next Post
Yadda Ƙungiyar NAL Ta Karrama Dokta Bukar Usman A Legas

Yadda Ƙungiyar NAL Ta Karrama Dokta Bukar Usman A Legas

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

TSOKACINMU NA YAU (16)

TSOKACINMU NA YAU (16)

March 16, 2025
Daura Birnin Bayajidda: Janar Buratai Da Ayarinsa Sun Ziyarci Buhari Da Sarki

Daura Birnin Bayajidda: Janar Buratai Da Ayarinsa Sun Ziyarci Buhari Da Sarki

June 4, 2023
MALUMFASHI/KAFUR: Dr. Aminu Waziri Steps Forward

MALUMFASHI/KAFUR: Dr. Aminu Waziri Steps Forward

April 19, 2026
Governor Radda Builds Nigeria’s Largest Motor Park

Gwamna Raɗɗa Ya Kusa Kammala Tashar Mota Mafi Girma A Najeriya

September 30, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Afirka Ta Fice Daga Gasar Kofin Duniya Na Bana
  • Book Launch Seeks to Rewrite Lassa’s Story, Preserve Cultural Heritage
  • Zaɓen 2027: Akwai Yiwuwar Farfesa Pantami Ya Yi Nasara – Farfesa Lawanti

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Afirka Ta Fice Daga Gasar Kofin Duniya Na Bana

Afirka Ta Fice Daga Gasar Kofin Duniya Na Bana

July 10, 2026
Book Launch Seeks to Rewrite Lassa’s Story, Preserve Cultural Heritage

Book Launch Seeks to Rewrite Lassa’s Story, Preserve Cultural Heritage

July 9, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.