• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, January 16, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

Babban Burina A Rubutu: In Bar Baya Mai Kyau – AHA

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
November 4, 2023
in Adabi
0
Babban Burina A Rubutu: In Bar Baya Mai Kyau – AHA

Malama Amina Hassan Abdulsalam

48
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Babban Burina A Rubutu: In Bar Baya Mai Kyau – AHA

~~~~~~~
Sunanta Amina Hassan Abdulsalam. Malamar makaranta ce, mai aikin tallafa wa marayu da marasa galihu ta fuskar ilimi. Ita marubuciya ce mai ta fannoni da dama, kamar ƙirƙirarrun labarun Hausa da Ingilishi. Marubuciyar wasan kwaikwayo da waƙa. Tana cikin marubutan farko da suka yi nasarar zama zakaru a Gasar Hikayata da Sashen Hausa na BBC ya fara a shekarar 2016. Marubuciyar ta tattauna da Bashir Yahuza Malumfashi a Mujallar Taskar Gizago.
~~~~~~~

Related posts

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

December 23, 2025
Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine

Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine

December 6, 2025
Wasu daga cikin littattafan marubuciya AHA

TG: Kina ɗaya daga cikin marubutan Hausa, ko za ki gaya mana tarihinki a taƙaice?

AHA: Sunana Amina Hassan Abdulsalam. An haife ni a Kano, na yi karatun Allo da Islamiyya. Na yi boko tun daga matakin firamare zuwa jami’a. Ina da shekaru arba’in da bakwai a duniya yanzu.

TG: Tun yaushe kika fara rubutu kuma mene ne ya ja ra’ayinki ga harkar rubuce-rubuce?

AHA: Na fara rubutu tun a shekarar 2002. Da farko sha’awa ce ta fara jan ra’ayina na fara harkar rubuce-rubuce. Da na yi sai na nuna wa wani marubuci, sai ya ce in sayar masa da labarin. Sai na sayar masa. Haka na ci gaba, ina rubutawa ina sayarwa, su kuma suna bugawa da sunansu. Daga baya na daina sayarwa, shi ne na buga littafina na farko da sunana.

TG: Ya zuwa yanzu, littattafai nawa kika rubuta? Guda nawa aka buga a littafin takarda kuma nawa kika buga a intanet?

AHA: Ban da waɗanda na sayar a baya, a yanzu na rubuta littattafai guda goma sha ɗaya. Idan kuma har da wanda muka yi haɗaka wajen rubutawa ne, zan ce goma sha biyu saboda ni na jagoranci rubuta littafin; ko in ce na rubuta bayanan da muka tattara. Sannan an buga guda huɗu a littafin takarda. Sannan nakan tsakuri labari na rubuta a intanet ko cikakken gajeren labari.

TG: Waɗanne irin matsaloli kike fuskanta a matsayinki na marubuciya, musamman ma a soshalmidiya?

AHA: A matsayina na marubuciya, matsalolin da nake fuskanta musamman ma a shoshalmidiya bai wuce na satar fasaha ba. Na sha ganin mutane suna kwafin labarina su mayar nasu, ba tare da sun ambaci cewa labarin kwafi ne daga gare ni ba.

TG: Tun daga fara rubutu, waɗanne irin nasarori kika samu ko kuma akasin su?

AHA: Nasarorin da na samu a rubutu sai dai in ce Alhamdu lillah. Na shiga Gasar Hikayata ta BBC Hausa, wacce aka fara a 2016, muka zama zakaru ko gwanaye na farko; inda na yi nasarar zama ta biyu. Sannan ga nasarar faɗakar da ɗimbin mutane ta hanyar rubutu. Sannan alheran da nake samu albarkacin rubutu su ma nasarori ne.

TG: A harkar rubuce-rubuce, waɗanne marubuta ne gwanayenki, da kike koyi da rubutunsu?

AHA: Eh to, ina da gwanaye da dama sai dai ba zan ce ina koyi da rubutunsu ba. A cikin gwanayena da farko, akwai Abubakar Imam; kusan zan ce da shi na fara buɗe ido da karatun labarai sosai tun ina aji ɗaya na firamare. Sai Sidney Sheldon, sai Anti Bilkisu Salisu Funtua, sai Zuwaira Isa, sai James Hardley Chase, sai Bala Anas Babinlata, sai William Shakespeare sai Ola Rotimi.

TG: An daɗe ba a ji ɗuriyar ki da sabon littafi ba. Shin me ya faru, ko kin daina buga littafi ne?

AHA: Gaskiya ne tun 2018 ban sake fito da sabon littafi a takarda ba saboda lalacewar harkar karatu. Mutane sun daina karatun littafi, musamman ma matasa.

TG: Wasu marubuta sun koma rubutun fim, ko ke ma kina da shirin haka?

AHA: Eh na koma. Ina harkar rubutun fim da rediyo in ta samu. Kaɗan daga cikin rubutun da na yi, akwai fim mai dogon zango mai suna Bilkisu na kamfanin Amara Studio. Akwai wasan kwaikwayo, shi ma mai dogon zango, na Kamfanin I-Studio. Haka kuma ina daga cikin waɗanda suka rubuta wasu finafinai masu dogon zango na farko, ƙarƙashin ‘Breakthrough Action Nigeria.’ Sai wasan kwaikwayo na rediyo, a ƙarƙashin iDevPro-FEM. Sannan akwai babban kamfanin rubutu na Script Plus, masu rubutawa da sayar da labarin fim. Nan ma na rubuta labarun fim masu yawa.

TG: Mene ne babban burinki dangane da rubutu?

AHA: Babban burina a harkar rubutu, shi ne in bar baya mai kyau.

TG: Ko kina da wani kira ga gwamnati da marubuta ‘yan uwanki da kuma al’umma masu karanta littattafanki?

AHA: kira na ga gwamnati shi ne, ta muhimanta marubuta, ta daraja su kamar yadda ake yi a wasu wurare.

Ga ‘yan uwana marubuta, kira na shi ne, su dinga ara wa ‘yan baya masu tasowa aron kafaɗarsu don su jingina a kai. Wato su tallafe su a yayin da suka buƙata.

Ga jama’a makaranta kuwa, kira na gare su shi ne, su dawo da al’adar nan ta karatu, domin karatu yana kai makaranci inda bai taɓa zuwa ba. Sannan a dinga yi wa marubuta uziri saboda mai rubutu yana tare da kuskure. Idan an ga kuskure a ankarar cikin lumana.
~~~~~~~

Previous Post

Kasafin N18b: INEC za ta biya ma’aikata 16,000 alawus ɗin su, ba a zaɓen Bayelsa, Imo da Kogi za ta kashe kuɗaɗen ba – Yakubu

Next Post

Honorary Doctorate Degree to T.Y. Buratai and Orodje of Okpe Kingdom: An Acceptance Speech

Related Posts

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)
Adabi

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

December 23, 2025
Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine
Adabi

Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine

December 6, 2025
Yau Take Juma’a: Allah Ka Albarkace Mu
Adabi

Yau Take Juma’a: Allah Ka Albarkace Mu

December 5, 2025
Next Post
Honorary Doctorate Degree to T.Y. Buratai and Orodje of Okpe Kingdom: An Acceptance Speech

Honorary Doctorate Degree to T.Y. Buratai and Orodje of Okpe Kingdom: An Acceptance Speech

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Za Mu Inganta Rayuwa Da Ayyukan ‘Yan Jarida – Minista Idris

Za Mu Sake Dasa Wa Al’ummar Nijeriya Ɗabi’ar Yarda Da Kalaman Shugabanni – Minista Idris

October 18, 2023
RAYUWA (Sadaukarwa Ga Talakawan Najeriya)

RAYUWA (Sadaukarwa Ga Talakawan Najeriya)

September 5, 2023

PHOTO GALLERY: Hajia Rabi Attends UNICEF Training

October 27, 2023
KADA Honours Ambassador A. Y Shehu with Excellent Award

KADA Honours Ambassador A. Y Shehu with Excellent Award

September 1, 2024

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation
  • Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco
  • Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

January 15, 2026
Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

January 14, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.