KHALID IMAM: Tattaunawa Da Marubuci Mai Hannu Da Yawa
Daga Bashir Yahuza Malumfashi
~~~~~~~
Idan kana neman marubuci mai himma, mai jajircewa a harkar duk da ya sa gaba, idan ka samu Khalid Imam, sai ka yi hamdala. A lokacin da mutane ke da hannu biyu, Khalid Imam shi hannaye ke gare shi da yawa – ga shi malamin makaranta, ga shi marubucin Ingilishi, ga shi marubucin Hausa. Rubutun ma da hannaye fiye da biyu yake yi. Ga shi marubucin waƙa, ga shi marubucin zube, ga shi marubucin wasan kwaikwayo. A tattaunawar shi da Taskar Gizago, ya warware zare da abawa game da rayuwarsa ta rubuce-rubuce da wallafa.
~~~~~~~

TG: Kana ɗaya daga cikin marubutan Hausa a wanann zamani. Ko za ka gaya mana tarihinka a taƙaice?
KHALID: Cikakken sunana shi ne Khalid Imam kuma an haife ni a garin Kano, cikin Unguwar Yakasai, a shekarar 1973. Na yi makarantar allo a gidanmu, wato Gidan Makarantar Malam Tadda. Na yi Islamiyyu a cikin garin Kano da kuma a Minna. Haka kuma na fara karatun boko a Kano, na ci gaba a garin Minna, inda na yi NCE, sai kuma na dawo gida Kano na fara aikin koyarwa daga baya na koma na ci gaba da karatu bayan kwashe shekaru ina koyarya. Na yi digiri na ɗaya da na biyu a Kano, duk a Jami’ar Bayero.
TG: Tun yaushe ka fara rubutu kuma mene ne ya ja ra’ayinka ga harkar rubuce-rubuce?
KHALID: Na fara rubutu tun ina karatun NCE a Kwalejin Ilimi ta Jihar Neja da ke cikin garin Minna, karatun da na kammala a cikin 2000. Na fara rubutun tun wajejan shekarar 1998 saboda ina da sha’awar karance – karancen jarida sosai tun ina karatun sakandare amma ban fara rubuce-rubuce a lokacin ba. Babban maƙasudin da ya sa na tsunduma cikin harkar rubutu ka’in da na’in shi ne gori da aka yi wa Hausawa da matasa ‘yan asalin Arewa, wanda wata malamarmu ƙabila ta yi lokacin muna karatun NCE a Minna. Zan iya cewa na zama marubuci ne tun bayan faruwar wannan gori da malamarmu ta yi mana, wanda hakan ya zaburar da mu, sakamakon fahimtar da muka yi kamar ta nuna mu Hausawa ba mu da basira da dagiyar da za mu iya yin rubutu ko bayyana baiwarmu a fagen rubutun ƙagaggun labarai a lokacin da take yaba wa wani abokin karatunmu, ɗan uwanta ƙabila fiye da ƙima saboda ya wallafa littafin wasan kwaikwayo a cikin harshen Faransanci.
Tun lokacin ni da wasu abokaina su biyu muka ƙudiri niyyar zama marubuta kuma hakan ta sanya muka shiga wata ƙungiyar koyon rubutu da aikin jarida, watau Press Club na wannan Kwaleji. Na ci gaba da zama ɗan wannan ƙungiya ta Press Club har ƙarshen karatuna a wannan Kwaleji kuma na zama an zaɓe ni Mataimakin Shugaban Ƙungiyar na biyu da muka shiga shekara ta ƙarshe.
A wannan ƙungiya ta Press Club na fara gwada basirata ta rubutu, har ta kai na fara aika wa jaridu rubutuna suna bugawa. Jaridar Weekly Trust ce ta fara wallafa rubutuna, wanda Editan Shafin Adabi watau Ibrahim Sheme ya wallafa wasu waƙoƙina na soyayya da na rubuta cikin harshen Turanci. Na rubuta waƙoƙin ne don yaba wa soyayya da ƙaunar da nake wa mahaifiyata da kuma wata budurwata Banufiya da muke karatun NCE tare a waccan lokacin.
TG: Ya zuwa yanzu, littattafai nawa ka rubuta? Guda nawa aka buga a littafin takarda kuma nawa ka buga a intanet?
KHALID: Ban taɓa wallafa littafi ba a shafin Intanet, musamman salo irin wanda wasu marubutanmu na Hausa suke a wasu dandali da shafukan soshalmidiya, sai dai na wallafa littatafaina guda biyu a shafin wallafawa da kasuwancin sayar da littattafai na duniya, watau AMAZON. Littattafan kuwa su ne: “Justice, Fairness and Egalitarian Societies” da kuma “Emir Muhammad Sanusi II the Toast of Kanawa.”
Batun littattafai kuwa da na wallafa ni kaɗai ko muka yi haɗin gwiwar rubutawa ko aikin editin, waɗanda aka buga a littafi za su kai ashirin da huɗu. Waɗanda na rubuta ba a buga ba kuwa sun fi gama sha biyar.
Na rubuta littattafai a kusan dukkan fanni na rabe-raben Adabi. Ina da Littattafai a fagen ƙagaggun gajeren labarai da kuma a fagen wasan kwaikwayo da kuma waƙa. Na rubuta littafi na wasan kwaikwayo mai suna “Sodangi” wanda ya zama ɗaya daga cikin zakarun Gasar Injiniya Bashir Ƙaraye. Kazalika na wallafa littafin da ya shafi taskance hirarraki mai taken: “Kundin Hirarrakin Bukar Usman” da kuma “Conversation with Bukar Usman” wanda littafi ne mai shafuka sama da ɗari tara.
A gaskiya na wallafa littattafai cikin harsunan Hausa da Turanci masu yawa. Misali na wallafa littafi a sigar wasiƙa mai suna “Letter to My Students” da kuma “A Citadel of Excellence.” Na rubuta littattafan ƙagaggun labarai na yara ‘yan makaranta, kamar su: “Barde Barbushe’ da “The Bird’s Evidence” da “The Amigo Sisters” da “Fati the Nupe Girl” da kuma “Sana’a Sa’a” da dai sauransu. Na rubuta littattafan da ban buga ba kamar su: “Wasiƙar Kurciya” da “Sanata Hankaka” da “Taskar Alheri” da “Sirrin Nasara” da kuma “Sirrin Samun Miji da Dabarun Mallakarsa Ɗari Biyu da Hamsin” da dai sauransu.
TG: Waɗanne irin matsaloli kake fuskanta a matsayinka na marubuci?
KHALID: Gaskiya zan iya cewa ina ɗaya daga cikin marubuta da suka auna sa’a duba da tallafin da Allah Ya ba ni wajen samun damar wallafa littattafai masu yawa kuma kusan duka ba da kashe kuɗin aljihuna ba. Sai dai kuma kasancewa ina cikin harkar rubutu tsundum ba zan ce ban fuskatar matsala ko ban taɓa fuskantar wata matsala ba. Amma dai nasarorin sun danne matsalar domin na sha samun gudunmawa ko haɗa gwiwa da ƙungiyoyin ci gaban al’umma na wallafa littatafai da suka shafi haifar da ci gaba a cikin al’umma. Ƙungiyata ta All Poets Network International da tallafin wasu ƙungiyoyi, mun yi haɗin gwiwa mun wallafa littattafai don wayar da kan al’umma game da annobar Kwarona, mai suna “Corona Blues” da kuma wani littafin a kan wayar da kan jama’a game da illolin cin hanci da rashawa a cikin ƙasa mai suna “Kwaraption” a cikin salo na Engausa, wanda ake gwama harsunan Hausa da Turanci wajen yin rubutu. Akwai littafi da muka buga na gajerun ƙagaggun labarai a kan annobar Kwarona, wanda shi ne littafi tilo da aka buga cikin harshen Hausa game da wannan annoba. Ni da Dokta Umma Aliyu Musa da take aiki koyarwa a wata jami’a a ƙasar Jamus, muka yi aikin wallafa littafin mai suna: “Rigakafin Korona.”
TG: Tun daga fara rubutu, waɗanne irin nasarori ka samu ko kuma akasin su?
KHALID: Na samu nasarori masu ɗimbin yawa sosai ta hanyar rubutu kamar yadda na bayyana a baya. Sakamakon rubutu an sha gayyata ta ƙasashen ƙetare halartar taruka da kuma ba da gudunmawa ta fannin aikawa da rubutu a buga cikin kundaye. Wannan ta sa an wallafa rubutuna a ƙasashe kamar Amurka Indiya da Birtaniya da Lebanon da Kenya da Poland da sauransu. Haka kuma na samu lambobin yabo masu yawa daga ƙungiyoyi kamar ANA da PIN da HIASFEST da Gwamnatin Kano da Inuwar Jama’ar Kano, duk bisa dalilin harkar rubutu.
Sa’annan na samu nasarori a fagen gasar rubutu sama da sau uku a cikin Kano da kuma a Nijeriya. Jaridu masu yawa sun sha karrama ni a matsayin marubucin maƙo ko na wata. Zan iya tuna kamar su Weekly Trust da New Nigerian Weekly da Public Agenda da Blue Print da dai sauransu. Babu abin da zan ce a rubutu sai dai in gode Allah, in sake gode masa. Rubutu ya sa an san ni a ciki da wajen Nijeriya. Hakan ta sa ina da abokai masu yawa marubuta a ciki da wajen Nijeriya da ma wajen nahiyarmu ta Afirka.
TG: A harkar rubuce-rubuce, waɗanne marubuta ne gwanayenka, da kake koyi da rubutunsu?
KHALID: A harkar rubutu musamman na waƙa, Marigayi Sa’adu Zungur da Marigayi Mudi Sipikin su ne gwanayena kuma da su na fi yin ƙoƙarin koyi, duk da cewa ina da ra’ayin yin waƙa salon irin wadda nake kira waƙa mai ‘yanci, wasu kuma suke kira da ballagaza. A fagen rubutun zube kuwa babu wani marubuci guda ɗaya da zan kira a matsayin wanda nake koyi da shi ko zan kira shi gwanina shi shi kaɗai, domin marubuta da yawa suna burge ni kamar su Marigayi Abubakar Imam da Dokta Bukar Usman da Farfesa Albishak da sauransu.
TG: Ya zuwa yanzu wane sabon littafi kake kan rubutawa kuma zuwa yaushe zai fita ga al’umma?
KHALID: A gaskiya ban fiya mai da hankali kan rubuta littafi guda ba. A mafi yawan lokaci za ka iya samu na ina aikin littafi sama da ɗaya a lokaci guda. Misali, wani littafin na waƙa ne, wani na zube ne, wani kuma na wasan kwaikwayo, duk zan iya yin aikinsu kusan a lokaci guda, sai dai kowanne idan ya bijiro mini sai in mayar da hankali kansa na yi ta yi. A halin yanzu dai akwai littattafan waƙoƙina na Hausa guda biyu da nake aikinsu da kuma littattafaina na adon zance da karin magana da nake ƙirƙira na Hausa da Turanci da nake ƙoƙarin haɗawa.
TG: Wasu marubuta sun koma rubutun fim, ko kai ma kana da shirin rubuta wani littafi na faɗakarwa da za a maida zuwa fim?
KHALID: Tun lokacin da na taɓa lashe gasar rubutun wasan kwaikwayo da Gwamnatin Jihar Kano lokacin Malam Ibrahim Shekarau ta shirya a ƙarƙashin Hukumar Ƙorafe- Ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta shirya da wani wasan kwaikwayo da na rubuta cikin harshen Turanci mai suna “The Mother’s Revolt.” Wasu daga cikin alƙalan gasar waɗanda masu rubuta fim ne, suka so in tsunduma cikin fagen rubuta fim gadangadan, wanda a cewar su suna buƙatar mutane irina a fagen. Amma gaskiya sai ban mai da hankali ba, ko in ji sha’awar yin hakan a wancan lokacin, kasancewa ta malamin makaranta, ba na son hakan ya hana ni mayar da hankali kan harkar aikina na koyarwa. Wataƙil tun da gobe kamar mace ce da ciki, ba a san me za ta haifa ba, in sami kaina cikin ɗaya daga masu rubuta fim ko ma fitowa a cikin shirin fim ɗin.
TG: Mene ne babban burinka dangane da rubutu?
KHALID: Ban da wani sauran buri a fagen rubutu nawa na kaina, domin duk kusan na cin musu. Ko ma ina da ragowar buri a harkar rubutu, bai wuce in ga kamfanina na Whetstone Publishers ya ƙara haɓaka ba, yadda zai samar wa ba ni kaina kaɗai ƙarin kuɗin shiga ba, har ma da zama tsanin damar samun aikin yi ga matasa masu yawa, duba da yadda samun aiki ga matasa yake same zama babbar matsala a ƙasa. Haka kuma zan so ‘ya’yana manya guda biyu, in ga su ma sun zama manyan marubuta a lokacin da nake raye, domin a yanzu dai sun dage suna gwada rubutu kuma suna halartar taruka na dandalin marubuta daban-daban a ciki da wajen Kano. Babban ɗana Khalid Imam Khalid (Junior) a yanzu haka an gayyace shi wani taron marubuta a garin Abuja, shi ko Shu’aibu Imam Khalid, wanda shi ban da ƙoƙarin koyon rubutun.ma har basirar zane-zane yana da ita. Sun dage burinsu a cewar su, su gaje ni kuma ni ma na fara jin a raina ina da burin su gaje nin, domin barewa ai ba ta gudu ɗanta yai rarrafe. Burina dai shi ne su ci gaba da mai da hankali a cikin harkar sosai don ta amfane su fiye da yadda ni na amfana da ita a gobe.
TG: Ko kana da wani kira ga gwamnati da marubuta ‘yan uwanka da kuma al’umma masu karanta littattafanka?
KHALID: Kira na ga gwamnatoci musamman na jihohin Arewa shi ne, su daina zama kurar baya a dangi, su dinga fitowa su ma suna taimaka mana kamar sauran takwarorinsu na Kudu, don bunƙasa wannan sana’a ta mu ta rubutu. Ba wai kawai su dinga tare ƙarfinsu wajen mu’amala da masu harkar waƙa ko ‘yan fim ba kawai. Haka kuma kira na ga marubuta ‘yan uwana shi ne, su rungumi damarmaki da ci gaban zamani ta fuskar fasaha ya kawo don inganta sana’armu. Ga masu karatu kuwa, kira na shi ne su ci gaba da karatu kuma su guji duk abin da zai jawo wa marubuta naƙasu ko koma baya a kodayaushe. Gwamnati da marubuta da masu karatu lokaci ya yi da za su gane cewa harkar rubutu wata babbar industiri ce da take buƙatar kowa ya ba da gudunmawa wajen bunƙasar ta. Shi dai rubutu kamar jinka ne, hannu ɗaya ba ya ɗaukar sa kuma kamar yadda Hausawa suke cewa, hannu da yawa maganin ƙazamar miya. Fata na shi ne, in ga lokacin da marubuta za su samu gata sosai a dukkan jahohinmu kamar yadda yanzu Shugaba Tinubu ya samar da hukuma, ya kuma naɗa Hannatu Musan Musawa Minista don bunƙasa harkokin rubutu da al’adu a Najeriya.
~~~~~~~












