• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, September 20, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

Ziyara Biu

WAƘE

Khalid Imam by Khalid Imam
May 11, 2024
in Adabi
0
Visit to Biu

Mai Martaba Sarkin Biu da Ayarinsa

15
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Ziyara Biu

(Wake)

Related posts

ALLAH TSIN€ WA MAƘIYA MANZO (SAW)

ALLAH TSIN€ WA MAƘIYA MANZO (SAW)

September 12, 2026
Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

September 10, 2026

Khalid Imam

*****

Malam Khalid Imam malamin makaranta kuma marubuci ne ya bar Kano mazaunin sa ranar 9 ga watan Afirlu, 2024 ya kai ziyara a Birnin Biu har ranar 12 ga watan Afirlu, 2024. Waɗannan waƙoƙi biyu, ya ƙaga su a lokacin Ƙaramar Sallar Ramadan, a ranar 11 ga watan Afirlu, 2024. Daga baya ya juya waƙoƙin a cikin Turanci

*****

Daga Hagu: Betaran Biu, Janar TY Buratai (mai ritaya), Mai Martaba Sarkin Biu da kuma Dokta Bukar Usman, OON

Na je Biu na yi Salla,
Ƙarama a cikin karamci,
Mutane masu kirki,
Mutumci ga zumunci.

Na je salla ta Idi,
Mun yi Idi har da sarki,
Difiti Gwamna na Borno,
Ya zo Salla gidansu.

Mutan Biu sun ga nasu,
Ya zo domin su gaisa,
Mata da maza da yara,
Sun yi murna sun ga ɗansu.

Kowa murna yake yi.
Sarki duka Hakimansa,
Sun hau doki da kansu,
Ana ta kiɗa da busa.

Ƙasar Biu na da kyawu.
Biu birni ce a tsauni,
Bishiyar tsauni halinta,
Dogon rai ne gare ta.

Na ga al’adu na dauri,
Masu adana tarihin Biu,
Masu bayyana martabarta,
Masu nuna farin jininta.

Masu bayyana tarihinta,
Masu nuna irin ƙawarta,
Jarumanta juriyarta
A Hawan Salla na gan su

Na je Biu gaida dangi,
Na Bukar Usmanu giwa,
Bukar Usmanu Dokta,
Mai gida ne ni gare ni.

Kogi bishiya halinsu,
Alheri ba su rowa,
Kogi zai ba ka kifi,
Ruwan sha ko na noma.

Bishiya ko ta ba ka ‘ya’ya,
Inuwar hutu ka huta,
Bukar Usmanu tabbas,
Bishiya ne ga shi kogi.

Bukar kishi gare shi,
Ya yi banki nan garinsu,
Bankinsa na al’umma ne,
Burinsa ya ba da jari.

Jarin sana’a da noma,
Mutan Biu duk su samu,
Rijiyoyi yai na bohol,
Shekaru sun kai talatin.

Duk don jama’a su rayu,
Cikin sauƙi wadata,
Sai mai kishi na dangi,
Ke kai jari garinsu

Na ga yadda ake zumunci,
A ƙasar Biu babu bare,
‘Yan uwa ne su ga juna,
Noma ba sa kasala.

Tallafin ƙaro karatu,
Bukar na ba wa dangi,
Bukar na ba maƙota
Tallafi na iri da taki.

Wanda ke jinya a dangi,
Ko maƙota bai barin shi,
Magani da kuɗin buƙatu,
Bukar na bai wa kowa.

Na je na gaida Sarki,
Sarkin Biu jarumi,
Zaki shi ke da iko,
A daji ba kamarsa.

Sarkin Biu gun karamci,
Jinjina tilas gare shi,
Ya san daraja ta baki,
Ni shaida ne Khalidu.

Sarkin Biu na da kyauta,
Ga alfarama da hira,
Fara’a ya zarce gonar,
Auduga ni na yi shaida.

Mun gaisa har da Sale,
Aboki gun Bukar ne,
Dattijo ne na gaske,
Mai barkwanci da ilmi,

Ya koyi halin Aminu,
Ya min saukar mutumci,
Baƙo daraja gare shi,
Wajen Manzo na Hafsa.

Garin Biu in da hali,
Can zan koma na tare,
Na yi noma har da rani,
Arziki na nan a noma.

Ba shakka da da dama,
Garin Biu za na koma,
Don nai kiwon awaki,
Shanu kaji tumaki.

Garin Biu na da Dokta
Wani mai kishin ƙasarmu,
Mota kayan jikinsa,
Da gida tutar ƙasa ne.

Komai ka gani gare,
Kalar tutar ƙasa ne,
Har takalmin ƙafarsa,
Hula tutar ƙasa ne.

Garin Biu jami’a ce,
Akwai darussa na ɗauka,
Tafkin Tila in ka ɓulla,
Ka sha kallo ka more,

Abin ajabi a tafkin,
Yana da yawa na dubi,
Kadoji na ta kiwo,
Kifaye na ta yawo.

Akwai lantarki na aiki.
Cikin Biu kulliyaumin,
Makarantu jami’o’i,
Akwai da yawa ƙasar Biu.

Jami’ar sojan ƙasarmu,
Garin Biu ne masauki,
Ƙasar Biu na da faɗi,
Masarauta ce daɗaɗɗa.

Mutan Biu na da kishi,
Sun raya garinsu sosai,
Ni na ga hakan da kaina,
Lokuna lungu da saƙo.

Dukkan titi da sola,
Ko’ina haske ka duba,
Titunan Biu babu rami,
Shugabanni na da kishi.

‘Yan siyasa masu aiki,
Su ke zaɓa wa kansu,
Ba sa zaɓe makance,
Sai sun tace su darje.

Dukkan titin garin Biu
Da kwata ta ruwa a gefe,
Wakilinsu da ke Abuja,
Shi Betara ɗan halak ne.

Wanda ke kishin garinsu,
Jinjina tilas gare shi,
Da a ce da irinsu dozin,
An bar kuka Arewa.

‘Yan ƙasar Biu jarumai,
Burutai babban Janar,
Fanni-fannin ƙwararru,
‘Ya’yan Biu za a gan su.

A nan zan jefa aya,
Khalid na je ziyara,
Imam na je da kaina,
Ƙasar Biu nai zumunci.

__________

(HM) Khalid Imam
A Garin Biu
7:33ND
11 ga wata Afirelu, 2024

Previous Post

Ruhin Bukar Usman

Next Post

SARAUTA TUSSLE: The Debacle in Kano State

Related Posts

ALLAH TSIN€ WA MAƘIYA MANZO (SAW)
Adabi

ALLAH TSIN€ WA MAƘIYA MANZO (SAW)

September 12, 2026
Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai
Adabi

Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

September 10, 2026
Alhaji Sule Lamido: Jagoran Talakawa Na Haƙiƙa
Adabi

Alhaji Sule Lamido: Jagoran Talakawa Na Haƙiƙa

August 29, 2026
Next Post
SARAUTA TUSSLE: The Debacle in Kano State

SARAUTA TUSSLE: The Debacle in Kano State

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (7)

ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (7)

June 10, 2025
#AdalciGaWalida (01): ƘIRA GA GWAMNATIN JIHAR JIGAWA DA TA ƊAUKI MATAKIN GAUGAWA A KAN KUƁUTAR DA WALIDA ABDULHADI

#AdalciGaWalida (01): ƘIRA GA GWAMNATIN JIHAR JIGAWA DA TA ƊAUKI MATAKIN GAUGAWA A KAN KUƁUTAR DA WALIDA ABDULHADI

February 23, 2026
KANA SON FAHIMTAR MATA?

KANA SON FAHIMTAR MATA?

November 9, 2023
Kwamishina Saulawa Jajirtacce Ne – Dr. Bala Nuhu

Kwamishina Saulawa Jajirtacce Ne – Dr. Bala Nuhu

August 10, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso
  • JAGORA: Leader of the Masses
  • MALAM SULE LAMIDO: Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

September 20, 2026
JAGORA: Leader of the Masses

JAGORA: Leader of the Masses

September 17, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.