• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, July 26, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Siyasa

Kasafin N18b: INEC za ta biya ma’aikata 16,000 alawus ɗin su, ba a zaɓen Bayelsa, Imo da Kogi za ta kashe kuɗaɗen ba – Yakubu

Daga Wakilinmu by Daga Wakilinmu
November 4, 2023
in Siyasa
0
Zaɓen gwamna: Mutum 2,318,919 za su yi zaɓe a Imo, 1,833,160 a Kogi, 1,017,613 a Bayelsa, inji INEC

Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmud Yakubu

17
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Kasafin N18b: INEC za ta biya ma’aikata 16,000 alawus ɗin su, ba a zaɓen Bayelsa, Imo da Kogi za ta kashe kuɗaɗen ba – Yakubu

Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana a cewa hukumar ta nemi naira biliyan 18 daga kasafin naira tiriliyan 2.17 ne domin ta biya ma’aikatan ta sama da 16,000 kuɗaɗen alawus ɗin da gwamnatin tarayya ta yi masu ƙari a cikin 2023.

Related posts

Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

July 24, 2026
Zaɓen 2027: Akwai Yiwuwar Farfesa Pantami Ya Yi Nasara – Farfesa Lawanti

Zaɓen 2027: Akwai Yiwuwar Farfesa Pantami Ya Yi Nasara – Farfesa Lawanti

July 8, 2026

Yakubu ya ce ba kamar yadda jama’a ke wa INEC yarfen cewa ta kashe naira biliyan 335 na kasafin 2022 a zaɓen 2023 ba, ya ce naira biliyan 18 da aka ware mata a wannan kasafin ƙarshen 2023, ba a zaɓuɓɓukan gwamnan Bayelsa, Kogi da Imo hukumar za ta kashe su ba.

Da ya ke jawabi a gaban Kwamitin Majalisar Tarayya a ranar Laraba, Yakubu ya ce akasarin kuɗaɗen duk wajen biyan ma’aikata za a kashe su.

Shugaban na INEC ya ce hukumar sa na buƙatar naira biliyan 10.6 domin biyan ma’aikatan ta ƙarin kashi 40% bisa 100% na alawus ɗin da Gwamnatin Tarayya ta yi masu ƙari.

Ya ce INEC na da ma’aikata 16,624.

Ya ce: “Za ku iya tunawa a cikin Afrilu na wannan shekara an yi wa mai’aikatan gwamnatin tarayya ƙarin wasu kuɗaɗen alawus har zuwa kashe 40% bisa 100%. To mu babu wannan ƙarin a cikin kasafin INEC na 2023, saboda an rigaya an rattaba wa kasafin 2023 hannu a majalisa tun cikin Disamba, 2022. A daidai wancan lokacin kuma an fitar da sanarwar daga gwamnatin tarayya a cikin Fabrairu cewa an ƙara wa ma’aikatan gwamnati kashi 40% bisa 100% na alawus ɗin DTA da wasu alawus daban.

“To INEC akwai sama da ma’aikata 15,000. Kuma a yanzu babu yadda za a iya samun kuɗaɗen da za a biya su, idan ba a bijiro da ƙwarya-ƙwaryan kasafin a ƙarshen wannan shekara ba.

“Dalili kenan muka gabatar da buƙatun kuɗaɗen ga gwamnati, don haka aka saka INEC cikin wannan kasafi.

“Kenan INEC ta na buƙatar Naira biliyan 10.6 domin biyan ma’aikatan ta 16,614 alawus ɗin su.”

Yakubu ya ci gaba da bayyana yadda hukumar zaɓe ta kashe naira biliyan 355 na cikin kasafin 2022. Ya ce INEC ba ta kashe ilahirin kuɗaɗen kamar yadda wasu mutane ke ta yi wa hukumar yarfe ba.

Ya ce ta yi amfani da wani kaso na kuɗin wajen shirya zaɓen jihar Osun da Ekiti.

Saboda haka sai Yakubu ya ce INEC za ta shirya zaɓen Bayelsa, Imo da sauran kuɗaɗen cikin kasafin naira biliyan 355, waɗanda har yanzu ba su ƙare ba.

Ya ce a yanzu sun nemi Naira biliyan 18 ne daga hannun gwamnati saboda biyan ma’aikata alawus ɗin su, wanda ya yi bayani a baya da kuma ƙarin wasu kuɗaɗe na tilas, musamman saboda yadda aka samu tashin farashin wasu kayayyaki a yanzu cikin 2023, kamar litar fetur, wadda aka yi kasafin kan farashin ta naira 197, yanzu kuma lokacin zaɓuɓɓukan Bayelsa, Imo da Kogi, litar fetur ta haura naira 600.

Previous Post

SHARI’AR MUSULUNCI: Bayan Yaƙi Da Baɗala, A Yaƙi Ɓarayin Gwamnati, Hanci Da Rashawa

Next Post

Babban Burina A Rubutu: In Bar Baya Mai Kyau – AHA

Related Posts

Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya
Siyasa

Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

July 24, 2026
Zaɓen 2027: Akwai Yiwuwar Farfesa Pantami Ya Yi Nasara – Farfesa Lawanti
Siyasa

Zaɓen 2027: Akwai Yiwuwar Farfesa Pantami Ya Yi Nasara – Farfesa Lawanti

July 8, 2026
Jaafar Jaafar Ya Buɗe Idanun ‘Yan Kwankwasiyya
Siyasa

Jaafar Jaafar Ya Buɗe Idanun ‘Yan Kwankwasiyya

June 17, 2026
Next Post
Babban Burina A Rubutu: In Bar Baya Mai Kyau – AHA

Babban Burina A Rubutu: In Bar Baya Mai Kyau - AHA

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Gwamnatin Tinubu Za Ta Fifita Amfani Da Na’urorin Zamani A Gidajen Rediyo Sa Talabijin – Minista

Gwamnatin Tinubu Za Ta Fifita Amfani Da Na’urorin Zamani A Gidajen Rediyo Sa Talabijin – Minista

October 26, 2023
Taya Ni Mu Gyara: Kisan Baƙi Sai Gayya

Taya Ni Mu Gyara: Kisan Baƙi Sai Gayya

November 1, 2025
Zaɓen gwamna: Mutum 2,318,919 za su yi zaɓe a Imo, 1,833,160 a Kogi, 1,017,613 a Bayelsa, inji INEC

Kasafin N18b: INEC za ta biya ma’aikata 16,000 alawus ɗin su, ba a zaɓen Bayelsa, Imo da Kogi za ta kashe kuɗaɗen ba – Yakubu

November 4, 2023
ACF Endowment Fund Sets Agenda for Transparency, Education and Empowerment in Northern Nigeria

ACF Endowment Fund Sets Agenda for Transparency, Education and Empowerment in Northern Nigeria

June 24, 2026

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • General Buratai to Marry Off His Daughter Today
  • Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya
  • Saƙon Godiya Da Bangajiya

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

General Buratai to Marry Off His Daughter Today

General Buratai to Marry Off His Daughter Today

July 25, 2026
Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

July 24, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.